← Book details Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 12

Sashe 3

Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai Momy ta ce "Doctor tun misalin sha biyu na lura idonshi biyu,na daren jiya tunanin nan dai daya sa kanshi, in yaga nace Dady sai ya rufe ido tamkar yana yin bacci.

Likitan ya ce "Ai sai a hankali,kin san fa kowa da akwai irin yanda so yake shigar shi.

Sha ɗaya daidai yayi miƙa gami da yin sallati da kuma ƴar gajeruwar miƙa, Momy ta je kasa dashi ta ce "ka tashi Babana ya jikin naka.?

Ya kai hannunsa ya shafa fuskarshi "da sauƙi Momy," ta ce likita ya shigo har sau biyu kana bacci sannan kuma abokan Dad ɗin ka ma sun zo su Alhaji Sabitu.

Ya ce "To nagode, Dad fa yazo?."

Ta ce "a'a ya dai kira phone É—ina yanzu ya ce suna tare da Uncle É—in ku may be ko tare É—in zasu zo,don ya ce daga wani guri suke."

Dady ya ce "Allah yasa daga gidan su Pretty suke,"Momy ta miƙo mishi Cup cike da tea ta ce to,sarki mai Pretty gashi ka shanye duka kafin ka sha magani.

Ya amsa ya soma sha yana cewa "Wai don Allah Momy me ya hana Hajja zuwa gurina."

Ta soma dariya tana cewa "Hajja tana fushi da mu wai zamu kashe mata jika, zuwan ta biyu lokacin baka cikin hankalin ka."

Kuka sosai ta yi mana ta ce duk laifin Dadyn kane don dama yayi mata ƙorafin bai son ka da Ruƙayya, shi ne tace duk laifin shi ne yaje ne ya yi musu wulaƙanci irin na masu sukuni dan tasa an bincika mata game mahaifin Ruƙayya, kuma ta samu labarin dattijon ƙwarai ne mai wadatar zuci, kuma shi ne mai gidan ba wai irin mazan da mata suke da gida ba, haka dai Hajja ta dinga faɗa akan haka in gaya maka sannan ta tafi ta ce ta daina ɓata ranta a banza in ma ka mutu ɗan mu ne mu ƙarata."

Dariya Dady yayi sannan ya ce "Hajja tawa kenan,bari ki gani bazata iya haƙura ba sai tazo, don yanzu nasan dai hankalinta yana nan."

Kafin Momy ta ce wani abu sai suka ga anturo ƙofa Abokan Dady sun kai su tara ganin shi zaune suka soma mishi dariya, Faisal ya ce "Son Guy,ka fara ramewa."

SadiÆ™ ya ce "a'a lover boy zamu sa masa yanzu, ya tashi daga Son Guy."

Daddy ya ce "babu komai,ina Hussain?"

Kafin su bashi amsa Hussain ya shigo yana dariya,ya ce "Kafa samu Son Guy na zata ba zaka gane ba guda É—aya ba."

Momy ta miƙe dan ta basu guri suka ce "Oh Momy sorry bamu kula dake ba, ina ƙwana? Ya me jiki?

Ta ce "Da sauƙi"

Sannan ta basu guri, Amir ya ce Son Guy yaushe ne wai zasu sallame ka?"

Ya ce ni fa É—in nan nike so na bar gurin nan, don hankalina yana gurin yarinyar nan ko bacci bana samu ina son in san halin da take ciki."

Hussain ya ce "Ina phone É—in ka ne,ba tana da phone ba?"

Dady ya ce "Tana dashi,Ok ku tambayi Momy phone É—in nawa ban san ina take ba."

SadiÆ™ ya ce "Ga tawa kira number É—in muji."

Dady ya ce "a'a bani na kira ta da kaina" duk suka sa mishi dariya.

Sai da ya kira wayar anci sa'a gidan ba kowa sai Umma tana É—aki.

Su Yaya Murja ma basu nan ta je makaranta.

Yaya Fati kuma tana gidan Yaya Amina,sai ta ji kukan waya cikin kayan Yaya Fati.

Da sauri ta ɗauka,sai da ta ɗan leƙa tsakar gidan babu kowa sannan ta ɗauki wayar tare da faɗin "Dady."

Ya amsa "Pretty na kina ina ne?"

Ta soma kuka ƙasa-ƙasa, zuciyarshi ta dugunzuma hankalinshi ya yi mugun tashi, ya ce "ki bar kukan ban son ji Pretty me yake faruwa ne me yasa Affa yayi min haka? Affa be san muna son juna ba ne?"

Cikin kuka ta ce "Ban san dalili ba Dady ina jin ka same shi nasan ƙila kai zaya sanar da kai komai kenan."

Ya ce "Zan zo yanzu ina asibiti ne, amma yau ne nike sa ran za'a sallame ni, don Allah ki taimaka min da kanki ki ƙwantar da hankalinki kin ji mata ta?.

Ta ce "To Dady kaima ka daina damuwa."

Ya ce "To kice min kina son zan fi jin daÉ—i."

Sam sai Ruƙayya ta ji yanzu zata iya yin duk abin da Dady ya ce tayi, cikin yanayin tausaya ma kansu ta ce "Yusuf ina son ka ina tsananin son ka zan cigaba da son ka har ƙarshen rayuwa ta. I love You so much," ta kashe wayar ta faɗa kan katifa taji daɗin jin muryar Dady tana sa ran in ya samu Affa komai zaya zo da sauƙi tunda Affa yana son shi.

Shi kam Dady ai mutuwa zaune yayi sanda Ruƙayya ta soma furta mishi kalmomi daya daɗe yana son ji daga gare ta,ganin yanda ya buɗe baki riƙe da waya,yasa abokanshi suka ƙwashe mishi da dariya. Al'amin ya zungure shi gami da cewa "yaya Son Guy irin wannan hangame baki kamar ka suma."

Cikin murna shima ya soma cewa "ni ma Ruƙayya ina son ki ina tsananin buƙatar ki I love You too." Tsalle sosai ya miƙe yana yi su kuma sai dariya suke masa.

Wanka Dady ya fito shadda fara ɗin kin 3-ƙwata, takalmi fari ya dubi fuskarshi a madubi,ya yi rama sosai idon shi ya ɗan ƙara haske ya ɗauki phone ɗin sa da key ɗin mota,ya sauka Momy tana gaban computer ya isa gurin ta "Momy na zan fita."

Da sauri ta dube shi "Dady ina zaka?" ( Bata jira amsa ba ta ci gaba) kasan fa Doctor ya ce ka natsu ka samu hutu yanda yakamata kuma ban da ka dage da fa ba zaya sallame ka ba."

Ya dafa ta "Kada ki damu Momy zan shiga Kabala ne naje naga Pretty sannan na je nayi bikon Hajja."

Ido Momy ta zuba mishi sannan ta ce "An ya kuwa zaka je gidan su Ruƙayya,ka san fa akwai ƴar hatsaniya da aka yi a ranar ɗaurin auren naku tsakanin Dad ɗin ka da mahaifinta,da ka bari ya huce sosai."

Shiru Dady ya yi na wani É—an lokaci sannan ya ce "Kada ki damu Momy zan ga Affan ne nasan komai kenan zan sani shine kaÉ—ai zaya fiddani daga duhun da na shiga.

Ta ce "Ok, to amma kada ka daÉ—e dan kasan Dad É—in ka zaya yi faÉ—a,in ya dawo baka gida."

Ya ce"ki ce masa na je gidan Hajja kawai.

Ta ce "a'a kasan dai bazan mara maka baya kayi ƙarya ba ko?

Yayi murmushi yana tafiya ya ce " Ba ƙarya bane Momy kin san har can fa zanje, tayi murmushi ta maida dubanta ga computer.

Umma ta dubi Ruƙayya wacce sai jiya ta ɗan soma sakin ranta har tana fitowa tsakar gida ta ce "To ni zan je gaida ɗan gidan Lamin Ado mai karaya,a Kabala wastin kinga Murja suna biki bata nan ki ɗora min tuwo kafin Fati ta shigo, Ita ma daga kai wa Amina saƙo ta je tayi zaman ta.

Ruƙayya ta ce "To Umma anyo cefanan ne?"

Umma ta dube ta "To waye ya yo daga dai ni sai ke,a ciki ni ce nayo?.

Ta ce "Ni dama Umma wallahi bana son fita ne sai mutane su yi ta nuna ni."

Umma ta saka hijabinta tana faɗin "To nidai ga kuɗin nan ƙasan filo kada ki je don kar a nuna ki,ki aje in Yayar ku Fati ta shigo ko Affan ku ko kuma ni in na dawo sai naje na yo cefanan." (Ta faɗa cikin gatse).

Ta tafi,ɗaki Ruƙayya ta koma tana cewa kai nidai na shiga uku!!! Banda dole babu abin da zaya fitar da ni gidan nan,ƙwanciya tayi tana tunanin gun da yafi kusa da zata je cefanan,a jikinta ta ji wai Dady ya shigo unguwar su,ta tashi ta fito tsakar gida,a duk sanda jikinta ya bata cewa Dady yana unguwar su to abin ya kan kasance,ta dubi jikinta riga ce da siket na wakas ƴar Nigeriya,ta ɗauko hijabinta na islamiyya tasa,ta ɗauki kuɗin cefanan ta fita.

Tana fita ƙarshen lungunsu motarshi tana tsayawa kamar mutuwar Soja haka Ruƙayya ta tsaya kyam tana dubanshi,ya fito shi ma gurinta ya nufo fuskarshi ɗauke da fara'a ta dubi fuskar tashi ya yi matuƙar ramewa,ga idanunshi masu birgeta suka ƙara haske, ɗan ƙyakkyawan gashin bakin shi daya zagaye ilahirin fuskarshi har zuwa haɓar shi da gefen fuskarshi ya ƙara fitowa,ƙyau ya yi masa sosai sannan ta ji ta ƙara son shi mai tsanani ji take kamar ta je ta rungume shi.

Daf da ita ya tsaya Pretty na,ta ɗago ido ta dube shi,tuni ƙwalla sun soma taruwa a cikin ƙwarmin idonta, ta juya cikin lungun ta nufi gida, da sauri ya biyo ta yana cewa "Pretty don son Manzon Allah ki tsaya kada kisa kaina ya sara Please tsaya." Ta tsaya daidai ƙofar gidan su ya iso "Haba Pretty menene na guduwa dan na zo?"

Ta sunkuyar da kai tana tunanin Affa, ya ce ko labari yaji an gansu tare to zata sani,tana tsoro kada a gaya mishi ko kuma Yaya Fati ta dawo ta gansu tare, tunda suma basu bata goyon bayan tsayawa da Dadyn ba, sun ce mata dole ne ta bi maganar Affa duk da basu san dalilin shi ba, gashi mutane sun tsura musu ido. Hannunshi yasa ya É—ago fuskarta, ta zuba mishi ido ya ce "Gaya min Pretty, me yake faruwa?"

Muryarta tana sarƙewa, ta ce "sai dai ka tambayi Affa,ni dai ya kafa min dokar cewa kada mu kuma tsayawa ni da kai."

Ya ce "What? Da gaske ki ke yi? Ya saki fuskarta, hankalinshi ya yi mugun tashi har tayi da na sanin gaya masa, hannu yasa ya riƙe kanshi, da sauri Ruƙayya ta ce.

"Dady ka sani ne,ka shiga mota ka gangara ƙasannan layi na uku zan zo sai muyi maganar yanda komai zaya kaya.

Ya dube ta ya ce "ba mutane ne a gurin? Kar su faÉ—a mishi."

Ta ce "Kai dai ka je ka jirani kada Yaya Fati ta zo ta ganmu,za ta ce ban ji maganar da Affa ya faÉ—a min ba."
Chapter 3 · 0% Book details