← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 34

Sashe 2

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shi dai Malik shiru ya yi ya lumshe idanun shi ya na sauraron su
cikin bacin rai ya bude idanun shi ya ce " Silence !! " ya fada da karfi duk sai da su ka razana ba shiri kowane ya ja bakin shi ya yi shiru ba

a hankali ya dago kai ya kali Diya
da sauri Diya ya sunkuyo da kan shi ya na sauraron abun da Malik ya rada mishi

gyada mishi kai kawai ya yi kafin ya koma ya tsaya
juyowa Malik ya yi ya kale su ya ce " ku na shaida a ranar da na hau kujerar nan , na yi Alkawari kwatarwa duk wanda ya kawo min kukan shi hakin shi ko da kuwa mai laifi ne , kamar yadda a ka kamo shi da sunnan ya kashe Malik , haka shi ma ya kawo min kukan shi domin na ceci Matar shi , bai kamata mu yanke mishi hukuncin ba tare da mun saurare shi , ba tare da mun ji dalilin shi na kashe Malik , abu guda zan fada muku , Abdoul Hakim ya fada min gaskiyar abun da ya faru , ya kuma fada min dalilin shi na kashe Malik , na yi muku alkawari duk wanda ya saka shi yin wannan aikin sai na kamo shi na yanke mishi hukunci dai'dai abun da ya aikata , na farko na saka shi kashe Malik , na biyu kuma Matar shi da ya sace , ko wanene idan na kamo shi zai fuskanci hukunci ba ruwa na da matsayin shi a waje na ko a cikin masarautar nan "
ya na gama fadar haka ya tashi ya fara takawa cike da Izza ya fice fadar , da sauri Diya ya bi bayan shi su ka bar wajen

kowane dai kallon shi ya ke , sun kassa cewa komai amma da ga gani ga tsoro nan konce saman fuskokin su , Ba karya General ya yi ba , yanzu duk wanda ya saka Hakim yin wannan aikin sai shiga tayi tayin shi , a nan ne wajen ceton kan shi zai yi mistake har a kama shi

bangaran Malik kuwa su na fitowa ya mika wa Diya Laptop din shi ya ce ya sa a kai shi part din shi , zai wuce wajen MALIKAT INAS
ba musu Diya ya karbi laptop din ya juya
har sun yi hannun riga Malik ya juyo ya ce mishi " Diya ya jikin Nesrine ? ta samu sauki ? "

juyowa shi ma Diya ya yi ya na murmushi ya ce mishi " don't worry , kawai Fever ce ta ke amma yanzu ta samu sauki "

gyada kan shi kawai Malik ya yi ba tare da ya ce komai ba ya juya ya ci gaba da takawar shi

kai tsaye part din MALIKAT INAS ya nufa dan ya san ita kadai ce za ta iya ba shi amsar tambayar shi

Bakin shi da Sallama ya shigo parlourn ta
nan ya tardo ta zaune tare da RIANNA su na hira fuskokin su dauke da murmushi

MALIKAT INAS na ganin shi ta tsuke fuska ta kauda kai gefe
sai da ya karaso cikin parlourn ya zauna saman sofa geffen RIANNA sannan ya ce " Ina kwana Ammie "

" lafiya " ta fada a takaice ba tare da ta juyo ba

yar karamar dariya RIANNA ta yi kafin ta dafa shoulder din shi ta ce " Akhie ina ga Ammie fushi ta ke da kai "

" Da gaske Ammie ? " ya fada cikin sanyin murya
tsuke fuska ta yi ta na kara kauda kai gefe
a hankali ya mike da ga saman sofar shi , ya tako ya dawo gaban ta ya zauna saman carpet ya kai hannu ya fara murza mata kafa ya na fadin " duk da ban san laifin da na yi ba , amma ina neman afuwar ki , Kin san ba na son ganin ki cikin fushi please Ammie kar ki ce za ki yi min fushi , wlh ba zan ji dadi ba "

a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce " Nawfel , ni fa wassa na ke yi maka ba fushi na ke ba "

a hankali ya kontar da kan shi saman cinyar ta ya ce " na sani , ai ba karamin abu zai sa Ammie na ta yi fushi "

" duk da hakan ina fushi da kai , tsakani da Allah yanzu Nawfel yaushe rabon da ka zo waje na ? ko da gaisuwar tsaye ya ce ? " ta fada ta na marairaice murya

dan lumshe idanun shi ya yi kamar mai jin barci ya ce " I'm sorry Ammie , ke ma yanzu kin san aikin da ya karun min "

cikin nitsuwa ta katse shi da cewa " Kar ka damu , na sani Allah ya taya ka riko bisa gaskiya kamar yadda mahaifin ka ya yi "

a tare shi da RIANNA su ka amsa mata da Ameen
sannan RIANNA ta ce " Akhie wai , ina baby ta yi ne na yi kwana biyu ban gan ta ba "
" wace baby ? wlh Ukhtie na lura duk ke ki ka bata yarinyar nan , sai ta kashe ni sannan ki huta "

dariya sosai RIANNA ta yi har ita kan ta MALIKAT INAS
sai da ta gama dariyar ta sannan ta ce " Nawfel fadi gaskiya ko dai kai ne ka ke takurawa babyn ta mu , na ji an ce har yaji ta yi maka "

da sauri ya dago kan shi fuska cike da mamaki ya ce " How do you know that ? "

yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mishi " Nawfel , ai labarin masarautar nan ba ya boyyiwa "

a hankali ya koma ya kontar da kan shi saman cinyar ta ya ce " to babu ruwan ku dai "
" Akhie , Fadi gaskiya me ka yi wa baby " RIANNA ta fada

lumshe idanun shi ya yi sannan ya ce mata " da ya ke ita yar aljanna ce ba ta laifi , sai na ma kara aure na huta da rigimar ta "

ya na gama fadar haka ya ji MALIKAT INAS ta sa hannu ta murde mishi kunne
kamar karamin yaro ya dago kai ya na cewa " Ammie , sake min kunne na da zafi fa "

" yi min shiru mara kunya kawai , yanzu baby tawa za ka yi wa kishiya ? A hir din ka wlh ban yarda da haka ba "

" Ammie ni fa wassa na ke miki "

a hankali MALIKAT INAS ta sakin mishi kunne , sannan RIANNA ta ce " Akhie , wlh duk ranar da ka yi wa baby kishiya ni da kai mun yi hannun riga , me ta yi maka haka kawai ? "

meda kan shi ya yi saman cinyar MALIKAT INAS cikin sanyin murya ya ce " in da a ce ina da Niyyar kara aure da lokacin da Mohammed ya ba ni auren Hafsat ba zan ce a'a ba , Ukhtie har ga Allah ba na tunanin zan iya zama da wata matar bayan Cutie , Ita kadai ta san sirri na ita kadai ke iya saka ni cikin nitsuwa , ita kadai ke iya saka ni cikin farin ciki kuma har duniya ta nadde ba za a samu ta biyu ta a waje na , kamar yadda ta ba ni ragamar rayuwar ta na yi yadda na ke so ita , haka ni ma na ba ta ragamar rayuwa ta ta yi yadda ta so da ita "

wani kyawatencen murmushi RIANNA ta saki ta na cewa " iyeeeee , Ammie ki na ji ko , yaron ki fa ya fada tarkon soyayya "

lumshe idanun shi Malik ya yi kafin ya ce " Ai ni dama na jima da fadawa "

murmushi mai dan sauti MALIKAT INAS ta yi ta kai hannu saman kan shi ta fara shafawa a hankali ta ce " Ka ce mu fara shirya kayan baby "

" wane kayan baby kuma ? " ya fada idanu a lumshe

MALIKAT INAS na shirin magana RIANNA ta riga ta cewa " Ai dama soyayyar ita ce step na farko , aure step na biyu , Step na uku kuma babys , a na ku labarin auren ne ya zo a step na farko no wonder , mun wuce step na biyu yanzu , kennan mu na cikin step na uku wato babys , na san a zaman da mu ke yanzu you are not virgin ko kuwa ? "

ba shiri Malik ya bude idanun shi ya na kallon ta ita ko kunyar fadin haka ba ta ji ba

ya na shirin magana Ya jiyo Muryar MALIKAT INAS ta na fadin " Kar dai ka ce min har yanzu ba ka yi dis virgin din ta ba ? "

" wayooo ni Nawfel na shiga uku hannun matan nan , ina ruwan ku da Sex life di ta , ko kunyar fada min haka yanzu ba ku ji ba ? " Ya fada ya kamar zai yi kuka

❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤

(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

💫🌸 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )🌸💫

STORY & WRITTEN BY : MEERAH 👑🔥

【THE ROYALTY LOVE 👑🕊❤】

《BOOK ________3 ✍📚🔥》

_______________________🕊❤🕊❤🕊❤🕊❤🕊❤🕊❤🕊___________________

P A G E 2 🥀 ❤

dan karamin tsaki MALIKAT INAS ta yi kafin ta ce " Tom sai a ka yi me , ni fa na haife ka dan na tambaya in ka yi dis virgin matar ka shi ne laifi ? mu de tambaya ce mu ka yi kuma dole ka ba mu amsa "

" dama ban zo wajen nan ba " ya fada ya na kokarin tashi

da sauri MALIKAT INAS ta medo shi ya zauna ta na dariya ta ce " shikenan kar ka tafi dawo ka zauna wassa mu ke maka "

ba musu ya dawo ya zauna ya na kauda kai gefe ya ce " sai na daina zowa wajen ki tun da haka ne "
Chapter 2 · 0% Book details