← Book details Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 12

Sashe 8

Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Murja ta ce "Jiya ko can gidan su muka wuni,sai faman labarin auren ki muke yi sai kace bikin ya zo."

Ruƙayya ta taɓe baki ta ce "Ni fa shiyasa bana son muyi hutu saboda zancen auren nan."

Murja ta na dariya ta ce "Ka ji yarinya ba dole ai miki zancen aure ba tunda kin isa."

Ruƙayya ta ce "To ai banida saurayi."

Murja ta ce "Aƙwai wani faruk ƙanin Baban Mama yasha min zancen ki,yana da kirki, gashi yana da aikin shi."

🖊️🖊️🖊️
[7/28, 18:44] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 2*

*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

Page 5

Ruƙayya ta ce "A ina ya ganni kin da mishi tallata." Ta ce "a'a zuwan ki da sallah ya ganki kin ma san shi wanda yazo na ce ki kawo mishi abinci har ma yace ya ƙoshi sai dai a bashi drink mai sanyi."

Ta ce "Ok na tuno shi gaskiya nidai be min ba."

Murja ta ce "Eye,ƙyau kika fishi ko iya ado ka jiki dan ma yace yana sonki."

Ruƙayya ta ce "Ya je da ƙyaunsa na yafe." Nan ta yi sannan ta dawo gida."

Washegari gidan Yaya Fati ta yi, Yayyanta kamar haÉ—in baki duk wanda ta je gurinshi sai ya yi mata zancen aure, takaici ni dai karatu zanyi tunda ku duk an rasa me yin sa kowacce daga secondary ta sare,sai su ce aiko badai a gidan Affa ba dan ba zaya yarda ba, ta ce to shikenan zaku gani.

Umma ta dubi Ruƙayya ta ce, "Auta ina ji kusan minti goma kenan da shigowar yaro ya ce ana sallama dake,ko kin manta ne."

Ta ce "Ƙyale su Umma samarin unguwar nan ƴan rainin wayo ne, ƙanana dasu ba a gama wanke musu kashi ba,sai ki gansu wai sun zo taɗi."

Umma ta harare ta "Dalla ni ki tashi ki fita,wato ke kin fi son kiyi ta zama damu gashi kin kusan gama makaranta, Allah ya baki sa'a kin san dai Affanku,ya iya wanke ki ya ba wani."

Cikin tura baki da fushi ta fita,Nasir ta gani tsaye da laida ranta ya ɓaci ta dube shi "Yaya ne Nasir na ganka a gidan mu.?"

Ya yi murmushi "Nasan dole ki tambaya zahirin gaskiya na jima ina son ki so na haƙiƙa na aure shiyasa na ce bari in zo dan hausawa suna cewa da zafi-zafi akan bigi ƙarfe."

Haushi ya kama Ruƙayya ta ce "Nasir ina matuƙar ganin girman ka kada muyi haka da kai dan zahiri zamu ɓata,ka kama kanka danni ba aure a kaina."

Da sauri ya dubeta "Saboda me?"

Ta ce "Wannan ba damuwar ka bane kai dai ka janye."

Ya ce "Ni kam sai naga ƙal uwar daka."

Ta ce "shikenan,ta juya tayi gida."

Shiru yayi na ɗan lokaci sannan ya wuce yana saƙa yanda zai ɓullowa abin.

Duk irin korar da tayi ma Nasir bai ji ba haka ya liƙe mata tamkar cingam, gashi in yazo ko taƙi fita sai Umma ta kora ta ya yo mata ɗin kunanta tsala-tsala sai ma taji ta tsani zannuwan,ban da ma zannuwan na cikin kayan da Dady yabar mata ne, Allah da bazata sa su ba,dan dai tana matuƙar son kayan dan suna sa ta cikin begen Dady tana alfahari da kayan ba dan kasancewar su masu tsada ba,sai dan kasancewar su daga Dady.

Dama ta ƙosa su koma makaranta dan haka hutun su na ƙarewa ko yini bata ƙara ba,ta koma ita da in sun koma sai tayi kusan ƙwana uku, ta ce ba'a komai. Nasir ma bata sanar dashi ba sai dai ya shafa ya ji bata nan, sai da ta koma a group ɗin su ita kaɗai ce tazo, amma duk da haka sai taji gara haka tunda ba mai damun ta da zancen aure bayan ƙwana biyu sauran suka iso. Matuƙa Ruƙayya tasa kai ga karatu sosai ba wasa don haka koda jarabawa sai taji mata sauƙi, ta kuma sa kai sosai, saboda tana son cigaba da karatu.

Ranar yayesu sun sha kukan rabuwa ita da ƙawayenta, bayan an watse daga taron na bada ƙyaututtuka,a mafiya yawan ƙyautukan Ruƙayya Sani ta amsa mutane da wasu iyayen sun yi sha'awar ta. Affa da Fati da Murja da Yaya Amina da yaran Yaya Sadiya duk sun je, mota guda suka yi,mijin Fati ya kai su,dan haka Affa ya yi alfahari da Ruƙayya, haka Yayyanta. Wasu kusa dashi suna faɗin "Kai Iyayen yarinyar nan sun ji daɗi ina ma su barta ta ci gaba da karatun da wannan ƙasa zata ƙaru da ita,ga tsafta ga tarbiyya duk itace ta amsa,Ɗayan ya ce gaskiya da sun ƙyauta,in sun barta aima duk ƙyautukan masu mahimmanci duk ta amshe, gashi shi kanshi mai bada ƙyautukan sai da ya bata tashi,ko menene ciki Oho. Ɗayan ya ce kuɗi ne na sani.

Hotuna dai sun ɗauka kamar me, sun yi kuka sosai sun rabu da alƙawarin za su zo Kaduna kawo mata hotunan bikinsu. Da Amira suka taho suka sauke ta Zaria, ta ce zata zo Kaduna very soon don aƙwai Yarta a unguwar Rimi zata nemi Ruƙayya.

Suka yi sallama, mijin Yaya Fati Baban Muhsin sai tsokanar Ruƙayya yake yi, ya ce "Ruƙy yanzu sai maganar aure ko?"

Ta ce "Allah shi ƙyauta sabon karatu zan dasa ko baka ji abin da mai raba mana ƙyautuka ya ce ba.?"

Ya ce "Naji yana ba iyayen ki shawara akan su barki ki ci gaba da karatu, har ma ya ce gata shi gudunmuwar nan ki sai form.".

Ta ce "To shi ne zaka kira min aure? To ni mijina koma ƙeroshi ba'ayi ba."

Ya ce "Kedai ki faɗa in baki dashi ne ki faɗa sai in fito duk da dai matata tafi ki ƙyau in rufa miki asiri."

Ta harare shi "Kama faɗa ka ce matarka tafi ni ƙyau,sai dai ta nuna min fari,farin me,ga kala ta ƴar yayi,jikina golding ne kasan ko ba kowa ke da wannan kalar ba,sai ɗan baiwa. Ni one in town ce a garin Kaduna ba ta biyu na,da fatan ka gane."

Duk dariya suka saki dama Affa ta haya ya biyo ya ce in zauna a gurin shi haka muka iso ana raha, don haka sai na manta da tunanin ƙawayena.

A gida mun samu Umma ta tsara mana É—an wake da mai da yaji harda Æ´ar miya ga mai so,Nasan tayi ne donni, don haka ban bata kunya ba,gurin ci ina santi na ce "Allah ya bar min ke Umma, ta ce "au to, Allah ko bazai barni ba, sai dai in lokaci na baiyi ba.

Ruƙayya ta ce "Umma bar faɗi, Umma sai kinga jikokina da tattaɓa kunne na." Suka sa dariya.

Umma ta ce "Allah ya tsare ni."

Haka suka yi ta raha da ƴan'uwanta da Umma, sun kuma duba ƙyautukan suna ta murna har zuwa kan ƙyautar mai bada ƙyautuka,wato ƙwamishinan ilimin jihar Katsina.

Check ne na zunzurutun kaÉ—i har naira dubu É—ari biyu da hamsin inda ya bada check É—in bankin arewa.

Suna ta murna, Affa ya shigo ya samu gidan tamkar sallah, Umma ta tashi ta ce "kun ga bari naje gurin tsohon mijina." Ta fita suna mata dariya, suka ce kije ki duba shi muma munfi son haka ."

Cikin sa'a Affa ya yarda Ruƙayya ta ci gaba da karatu, don haka sai ta siyo jam form dama da result ɗin ta ya fito taga yanda tayi tsammani, don duk set ɗin su ba mai yawan credit ɗin ta.

Sun yi jarabawar jam bayan ta fito suka duba, cikin sa'a ta samu Bayero Kano kuma sun bata Course É—in da take so wato law.

Kuɗin ta da ƙwamishina ya yi mata ƙyauta gaba ɗaya ta amso su, kuma ga kuɗin da Dady ya bar mata ko taro Affa bai ci ba, don haka aka soma shige da fice inda kuma ta je tayo registration, sannan ta zo ta kammala komai sai makaranta, kafin tafiyar ta tasha nasiha gurin Affa da Umma,sun kuma hore ta data tsaya tsayin daka tayi karatu dan shi ya kaita,ta kame kanta tare da maida kai gurin ibadarta. Tai musu alƙawarin bin yadda suka ce tare da tsare dokar Ubangiji.

Ta soma karatu cikin nasara ba wani problem hutun farko da ta dawo sun yi bikin Safiya dana Walida,sati É—aya tsakanin su sun sha zirga-zirga tsakanin Katsina da Funtuwa, samarin Katsina sun sha kai hari ta ce no way.
Chapter 8 · 0% Book details