← Book details Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 34

Sashe 29

Exiled Prince Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk Rouksar ta ji gaban ta ya fadi , murya na kerma ta ce mata " me me ki ke magana a kai ? "

" kar ki ce za ki raina min hankali , ki fada min ina ki ka boye shi " Inaya ta fada cike da isa kamar ba ita ba ce wannan uwar shagwabar ba

" kin ga ban san abun da ki ke cewa ba , ki ba ni hanya na wuce "
" shikenan , amma ki sani ba zan kyale ki ba , macijiya kawai " Fadin Inaya ta na murguna mata baki kafin ta raba ta geffenta ta wuce
wata yar karamar ajiyar zuciya Rouksar ta sauke ta na fadin " kai Aymane , ka cuceni wlh , dole na bar masarautar nan cikin daren nan " ta na gama fadar haka ta fara takawa ta bar wajen ita ma

bangaran Inaya kai tsaye cemetery din masarautar ta nufa ,
ko me ta je yi cen ba ta ma tsoron fatalwa ? 🤔🤔

sai da ta karanta addu'a sannan ta shiga cemetery din
ta na shiga idanun ta su ka sauka kan Malik , tsaye bakin wani kabari ya rike hannayan shi a baya
kabarin zagaye ya ke da wasu flowers gwanin burgewa
sai da ta yi tafiya mai dan nisa , dan wajen ba karamin girma gare shi ba
sannan ta karaso geffen shi cikin sanyin murya ta ce " yaya Zayd ! "

a razane ya juya ya na kallon ta , har ga Allah ya ji tsoro , a hankali ya bude baki ya ce " me ki ke yi a nan ? "

wani dan karamin murmushi ta sakin mishi ta na fadin " kai ma me ka ke yi a nan ? "
a hankali ya juya kan shi ya ci gaba da kallon kabarin da ke gaban shi
sai da ya dauki lokaci kafin ya sake ce mata " ya a ka yi ki ka san ina nan ? "
" ummmm , ni ma ban sani ba , jiki na ne ya ba ni ka na nan " ta fada cike da shagwaba

shiru ya yi bai ce mata komai ba
ya na a haka ya jiyo Muryar ta ta na dariya kassa kassa
a hankali ya juyo ya kale ta ya ce " why did you laugh ? "

juyowa ita ma ta yi ta kalle shi ta ce " uncle ya ce ba ka ji dadin rayuwar ka ba da wannan uban miskilancin naka " ta kai karshen ta na sakin wata yar karamar dariya

dan zaro idanu ya yi a rude ya ce mata " ki na da hankali kuwa ? ki na jin abun da ya ke cewa ? "

gyada mishi kai ta yi allamun Eh ba tare da ta ce komai ba
a hankali ya juya ya kalli gaban shi ya na cewa " ya a ka yi ni ba na jin shi ? "
daga mishi kafadun ta yi ta na cewa " ya ce shi ma bai sani ba "

shiru ya yi bai ce mata komai ba ya ga allamun idan ya biye mata sai ya zauce
ya na a haka ya jiyo Muryar ta ta na fadin " baby uncle ya ce , da allamun ka angonce dan ya ga ka kara kyau har da haske ma "

wani dan karamin tsaki Malik ya ja ya na cewa " ka mutu ma ba za ka kyale ni ba ? "
wata yar karamar dariya Inaya ta yi ta na cewa " ya ce kai babyn shi ne ba zai kyale ka ba "

cikin sanyin murya Malik ya ce " ina matukar kewar ka , why za ka tafi ka bar ni ? ba ka san irin halin da na ke ciki ba a yanzu "

wani cool murmushi Inaya ta saki kafin ta kai hannu ta riko nashi hannun ta ce " ni ma ina matukar kewar ka babyna , amma ba yadda zan yi haka kaddarar ka ta zo , ina matukar alfahari da kai , ina alfahari da Malik din da ka zama , ni dama na sani na bar magaji a bayana "

cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " no Abbi , ba na so , ba ka san abun da ke faruwa cikin rayuwata , na kasa samun sukuni tun lokacin da na hau wannan kujerar nan "

" shikenan , ka sauka , ba zan ga laifin ka ba , amma ni ban haifi ragon namiji ba , dole sai ka zama jarumi in ka na son zama kan kujerar nan dan ba a yi ta dan rago ba , ba ka san irin abun da na fuskanta lokacin da na hau kujerar nan ba , ba ka san irin tubbun da a ka sha yi min ba , amma ka je ka tambayi Ammien ka , za ta fada maka yadda a ka raba ta da mahaifar ta sannan a ka kashe mata yaron ta " ta na gama fadar haka ta ja wani dogon nunfashi har da lumshe idanun ta

bayan zaro idanu ba abun da Malik ke yi , hakan na nufin MALIKAT INAS ta taba haihuwar namiji ?

a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya juya ya kalle ta ya ce mata " my Cutie za ki iya komawa cikin masarauta ina zuwa "

shagwabe mishi fuska ta yi ta na cewa " ba za ka jima ba ? "
gyada mata kai ya yi ya na fadin " Eh , ba zan jima ba "
ba ta ce mishi komai ba ta saki hannunshi ta juya da gudu ta bar wajen
da sauri ya ce mata " yi a hankali " ya fada da dan karfi dan kar ta ji ciwo
ba musu ta rage gudun ta
da kallo ya raka ta har sai da ta bar cemetery din sannan shi ma ya juya ya fara takawa cike da nitsuwa ya bar wajen

▪MALIK

bakin shi da Sallama ya shigo parlourn MALIKAT INAS
zaune ta ke saman Sofa ta na rike da kur'ani ta na karantawa cikin nitsuwa
a hankali ta dago kai ta na amsa mishi sallamar
ta na ganin shi ta saki wani kyawatencen murmushi ta na fadin " babyna , na zata ka na cen ka na hutawa , ya a ka yi baby ta baro ka ka fito ? "

bai ce mata komai ba ya karaso gaban ta ya zauna a kassa ya kontar da kanshi saman laps din ta
a hankali ta rufe kur'anin hannunta ta ajiye gefe , sannan ta daura hannun ta saman kanshi ta fara shafawa a hankali ta na fadin " ka daina saka damuwa a ranka babyna , in sha Allah komai zai zo karshe , idan ka na saka damuwa a ranka za ka iya samun matsala ka sani ko ? "

slowly ya bude baki cikin sanyin murya ya ce mata " na sani Ammie in sha Allah zan rage "

wani cool murmushi ta saki ta sunkuyar da kai ta manna mishi kiss a forehead ta na sa mishi Albarka

a hankali ya dago kan shi ya ce " Ammie , please ina son na yi wata tambaya ina fatan hakan ba zai bata miki ba ? "

gyada mishi kai MALIKAT INAS ta yi a hankali ba tare da ta ce komai ba
dan jinkirtawa Malik ya yi kafin ya ce " Ammie , bayan RIANNA kun taba samun wani babyn ? "

cak MALIKAT INAS ta tsaya waje guda , nan take yanayin face din ta ya sauya kamar ta na shirin yin kuka
da sauri Malik ya ce mata " Ammie , bari zancen kawai , ni ma ban san abun da ya sa na yi miki wannan tambayar ba , i'm sorry "

wani cool murmushi MALIKAT INAS ta saki kafin ta ce " NAYEL , sunan shi NAYEL , ku na kama sosai da shi kamar an tsaga kara , har wadanan Hazel eyes din na mahaifin ku , lokacin da ka shigo duniya na yi tunanin kamar Nayel di na ne ya dawo " ta kai karshen hawaye na zubo mata

a hankali Malik ya dago hannu ya goge mata hawayen ta
wani cool murmushi ta saki ba ta ce mishi komai ba
sai da ya goge mata hawayen ta sannan ya ce " fada min , me ya same shi ? "

dan jinkirtawa MALIKAT INAS ta yi kafin ta ce " ni ma ban sani ba , lokacin da na haife shi ba na cikin hayacina saboda tsananin nakudar da na sha , bayan na bude ido na na gan shi konce a gefe na , ya na wuntsila kafafun shi gwanin burgewa , a ranar mahaifin ku ruwa kawai a bai zuba ba a kassa ya sha , ban taba ganin irin farin cikin da ya yi a ranar , musaman ya bude bankin masarautar , duk wata masarauta da ke karkashin Daular Saudiya sai da ya ba da makudan kudade a yi sadaka , a ranar kassa rufe bakin shi ma ya yi ko wane lokaci sai dai ya yi murmushi ko yi wata yar karamar dariya specially idan ya kalle shi konce a gefena , ina shirin gobe zan koma part di na kawai su ka raba ni da shi , mu na konce cikin Room din mu , na fara jiyo kukan shi sama sama a disashe , a hankali na bude idanu , nan na gan shi sai faman kuka ya ke yi da karfi jikin shi cike da sarar maciji sai zubar da jini ya ke , kafin ma na sauko da ga saman gadona , ya koma ga mahallicin shi "

cikin rudu Malik ya katse ta da cewa " ya isa haka Ammie , ya isa " ya fada saboda ya ga ruwan hawayen da ta ke yi

nan take ta saki wani dan karamin kuka ta kassa cewa komai
a hankali ya mike ya zauna geffenta ya rungume ta ya na fadin " ya isa haka Ammie , I'm sorry , ki daina kukan nan please "
Chapter 29 · 0% Book details