← Book details Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 12

Sashe 7

Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kam Dady ai akan shi aka ƙwana asubar fari sai asibiti,ƙwananshi sha ɗaya abu ba sauƙi sai na Allah. Dad da kanshi ya yi ma wanshi waya yana neman shi, bayan ya zo suka yi shawara Dad ya so suje su roƙi Affa ya yi haƙuri ya ba Dady Ruƙayya, amma sai ɗan'uwanshi ya ce, a'a ba haka za ayi ba, abin da zaya fi shi ne haɗa Dady da Yusra, tunda ai Ruƙayya ba fin Yusran zatayi ba, bayan haka ma tunda Yusra tafi Ruƙayya girma zata mantar dashi Ruƙayya tare da tattalinshi,ka ga tunda an gama komai game da wannan Company shi sai a haɗa da bikin buɗe Company dana auransu.

Dad ya amince amma Momy ta ƙi yarda, ta ce "Sam a bar mata yaronta ya samu lafiya kafin ayi mishi shawara in ya yarda,fa ni'im in bai amince ba sai a fasa."

Shi ma likitan ya ba Dad shawara, suka bari yaji sauƙi kuma kada ai mishi dole, wannan ne dalilin da yasa Dad duk ya fita daga haiyacin sa,koda ya tuntuɓi amininshi mahaifin Hafsi sai ya ce mishi "baya goyon baya mutum kamar shi ya je yana roƙo ga talaka, don haka ya barshi kawai."

Kan Dad ya yi zafi yama rasa yadda zayayi, Momy ce ta zaunar da shi ta ce "Ya ƙwantar da kai ya je ya samu su Alhaji Sabitu su dafa mishi baya ya je ya ba Affan Ruƙayya haƙuri.

Hakan ce kuwa ta kasance amma Affa ya ce "Sam."

Zuwan su Dad uku saboda kowa yaga Dady sai ya tausaya mishi in dai kana da zuciyar imani. Shima Affa duk da baiga Dady ba ya tausaya mishi,sai dai yana son Alhaji Mansur yaji yanda ya ji shima san da aka tsare shi akai ta zuwa ana roƙon shi amma yaƙi.

Ita ma Ruƙayya duk da tana ƙoƙarin nuna cewa ta haƙura babu daran da bazatayi kuka ba, kuma su Murja sun san tana yi, suna nuna mata basu sani bane, kuma suna tausayin ta sai dai basu so su nuna mata ne dan kada ta samu ƙofar kawo musu zancen Dady duk ta rame karatun tama ya yi rauni tun daga boko har islamiyya.

Germany su Dad suka yanke shawarar kai Dady dukansu suka tafi har ma da ƴan rakiya. Su Ruƙayya suna tsaka da zana jarabawa ciwon cikin ta ya motsa, kasancewar wancan watan batayi ba sai yazo mata da muguwar matsala tasha wahala sosai, ita ason ranta ma Allah ya ɗauki ƙwananta ta huta saura paper ɗin ta uku batayi ba,dan ma tayi masu muhimmanci.

Haka lokaci ya cigaba da tafiya sai ki ga da gari ya waye har yamma tayi sai ki ga dare ya shigo gari ya ƙara waye wa,ba wuya ace juma'a ta zago gashi har Dady ya samu wata uku a can Germany ya warke sarai sai dai zuciyarshi ce bata warke ba har yanzu son Pretty ɗin shi yana nan daram ƙauna zalla daga Allah, ya yi ƙyau ga wani haske da idonshi ya ƙara sai dai bai gama maida jikinshi ba. A wannan lokacin Ruƙayya tuni ta soma karatun ta a makarantar ƙwana dake Bakori a jihar Katsina. Affa ya yi hakane dan ya nisanta ta daga gida, duk da labari ya sameshi an fita da Dady (Germany)ta soma (S.S.1) ɗin ta ne cikin haƙuri da juriya.

Suna makaranta aka yi bikin su Fati,taso ace tana nan amma ina,taji haushi sosai ƙawayanta Safiya Umar da Walida da Amira sune suka yi ta bata baki. Safiya ƴar Katsina ce a Tudun Wada ita ko Walida ƴar Funtuwa ce ya yin da Amira ta zama ƴar Zariya.

Su huɗun nan koda yaushe suna tare. Suna mata labarin samarin su,Amira auran zumunci zasuyi ita da Mansur, ɗan kawun ta, ita ko Walida yaron Ogan Babanta zata aura na gurin aiki, Safiya kuwa ɗan layin su ne Usman, dukkansu Ruƙayya ta san su saboda sun zo lokacin ziyara.

In sun ce tana da saurayi,sai ta ce a'a, wata rana suna ƙwanarsu suna ta hira sai Walida ta ce "Ruƙayya don Allah zan tambaye ki wani abu zaki bani?."

Ruƙayya ta ce "Faɗa ko menene."

Ta ce "wannan zoben nake so."

Ruƙayya ta ce "Kash,aikuwa Walida sai dai ki amshi ɗayan nan amma ban da wannan don mutuwa ce kaɗai zata raba ni da zobannan."

Amira ta ce "Zoban alƙawari ne."

Ruƙayya ta yi murmushi ta ce "Ko masu bincike makarantar nan sun bar ni da zobannan, Zoban Dady Allah sarki Dady mai sona da gaskiya." Sai hawaye kuka sosai tayi da ƙyar su Amira suka lallasheta suka kaita har gadonta suka zauna.

Safiya ta ce "Ruƙayya Dadyn ya rasu ne?"

Murmushin ɓacin rai tayi ta ce "Dady yana nan sai dai yanzu ban san inda yake ba." Nan ta basu labarin Dady har ta nuna musu wayar ta daya bata sun sha mamaki, tare da tausaya musu sannan suka ɗauki alwashin sa ta a cikin addu'arsu kullum suka yi sallah biyar.

Walida ta ce "Ba zaki kirashi a wayar ba ne?"

Ruƙayya ta ce "bazaya yiwu ba tunda bazan same shi ba,gara nayi ƙoƙarin nesanta kaina dashi."

Su kam su Walida sun so ace wayar da chaji su ga yanda ake amfani da waya kasancewar wayar a wancan lokacin sai wane da wane ko a masu kuɗin. Suna cikin haka har lokacin hutu ya zo sun yi murna da ɗoki sosai na zuwa gida, Umma ta ce "Auta har yanzu kina nan kina ƙulafucin Dady ko?."

Ruƙayya ta yi yaƙe sannan ta ce "Haba dai Umma ai ni nama mance da wani Dady me kika gani?.

Ta ce "har yanzu baki maida jikinki ba, gashi kin samu É—an wake sai Allah."

Ruƙayya ta ce "munyi ciye-ciye ne a mota (ta sako wata maganar) Umma lokacin dana samu labarin auran su Yaya Fati sai da nayi kuka nace shin Affa yasa lokaci kusa dan kada naga bikin ko?"

Umma tana dariya ta ce "Ke da Affan naki in yazo sai ku ƙarata."

Ruƙayya ta ce "ina aka kaisu?"

Ta ce "Fati tana Kakuri, ita kuma Murja N.N.P.C ƙwatas."

Na ce "Eh,anan Yaya Ahmad yake aiki."

Umma ta ce "Eh, suna ta labari har Affa ya shigo duk da ya kula har yanzu Ruƙayya bata maida jikinta ba,ya ji daɗin ganinta tana ƴar walwala suna aiki tare da Ummanta.

Ruƙayya ta durƙusa ta gaishe shi cikin fara'a,ya amsa mata tare da nuna mata murnar shi na ganinta. Cikin hirar da suke yi da daddare take ƙorafin anyi biki bata, Affa lokacin da aka aiko min da wasiƙar nan sai da nayi kuka."

Ya yi dariya ya ce "Neman ilimin kenan,kema gashi makarantar Islamiyyarku da kuka yi sauka anyi walima ba ƙyanan,sai dai ke an aiko miki da ƙyautukan ki

Ta ƙara turo baki "kai gaskiya ni dai ban so haka ba."

Affa ya ce "To ai shikenan ya wuce ai ko?."

Ta je gidan Fati ta wuni washegari ta je gidan Murja,sun ji daɗin ganinta sai dai dukkansu sun mata ƙorafin rashin maida jikinta, cewa ta yi karatu ne, tayi sha'awar yanda mahaifin nasu yayi matuƙar ƙoƙari ya tsarawa ƴan'uwanta ɗaki ta je gidan su Yaya Amina Yaya Suwaiba da Sadiya, duk sun yi murnar ganin Auta ta ƙwantar da hankalinta.

Bayan sun koma makaranta sun haɗu da ƙawayenta suka ci gaba da karatu.

Ƙwanci tashi gurin Allah ba wuya sai gashi sun shiga S.S.2, ciwon cikin ta kam yana nan tana shan wuya,malaman su har sun gane ta, saboda duk wata sai tayi wani sa'in kuma tana yin wata biyu ko uku,in ta dawo hutu samari kamar me amma bata fita ko Umma ta ce tashi ki je tunda ai ba danki zamuyi dake ba kina gamawa aure zakiyi,sai ta tura baki tana fita zata korashi,in ko a hanya ne sai ta ce tana da miji.

A haka dai har suka shiga S.S.3 ance aski in yazo gaban goshi tafi zafi to haka suma karatun nasu yafi zafi yanzu,dan haka suna ƙoƙari kuma har zuwa wannan lokacin Ruƙayya tana kukan Dady da yawa tana ganin shi cikin mafarkin ta,yana faɗi mata kar ta karya alƙawari.

Sun samu hutun zango na biyu a shekarar su ta ƙarshe bakin titi suka tsaya suna ta banƙwana Ruƙayya da Amira hanyarsu guda dan haka tare suka taho a Zaria Amira ta sauka ita kuma ta nufo Kaduna.

Girma da cika Ruƙayya tayi ga ƙyanta ya bayyana fatar ta tamkar Black America wasu kuma su ce kamar ƴan matan Ethiopia duk saurayin da ya ganta sai ya sake dubanta.

Cikin shadda pink kayan ya yi matuƙar amsar ta gidan Yaya Murja zata. Bayan ta miƙa ɗinkinta gurin Nasir,a hankali cikin natsuwa take tafiya ƙwarai tana birge mutane, shagon Nasir ta tsaya ƙyaƙƙyawan saurayi mai son neman na kansa ya yi matuƙar iya ɗinki da aikin surfani na mata,dan haka ma shine ke ma mata manya da ƴan mata masu son a birgewa,yana ganinta ya ce "manya Ruƙayya saukar yaushe?"

Tayi murmushi ta ce "shekaran jiya na dawo ya aiki?."

Ya ce "Alhamdulillah,"ta zube mishi zannuwan ta "kin san kuÉ—in zannuwan nan kuwa."

Ta ce "Nasir kenan, nima ban sani ba."

Ya ce "ai naga alama daga yanayin riƙon da kikai musu. Dariya ta saki tana cewa "lallai Nasir to wane irin riƙo nayi musu?."

Ya ce "Oga ne ya siya miki ko?"

Ta ce "wane Oga aini banida wani Oga."

Ya gyara tsayuwa dan ya daÉ—e yana son ta sai dai yana shakka dan yasan dole tana da samari "Ban yarda ba, domin ke son kowane." Ta É—an rage fara'a.

Ta ce "To nagode, yanzu kana da style a ƙasa."

Ya ce "Ko babu dole na nemo shi."

Ta ce "ayimin landin full a riguna,sun fi zama."

Ya ce "An gama."

Ta ce "Bill É—in kuÉ—ina naji."

Ya ce "Ki je sai angama."

Gidan Yaya Murja ta wuce ta sameta tana dafa abinci a kitchen,kicin ɗin suka shiga tare,alalanwake da hanta da ƙwai take yi Ruƙayya ta ce "ina mama ne?"

Murja ta ce "tana bacci yanzun nan ta ƙwanta bayan ta gama rigima zata bi babanta."

Ruƙayya ta ce "Ai dama mama ƴar dan ja ce aƙwai rigima, Muhsin ɗin Yaya Fati yafi ta haƙuri."
Chapter 7 · 0% Book details