← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 34

Sashe 33

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani cool murmushi Inaya ta saki kafin ta ce " ba za ta bar wajen nan ba sai ta cire abun da ta yi wa momy , idan kuma ta dauka da wassa na ke bismillah ga hanya nan " ta kai karshen ta na nuna mata hanyar fita

cikin bacin rai Rouksar ta ce mata " ba ki da hankali wlh " ta kai karshen ta na fara takawa

da sauri Tesnim ta bi bayan ta ta na fadin " Rouksar , please ki ts....... "
ba ta kai karshen maganar ta ba ta ga Rouksar ta tsaya cak ta na sakin wata yar karamar kara ta dafe saitin zuciyar ta

" Rouksar , lafiya ? " Tesnim ta fada ta na nufar Rouksar
da sauri Inaya ta riko hannun ta , ta na fadin " Ki tsaya kar ki taba ta " ta kai karshen ta na janyo ta da karfi ta yo baya har sai da ta fadi kassa

a rude Tesnim ta mike ta na kallon Inaya ta ce " baby , lafiyar ki kuwa ? " ta kai karshen ta na fara takawa za ta nufar Rouksar da ta Zube a kassa ta na murkuso

da sauri Inaya ta riko ta da duk hannayanta biyu ta na fadin " Aunty Tesnim , kar ki taba ta , don Allah wlh za ta cutar da ke , asirin da ta yi wa momy ne na kare "

cak Tesnim ta tsaya ta na kallon Inaya irin kallon nan na rudu kafin ta juya ta kali Rouksar
a hankali Rouksar ta mike sai faman hakki ta ke yi , murya a disashe ta ce " me ki ka yi wa bishiyar nan ? " ta fada ta na kallon Inaya idanun ta cike da ruwa har wani lumshe su ta ke kamar mai jin barci

cikin ko in kula Inaya ta ce mata " na sa a cire ta , kuma na san yanzu haka sun kusa Kamalawa "
Dum Rouksar ta ji zuciyar ta ta buga wata yar karamar kara ta saki ta na fadin " No , me ya sa za ki yi haka , ba ki san abun da ki ka aikata yanzu , na tabbatar miki abun da zai biyo bayana ba za ki iya yaki da shi ba "

ba ta gama rufe bakin ta ba Tesnim ta daga murya ta na fadin " ya isa haka , wai maganar me ku ke yi haka ? na kassa ganewa "

Har Rouksar ta bude baki za ta yi magana kawai ta ga Ruhin MALIKAT AL'UMU ya shigo dakin ya nufi MALIKAT AL'UMU zai koma jikin ta
a dubu dari Rouksar ta yi kokarin kamo shi ta na sakin wata yar karamar kara
amma ina ko taku biyu ba ta yi ba ya shiga jikin MALIKAT AL'UMU

wani irin dogon nunfashi MALIKAT AL'UMU ta ja kafin ta ware idanun ta a dubu dari ta mike zaune ta na nunfashi da karfi

a dubu dari Inaya da Tesnim su ka nufe ta su na fadin " momy , momy "
a rude MALIKAT AL'UMU ta ke kallon wajen ta na fadin " Baby , Tesnim , me mu ke yi a wajen nan kuma ? "

har Tesnim ta bude baki za ta yi magana su ka jiyo Muryar Rouksar ta na fadin " why , why za ki yi haka , ba ki san abun da ki aikata yanzu ba , wlh abun da zai biyo baya ya fi karfin ku baki daya "

a rude su ke kallon Rouksar ta Zube a kassa , nan take idanun ta su ka sauya su ka koma na maciji , har skin din ta ta koma ta maciji

a razane Tesnim da Inaya su ka saki kara su ka fada jikin MALIKAT AL'UMU su na sakin kara , MALIKAT AL'UMU kuma ta na faman karanto addu'ar tsari
su na a haka kawai su ka ga Rouksar ta koma wani dankareren maciji
wata irin razananiyar kara ce Tesnim ta saki ta na kara shigewa jikin MALIKAT AL'UMU ta na karanto kalmar shahada
karar da ta saki ne ya sa Guards din da ke tsaye bakin kofar su ka shigo
su na ganin macijin Rouksar su ka tsaya cak su na karanto kalmar shahada , nan take su ka fiddo gun su ka fara harbin shi
amma ina ko a jikin shi , nan take ya sa wutsiyar shi ya buge guards din nan su ka yi cikin bango su ka fadi

su na faduwa Inaya ta raba jikin ta da na MALIKAT AL'UMU
da sauri Tesnim ta riko hannun ta ta na fadin " kar ki tafi za ta cutar da ke "
da karfi Inaya ta kwace hannun ta , ta fara takawa ta nufi macijin nan lips din ta na motsi allamun ta karanto wani abu

ta na karasowa dab da macijin nan idanun ta su ka koma bakin kirin ko digon fari babu , a hankali gown din jikin ta da Alkyabar ta su ka koma baki kirin , har wani bakin hayaki ke tashi da ga saman su , veil din ta ya warware da kan shi ya fado kassa , gashin ta ya fara yin sama , bakinshi ya kara cizawa har wani kwarri ya yi kamar an nadde shi

Tesnim na ganin haka ta fadi sumamiya a wajen dan abun ya fi karfin ta , MALIKAT AL'UMU kuma bayan kalmar shahada ba abun da ke fitowa da ga bakinta , zancen guards kuma a bar ma maganar su dan tun bugewar ban da maciji ya yi musu , su ka sume a wajen

a hankali Inaya ta daga hannu sama , kamar da ga sama wata katuwar sword baki kirin mai mugun tsawo ta fito cikin hannunta da ta daga sama
move guda ta yi da hannunta ta raba macijin nan gida biyu da takobin hannunta
nan take wata bakar guguwa ta tashi ta mamaye sa-san macijin nan kafin ta bace bat tare da macijin kamar ba a taba yi ba

ya na bacewa ko Malik da Diya su ka turo kofar dakin su ka shigo kamar an koro su , lokacin da guards din nan su ka shigo dakin guda cikin su ya juya da sauri dan ya je ya fadawa Malik abun da ke faruwa

cak Malik da Diya su ka tsaya su na kallon Inaya tsaye da wannan sword a hannun ta ga idanun ta sun koma bakin kirin ba karamar razana Diya ya yi ba har ya fara karanto kalmar shahada

a hankali Malik ya daga kafa ya karaso cikin dakin , kafin ya yi taku biyu wannan sword din hannun ta ta bace bat , kaya jikin ta su ka koma kamar da farko , a hankali ta fara lumshe idanunta , ta fara yin kassa allamun sumewa za ta yi

da sauri Malik ya tako ya riko kugun ta ya janyo ta jikin shi , ya daura hannunshi saman kumatunta ya fara bubugawa a hankali ya na cewa " Cutie , Cutie ! "

wani irin dogon nunfashi Inaya ta ja , a razane ta ware idanun ta ta na sakin kara
da sauri ya rungume ta jikin shi ya na fadin " calm down ba abun da ya faru "
ta na jin Muryar shi ta sauke wata nanauyar ajiyar zuciya

a hankali ya dago ta da ga jikin shi ya talabo face din ta da hannayanshi ya ce " shikenan ? "
a hankali ta gyada mishi kai ta na sakin wani dan karamin murmushi
lips din shi ya kai saman forehead din ta ya manna mata kiss kafin ya raba ta geffen ta ya nufi MALIKAT AL'UMU ya riko hannayan ta ya ce " momy , ki na lafiya ? "

a rude MALIKAT AL'UMU ke fadin " Nawfel , mafarki na ke yi amma ko ? "
cikin sigar rarrashi ya ce mata " calm down momy , ba abun da ya faru , ki kontar da hankalin ki "

da sauri ta katse shi da cewa " Nawfel ta ya za ka ce na kontar da hankalina , yarinyar da ta girma gaban idona ta koma maciji , ni , ni , ni ban ma san yadda zan kwatanta maka , wacece yarinyar nan da ka kawo matsayin matar , wlh mutum ba ce aljana ce " ta fada da allamun ta fita cikin hayacin ta

a hankali Malik ya juya ya kalli Inaya da ke tsaye kamar an dassa ta a wajen
wata yar karamar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juyo ya kalli MALIKAT AL'UMU ya ce " momy , ba abun da ya faru , ki kontar da hankalin ki please "

a hankali MALIKAT AL'UMU ta sauke ajiyar zuciya ta na lumshe idanun ta , ya na jin ta sauke ajiyar zuciya ya juya ya kalli Tesnim da ke konce a wajen

hannu ya kai hannu wajen yar drawer da ke bakin gadon , ya dauki bottle din ruwa guda , ya bude ya zuba kadan a hannunshi ya yarfawa Tesnim

wata razananiyar kara ta saki ta na dawo cikin hayacinta kafin ta mike da sauri ta fada jikin MALIKAT AL'UMU ta na sakin kuka kamar mahaukaciya

a hankali ya daura hannun shi saman face din Tesnim ya na fadin " Tesnim , ki kontar da hankalin ki please "

slowly ta ware idanun ta , ba su sauka ko ina ba sai cikin na Inaya
wata yar karamar kara ta saki ta na lumshe idanunta da karfi ta kara kankame MALIKAT AL'UMU

cikin sanyin murya Malik ya ce mata " Tesnim , ki kontar da hankalin ki ki fada min abun da ya faru "

ba tare da ta bude idanun ta ba ta shiga ba shi labarin abun da ya faru tun shigowar Inaya dakin har zuwa lokacin da ta suma
Chapter 33 · 0% Book details