← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 34

Sashe 11

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakim na jin Muryar ta ya ji zuciyar shi ta yi mugun bugawa , a hankali ya dago da kan shi dan a sunkuye ya ke tun lokacin da ya Kamala maganar shi
ya na ganin ta , Ya dan zaro idanu , ya ma manta da mutanan da ke wajen ya tashi da sauri ya rungume ta ya na sakin wani dan karamin kuka ya ce " Najoua , da gaske ke ce ? ba abun da ya same ki ? ba su cutar da ke ba ko ? "

ya kai karshen ya na raba jikin shi da nata , ya talabo face din ta da hannayan shi biyu
Dum ya ji gaban shi ya fadi lokacin da idanun shi su ka sauka saman shatin hannun mutum a face din ta , da allamun marin ta a ka yi ba guda ba dan wajen ya yi jazir

cikin bacin rai Hakim ya juya ya kai wa Miram wani mugun bugu a fuska ya na fadin " wa ya ba ka izinin taba min ita ? "

da sauri Sojoji su ka taho su ka ririke Hakim dan da ga gani zai iya kashe Miram
Cikin nitsuwa Malik ya ce mishi " Hakim , ka fara tambayar ta wanda ya yi mata hakan tukunna "

cak Hakim ya tsaya ba shi kadai ba duk mutanan fadar sai da hankalin su ya koma kan Najoua
Umarni Malik ya ba wa sojojin nan a kan su saki Hakim
ba musu su ka sake shi su ka dan ja da baya kadan

su na sakin shi ya juya ya kali Najoua ya ce mata " baby , ki kontar da hankalin ki ba abun da zai yi miki , ki fada min waye ya dake ki "

ba ta ba shi amsar tambayar shi ba ta sa hannun ta dama ta yi sama da hannu abayar ta na hagu ta na kuka ta ce " ni ba duka na ya yi ba abun da ya fi duka ya yi min "

a rude Hakim je ce mata " please baby tell me , ki fada min na yi miki alkawari ba zan kyale shi ba "

girgiza mishi kai ta yi murya kassa kassa yadda shi kadai zai ji ta ce mishi " He tried to rape me " ta kai karshen ta na kara sautin kukan ta

Dan zaro idanu Ya yi ya na maimaita abun da ta fada cikin zuciyar shi , ya na shirin magana ya jiyo Muryar Malik ya na fadin " Miss Najoua , za ki iya gwada mana wanda ya yi miki hakan ? " ya fada kamar ya ji abun da ta fada

a hankali ta dago kai ta kali Malik sannan ta gyada mishi kai a hankali ta kali saitin Maza ta na bin su da kallo daya bayan daya
cikin rudu Hakim ya ce mata " ga wanda ki ke magana a kai nan why ki ke kallon wani wajen daban ? " ya fada ya na nuna mata Miram

girgiza mishi kai ta yi ta na cewa " no ba shi ba ne , wancen ne " ta fada ta na nuna shi da yatsa
a tare duk su ka kali saitin da ta nuna , nan su ka ga ashe Mohammed ta ke nunawa

su na a haka su ka jiyo Muryar Miram ya ka cewa " Ran ka shi dade har da shi , tare mu ka kashe Malik , shi ya kawo shawarar kashe shi "

da sauri Mohammed ya katse shi da cewa " kai Miram ka san abun da za ka fada , ranka shi dade wlh karya ya ke min , babu ruwa na cikin abun da ya aikata "

ya na gama rufe bakin shi Najoua ta ce " ranka shi dade karya ya ke , wlh har da shi , tare su ka yi wannan aikin sun sha kawo min ziyara a tare " ta fada da karfi kamar za ta yi kuka

mikewa tsaye Mohammed ya yi ya na girgiza kai ya na fadin " wlh ranka shi dade karya su ke min , dalilin mi zai sa na kashe Mal ...... "

bai kai karshen maganar shi ba Malik ya katse shi da cewa " saboda ba kai a ka nada a matsayin Malik ba duk da kai ka auri babbar y'a ga Mai martaba Malik Abdoul latif bin Saud ba "

Dum Mohammed ya ji gaban shi ya fadi har wani zaro idanu ya ke ya na kallon Malik

a hankali Malik ya mike tsaye , da sauri mutanan wajen su ka yi kokarin tashi , sai dai ya daga musu hannu a kan su zauna , ba musu kowane ya koma ya zauna ya na kallon Malik

a hankali ya yi taku biyu sannan ya tsaya ya rike hannayan shi a baya ya ce wa Mohammed " kamar yadda na fadawa shi Miram , duk wani abu da ke faruwa cikin masarautar nan ina sane da shi , ko da kuwa gwayar zarra ce , kawai dai ina shiru ne na ga gudun ruwan ku , ko ka zata ba ni da masaniya a kan abun da ku ka shirya , na san kai ka kawo shawarar kashe Malik , da farko Miram bai yarda ba amma ka matsa mishi , tun kafin na dawo masarautar nan ku ka shirya wannan , tare auren Gimbiya RIANNA da Miram yadda da kun kashe Malik a nadda Miram matsayin Malik tun da ba na nan yadda za ku yi yadda ku ka so cikin masarautar nan , amma shirin ku ya ruguje bayan dawowa ta , duk da hakan sai da ku ka saka a kashe Malik , da ga baya ya zagayo ya kashe ni , amma General ya yi nassarar kamo Sniper din da ku ka saka aikin , bayan an kai Hakim prison , sai da ka je wajen shi ka yi mishi kashedi a kan kar ya fada min gaskiya a kan cilas ta mishi a ka yi ya kashe Malik , amma bai saurare ka ba ya fada min , bayan na yi maganar a fada , shi ne ka tsorata , ka je wajen Miram , ka ba shi shawarar ku kashe Hakim tun kafin ya bayana gaskiya , a ranar da Miram ya yi kokarin kashe shi a cell , a tare ku ke , sai dai kai , ka tsaya a bakin kofa ba ka shiga cell din ba , ta yadda ko an tashi kamawa , Miram ne za a kamawa ko ba haka a ka yi ba ? " ya kai karshen ya na dagawa Mohammed gera guda

wasu wahalalun yawu Mohammed ya hadiye , ramin da ya gina ya rumzo mishi , ta ina zai fita yanzu ?
GASKIYA MALIK KA CIKA DAN SA IDO 🤣🤣 NI BAN MA SAN WANNAN LABARIN SAI DA YA FADA , GASKIYA NA SARA WA BASIRAR KA 😂😂

ya na a haka kawai ya jiyo Muryar Malik ya na fadin " Mohammed Magid , Miram bin Salman , an kama ku da laifin kisan marigayi Malik , ko ku na da abun fada kafin na yanke muku hukunci ? "

da sauri MALIKAT AL'UMU ta ce " Ranka shi dade me kuma za su ce ? A yanke musu hukunci dai'dai abun da su ka aikata , dama dokar musulumci ta ce wanda ya kashe a kashe shi , hukuncin kisa ne kawai ya dace da su , dalilin su ɗiya na guda uku sun rasa mahaifin su , ni da yar uwa ta mun rasa mijin mu , wace damar magana za a ba su kawai a kashe su kamar yadda su ka kashe shi " ta kai karshen ta na sakin kuka

a hankali MALIKAT INAS ta sa hannu ta janyo ta jikin ta ta rungume dama Sofar su a kusa ta ke , Ita kan ta ba ta taba tunanin mijin yar uwarta zai raba ta da nata mijin , idan ta ce ta yi magana ta san Manisha ba za ta ji dadi , shi ya sa kawai ta yi shiru amma har cikin zuciyar ta ta na bayan maganar MALIKAT AL'UMU

Shi dai Malik shiru ya yi ya na sauraron abun da su ke fada , kawai ya tsare Mohammed da idanu babu ko kiftawa , shi dama ya na sane da kishin da Mohammed ke yi wa mahaifin shi , dan tun ya na yaro Mohammed ya sha tsangwamar shi , ya na dukan shi , har ya zagi Malik gaban idan shi , amma bai taba nunawa ba

A hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya bude baki ya ce " duk wanda ke son yin magana , na ba shi dama , ya yi maganar shi "

a hankali Miram ya dago kai ya ce " ranka shi dade , ko cell za a saka mu kar a hada ni da shi "

" kar ka damu kowane za a saka shi cikin ta shi cell din " Malik ya fada cikin nitsuwa

da sauri Mohammed ya kali Miram ya ce " maciya Amana kawai "
wani murmushi mai dan sauti Miram ya yi kafin ya ce " Ai kai ne wanda za a kira da maciya amana , kai da kashe mijin kanwar matar ka , sannan ka yi wa yarinyar mutane fyade , ko kunyar shekarun ka ba ka ji ba "

da sauri Najoua ta ce " bai yi nassara ba "

wani dan karamin murmushi Miram ya yi kafin ya dago kai ya kale ta ya ce " ai ni ba a kan ki na ke magana ba "

da sauri Mohammed ya ce mishi " kai Miram kar ka yi min Kazafi dan kwatar kan ka "

hararrar shi Miram ya yi kafin ya juya ya kali Malik ya ce " ranka shi dade , mai girma Rafik , Mohammed shi ya kashe maka yarinyar ka , Tun da lokacin tonan asiri ne , ba zan kyale ka ba "

a dubu dari Rafik ya mike ya na fadin " Miram , ka na nufin Mohammed shi ya kashe Rhalida ? "
Chapter 11 · 0% Book details