← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 34

Sashe 13

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a hankali ya bude baki ya ce " Me ya faru ? " ya kai karshen ya na daga mata gera guda
marairaice mishi fuska ta yi ta na fadin " sai da na ce maka kar ka hadiye "

har ya bude baki zai yi magana kawai sai ya shiga cough , idanun shi su ka koma jazir
a rude Inaya ta koma geffen shi ta na fadin " baby lafiya , me ya faru ? "
a hankali ya bude baki murya a disashe ya ce mata " take me water "

bai gama rufe bakin shi ba ta tashi da gudu ta nufi dining room , ta na isa bakin dining table ta kai hannu ta dauki glass da jug din ruwa , ta zuba ruwan cikin glass sannan ta juya da Sauri ta dawo cikin parlourn

tun kafin ta karaso gare shi ya saki glass din ya fadi kassa , wata razananiyar kara ta saki kafin ta nufe shi da gudu har sai da ta taga glass din ba ta sani ba
da gudu ta Zube saman guyiwowin ta ta talabo kan shi ta na bubuga kumatun shi ta na fadin " baby , baby me ya same ka , ka bude idanun ka don Allah , baby ! " ta kai karshen da karfi

ina ko jin ta ba ya yi idanun shi su na rufe , jikin shi ya yi zafi , sai wata rawa ya ke , ga wata zufa da ta karayo mishi a Fuska kamar an watsa mishi ruwa
ta na a haka kawai ta ga wani fari abu kamar kunfa haka ta na fitowa da ga bakin shi

dan zaro idanu ta yi ta na kallon shi , ba ta san lokacin da idanun ta ke cikowa da ruwa ba ita kawai sai faman jijiga shi ta ke ta na fadin " baby ka tashi don Allah in wassa ka ke min ka daina " ta kai karshen ta na sakin kuka

amma ina ko motsi bai yi ba
a dubu dari ta sake shi , ta mike da gudu ta nufi lift ta shiga ta baro part din
gudu ta ke cikin fitar hayaci ga kafafun ta sai zubar da jini su ke yi amma sam ba ta jin komai , duk wanda ya gan cikin wannan halin kowa sai ya tambayo kan shi me ya sa ta gudu haka , ga shi kuma sai zubar da jini ta ke

a haka ta ke gudu har ta karaso cikin parlourn MALIKAT INAS babu ko sallama
a dubu dari MALIKAT INAS da RIANNA su ka mike su na kallon ta har su na hada baki su na tambayar ta lafiya

bayan haki ba abun da Inaya ke yi dan maganar ta ki fitowa
bin ta da kallo RIANNA ta yi nan ta ga ko shoes babu a kafafun ta ga shi kuma duk jini
a razane ta ce " inallillahi , baby me ya same ki haka ? "

ta na gama fadar haka Inaya ta saki wani kuka mai cin rai hawaye na zubo mata bibiyu ta na nuna musu hanyar fita parlourn ta na fadin " yaya Zayd di na , Aunty RIANNA mu je ki cece shi don Allah "

cikin rudu MALIKAT INAS ta ce mata " baby ki kontar da hankalin ki ki fada mana abun da ke faruwa "

" Ammie , Yaya Zayd ne , ban san abun da ya same shi ba kawai mu na shan fruits na ga ya fara tari , shi ne ya ce min na je na kawo mishi ruwa kafin na dawo na tardo shi konce ba ya motsi wani farin abu na fitowa da ga bakin shi , Ammie don Allah mu je ki duba shi kar wa......... wani Abu ........ " ba ta kai karshen maganar ta ba ta sulale a kassa sumamiya a wajen

sam RIANNA ba ta bi ta kan Inaya ba ta nufi hanyar fita parlourn da gudu ta fice dan ganin dan uwan ta
da sauri MALIKAT INAS ta Zube saman guyiwowin ta ta talabo kan Inaya ta na dan bubuga kumatun ta , ta na kiran sunan ta
amma ko motsi Inaya ba ta yi ba
wani dan karamin tsaki MALIKAT INAS ta ja kamar za ta yi kuka ta ke furta " inallillahi wa'ina illaihi raji'un " har sau uku
ta ma rasa me za yi dan duk ta bi ta rude

ta a haka kawai ta ga wasu nurse guda biyu sun shigo parlourn su na sallama cikin girmamawa su ka gaishe ta sannan su ka nufi Inaya

har sun sa hannu za su daukar ta MALIKAT INAS ta ce musu " wait , ina za ku kai ta wa ya aiko ku ? " ta tambaye su dan ita yanzu ta daina yarda da kowa indai abun da ya shafi familyn ta ne

Cikin girmamawa daya da ga cikin su ta ce " Ranki shi dade Gimbiya RIANNA ce ta aiko mu ta ce mu kai word room "

" shikenan ku dauke ta mu tafi " ta fada ta na kokarin tashi
ba musu nurse din nan su ka sa hannu su ka dauki Inaya su ka nufi hanyar Fita part din da ita MALIKAT INAS na bayan su
su na fitowa ko sai saman Motar ambulance , su ka saka Inaya a ciki

ashe fitar da RIANNA ta yi da waya a hannun ta , tun kafin ta isa part din Malik ta tura Text a aiko mata da ambulance a part din Malik da part din MALIKAT INAS

kai tsaye Word room su ka nufa da Inaya da mugun gudu
ko one minute ba su ba su ka iso , da sauri Nurses din nan su ka fito , su ka fito da Inaya da ga cikin motar saman wani gado su ka nufi word room din da ita
( yanayin word rooms din kamar wata yar karamar likita ya ke har da reception )

su na shigowa da Inaya ko , wasu Nurse su ka shigo Malik konce saman gadon Jinya RIANNA na biye da bayan su

cikin daya da ga cikin word room din nan su ka nufa da Inaya , Malik kuma su ka wuce kai tsaye A&E ROOM da shi

RIANNA da MALIKAT INAS kuma su ka tsaya a reception
a hankali RIANNA ta matso kussan MALIKAT INAS ta na fadin " Ammie wai me ya faru da su ne haka ? "

" ni ma ban sani ba RIANNA , ban sani ba , don Allah kar ki fadawa MALIKAT AL'UMU abun da ya faru har sai mun Doctor sun shawo kan abun da ya same shi "
MALIKAT INAS na gama fadar haka Wata doctor ta fito da ga dakin da a ka kontar da Inaya ta karaso gaban MALIKAT INAS
ta ce " barka da wannan lokacin ran ki shi dade "

da sauri RIANNA ta ce mata " doctor me ya same ta ? "

" ku kontar da hankalin ku , suma ne ta dan yi , jinin ta ne ya dan hau , ga shi kuma ta samu rauni a kafafun ta har ta zubar da jini shi ya sa , amma ba abun da ya same ta " Ta na gama fadar haka ta juya ta bar wajen

a hankali MALIKAT INAS ta sauke wata boyayyar ajiyar zuciya ta na fadin " Allah na roke ka ka sa shi ma sumar ce ya yi ba wani abu ba "

cikin nitsuwa RIANNA ta ce mata " ba na tunanin Suma ce ya yi Ammie "

" why ki ka ce haka ? wai ni INAS , na ma rasa ya zan yi , sun kassa bar min Ahali na lafya , ya Allah me ya sa ka halice ni a cikin gidan sarauta , yanzu ga shi su na neman su raba ni da yaro na saboda wannan banzan Mulkin , ni wlh su je su rike amma su bar min Ahali na " Fadin MALIKAT INAS hawaye na zubo mata

da sauri RIANNA ta rungume ta cikin raunin murya ta ke cewa " ki kontar da hankalin ki Ammie in sha Allah ba abun da zai same shi " ta fada cikin sigar rarrashi

su dai din da ke reception kallon su kawai su ke tun da ba su san abun da ke faruwa ba

▪AFTER SOME MINUTES

sannu sannu sai da su ka share one hour zaune a reception , babu doctor din da ya fito da ga A&E room bare su tambaye shi abun da ya samu Malik

su na a haka kawai su ka ga wasu doctor guda biyu sun fito
da sauri RIANNA ta mike ta nufe su a rude ta ke tambayar su lafiyar Malik
cikin nitsuwa daya da ga cikin su ya ce mata ta yi hakuri su biyu shi office din shi dan ba zai iya yin maganar a tsaye ba , da ga haka ya raba ta geffen ta ya wuce ya nufi office din shi

juyawa RIANNA ta yi ta kali MALIKAT INAS kafin ta fada mata abun da doctor ya ce
ba musu MALIKAT INAS ta tashi ita da RIANNA su ka bi bayan doctor din nan
da sallama a bakin su su ka shigo office din shi , nan su ka tardo shi ya na zaune saman chair din shi , ga kuma gudan doctor tsaye ya na rike da wani file ya na duba

cikin girmamawa Doctor ya ce musu bismillah su shigo
karasowa su ka yi cikin office din , su ka zauna saman chair din da ke fuskantar doctor din sannan RIANNA ta ce mishi " Doctor Mike me ya samu dan uwa na ? "

a hankali doctor ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " ranki shi dade , ba na daya da ga cikin likitocin da ke aiki da bugun zuciyar mutum dan tantance ya na raye ko a mace "
Chapter 13 · 0% Book details