← Book details Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 12

Sashe 5

Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ikon Allah ne ya kai Dady gida ya fito a mota hankalin nan nashi a tashe yana shiga cikin falon su ya hangi Momy ita da Dad wajen daning Dad yana tsaye da alama ma faɗa yake yi, ya isa gurinsu Dad ya dube shi da sauri ina ka shigane Son tunda na dawo nike neman ka a phone ka kashe ka shiga gari kaji dai abin da Doctor ya ce kana buƙatar hutu shi ne amma zaka tashi kalar neman damuwa ai gashi nan kana yaronka jininka ya soma hawa nida girmana nawa be hau ba sai naka dan kaine kasa kanka, Momy ta miƙe ta ce "Haba Alhaji yaya zaka sanar dashi halin da yake ciki in kuma yaji ya ƙara tada hankalinsa fa."

Dad ya ce "ai gara yaji in zayayi mentain É—in lafiyar sa yayi in bazai yi ba shi ya sani."

Tunda Dad yake ta faɗa Dady ko ajikinsa sai da ya gama ya zauna sannan Dady ya dube shi ,kayi haƙuri Dad nima dole ce tasa na fita ya cigaba. Ya ce "Dad wai dan Allah meke tsakanin ka da Affan Ruƙayya da kuma Alhaji Aminu Jega?" Ido Dad ya tsura mishi na ɗan lokaci sannan ya ce me kake son sani ne? Wannan ba damuwar ka bane,kana ji na ko Son?"

Dady ya ce "Damuwa ta ce domin akan ta zan rasa Ruƙayya wanda hakan zaya iya haifar da komai mahaifin Ruƙayya shi ne ya turo ni gurinka dan naji daga gareka,dan ya ce kaine kafi cancanta ka sanar dani dalili kuma ya ce na yarda duk abin da ka gaya min."

(Dad ya katse shi) "Son ka kiyaye ni fa zanyi fushi da kai banason kana zuwa gurin wannan ɓarawon mutumin ka koma shi ya gaya maka da kansa tunda kai ya zama dole sai ka auri ƴarsa." Da faɗar haka yayi saman shi cikin ɓacin rai.

Kai Dady ya kifa akan daning table zufa ce ƙwarai ke zubo masa ya yin da kansa ya soma sarawa ya sa hannu ya riƙe kan.

Momy ta tashi ta kamoshi ta ce "Dady zo muje É—aki zo ka sanar da ni yanda kukayi."

Ko gani sosai bayayi suka shiga ɗaki bakin gado suka zauna ta dafashi "Yaya kuka yi da Affan Ruƙayya? A hankali ya sanar da ita komai."

Ta ce"ka ƙwantar da hankalinka gobe zamuje ni da kai dan ya sanar damu komai kenan daga nan sai naga abin zanyi akai."

Duban Momy Dady ya yi ya ce "Nagode Uwata mai maganin damuwata Allah ya bar min ke" ta ce to kayi bacci bana son hirar dare ka ji." Ya ce "insha Allah " ya miƙe cikin ƙarfin gwiwa.

Talatainin dare tunda ya ƙoƙarta ya yi wanka sai ya zama ya kasa bacci sai faman sintiri yake a tsakar ɗaki,ƙarfe biyu da minti ashirin sannan ne ya samu ya faɗa kan gado, hannu yasa ya janyo filo ya rungume shi tsam,ban da muryar Pretty dinshi babu abin da yake muradi hannun shi yasa ya ɗauko wayar sa ya soma neman ta nan take ya tuna cewa ta ce suna ƙwana tare da Yayyanta. Amma duk da haka sai yaji zuciyarsa tana matsa masa, don haka sai ya ci gaba da neman layin ta, ringing ɗin farko Ruƙayya ta miƙe ta ɗauko wayar da sauri ta koma can bayan jakunkunan kayan su,a hankali take magana "Dady ya ya ne?" Ya yi ajiyar zuciya gami da juyi rigingine ya kuma ƙara rungume filon tsam ji yake tamkar ita ce a ƙirjinsa ya ce "Oh my sweet heart,ina cikin damuwa na kasa bacci."

Ta ce, nima haka ya ce "Allah sarki, yanzun dama ɗaya ta rage mana don haka gobe zamu zo da Momy ƙila ya yarda."

Ta ce "Allah yasa haka."

Ya ce "Amin,ki dinga zama koda yaushe da wannan wayar zan dinga kira."

Ta ce "To, amma kada ka kirani kuma lokacin da mutane.

Ya ce "Zan gaya miki yanda zaki maida ta a silent in na kira sai dai tayi vibrating ba mai ji sai ke kinga sai ki kauce daga gurin mutane."

Ta ce "To."

Ya ce "Yanzu gaya min kina zaune ne ko kina ƙwance?"

Ta ce "A'a ina ma raɓe ne bayan kayan sawar mu,kai fa?"

Ya ce "Allah Sarki,Ni kam yanzu ina ƙwance a ɗaki na kan gado rungume da filo a ƙirjina,sai ina ji tamkar Pretty ɗina ce na mannata." Ta yi ƴar dariya ta ce

"Kai ko."

Shima ya ce "Ke ko." Suka yi dariya tare.

Ya ce "I love You."

Ta ce "me too"

Sai kawai taji ya yi kiss ɗin ta a wayar a kunnanta taji ya ratsata har tafin ƙafarta,da sauri ta kashe wayar tayi ajiyar zuciya gami da ɗan murmushi cikin jakar kayan ta ta tura wayar ta koma tayi ƙwanciyar ta.

Shima dariya ya yi har da wuntsilawa zuciyarshi ta yi fes ya miƙe ya shiga toilet ya ɗauro alwala ya shiga miƙama Ubangiji matsalar sa.

Ruƙayya tana sharan tsakar gida Umma ta na ɗaki lokacin dai dai ƙarfe biyar sun gama abincin dare sun sa a kula Fati da Murja suna ɗaki suna labari Momy ta yi sallama da sauri Ruƙayya ta miƙe suka dubi juna murmushi Momy ta saki ta ce "Ruƙayya ƴata kina shara ne."

Ruƙayya ta sunkuyar da kai sannan ta ce "Momy sannu da zuwa."

Momy ta ce "yauwa ƴata ina Umman taki?"Ruƙayya ta shiga ɗakin Umma ta ce "kinyi baƙuwa." Ta fito ta shiga ɗakin su,Yaya Fati anyi baƙuwa fa.

Suka dube ta "Wacece."

Ta ce "Momyn Dady ce." Da sauri suka tashi suka fita sun samu Umma ta fito mata da tabarma ta shinfiɗa mata a tsakar gidan dake share ƙal. Dan Umma ta ce mata ta shiga ɗaki amma sai ta ce nan yayi ma, Yaya Fati ta kawo mata ruwa mai sanyi na randa sai ƙamshin saiwar da ake sawa cikin ruwa ta zuba shi ne cikin sabon jug irin na kayan auran Ruƙayya Yaya Murja kam tuwon Affa ta kawo mata cikin sabuwar kula da yake ance baƙon ka annabin ka.

Momy ta ce "Agaishe ku Æ´aÆ´ana." Suka russuna suka gaishe ta.

Ta ce "ina Æ´ata shi ne ta shige É—aki."

Suka yi dariya sun yabawa Momy mace mai sauƙin kai da rashin ƙyamar talaka, ita ma sun burge ta sosai.

Ta yaba da tarbiyyar su ta girmama na gaba,sun gaisa da Umma, Umma ta ce to baki ci tuwon ba.

Momy ta ce Alhamdulillahi na sha ruwan,dan dama nazo gurin Affan nasu Ruƙayya dan Dady ya ce min ƙarfe biyar zamu sameshi."

Umma ta ce "ƙwarai ya kan dawo biyar ɗin, to yau dai gashi har shida saura nasan dai yana hanya."

Momy ta ce "Allah ya kawo shi lafiya."

Umma ta ce "Amin." Phone É—in ta ta soma kuka ta É—auka.

Ta ce "Yaya ne Dady?"

Yayi muryar tausayi "Please Momy ki turo min Pretty mana."

Momy ta ce "A'a ka shigo mana kaima ai gidanku ne."

Ya ce "Ina jin kunyar Umma,dama dai Affa ne zan iya shigowa."

Ta ce "to sai ka jirashi don be ƙaraso ba." Ta kashe wayar.

Affa tare suka shigo da Dady,yana riƙe da ledar da Affa ya ruƙo daga kasuwa mai ɗauke da lemu da yalo da kuma gautan ɗaci, Umma ta tashi tana sannu da dawowa Malam, ta buɗe mishi ɗakinsa Momy ma ta mai sannu ya amsa sannan ya shiga ɗakin Dady ya ɗan russuna ya miƙa ma Umma ledar bayan ta fito daga ɗakin Affa inda ta kai masa ruwan sha, ya ce "Yusuf shigo mana."

Shi kam yana ta waiwayen inda zai hango Pretty É—in sa.

Momy ta ce "kaifa yake kira." Sannan ya bar leƙen windon ɗakin su Ruƙayya inda ya hango ta,tai mishi gwalo ta tsugunne shi ne yake ta faman leƙen windon.

Ya shiga suka gaisa sannan ya ce "Na kawo Momyna tana son ganin ka."

Affa ya ce "to ai babu damuwa,sai ku shigo."

Momy ta nemi guri ta zauna a cikin É—akin, Affa ya dubi Momy "sannu da zuwa Hajiya."

Momy ta amsa sosai suka gaisa, sannan ta ce "Dama dalilin zuwa na shi ne, ina neman alfarma da kayi haƙuri ka yarjewa yaran nan da su auri juna, musamman ma ita Ruƙayya dake fama da matsala,ni na rasa menene ainihin matsalar.

Affa ya gyara zama ya ce "shi maigidan naki bai sanar dake komai a kai ba?"

Ta ce "Wallahi bai gaya min komai ba."

Ya ce "Ni dai nafi son kuji daga gareshi."

Momy ta ce "Babu komai,in kaima ka sanar damu."

Ya ɗan ɗaga murya ya ce "Ke Fati." Ta amsa, ya ce "Kira min Ruƙayya ku zo harda Murja.."

Suka shigo da sallama ciki suka wuce suka zauna, Dady kam ko kunya ya tsurawa Ruƙayya ido, ita kam sunkuyar da kai tayi tana tunanin Allah yasa Affa ya amince su auri juna.

Ya dube su duka, sannan ya ce "Hajiya ina son ki bani aron hankalinki har da naku ku ma,ki min adalci shin ya dace na bada Æ´ata ga É—an wanda ya yi min wannan aikin.?

Wata sansayar yamma ce ta ranar Laraba ina aiki cikin gonar gadon mu da mahaifina ya rasu ya bar mana ni da ƙannena mu goma sha ɗaya mu biyar mazane shida kuma mata,mu huɗu da ƙannena uku muna aikin noman rani da damina sai ga wani mai gadi nan kusa damu mai suna Isa ina aiki ya shigo muna gaisawar zumunci da Isa shi yana gadin filin former I.G Alhaji Mansur Yusuf ƙaton fili ne kuma an zagaye shi da katanga, shi wannan filin rabin shi na mahaifinmu ne, former I.G ya karɓa ya bashi dubu sha biyar amma can lokacin,ya nemi gwamnati ta mallaka mishi filin wanda a yanzu zai kai miliyan hamsin.

Malam Isa ya ce dani "Malam Sani an aikoni gurinka." bayan mun zauna sai yake min bayanin Alhaji Mansur mai gidan shi yana son gani na,na ce to ko lafiya? Ya ce lafiya lau ina ga dai alheri ne dan mai gidan namu mutumin kirki ne,na je na kira ƙanina Sulaiman na ce yazo mu je.

Affa ya dubi Momy ya ce "Kina ji na?"
Ta ce "ina jin ka."
Chapter 5 · 0% Book details