← Book details Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 25

Sashe 20

Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Siyayya Sosai Tasleem ta yi na komawa school, tunda yanzu she's current on social networks, hakanan sai 5stars su kira video group call, ta na ganin za ta sauka ta fake da ba network mai karfi a kauyen a haka harsu ka gaji da Kiran video call...

Yau Saturday da yamma ta koma cikin school, Maryam sai farinciki take yi mai bata ta dawo, Farhan ma yau ta dawo, murna sosai su kayi na ganin juna kuma ga Tasleem da iPhone 14 hakan yasa su Farhan kara yarda da cewa ita din mai kudi ce...

Kasancewa gobe Monday duk ya wanci classes nasu da safe ne, a jere suka shiga lecture theatre, sai ka kalle su ka kara tsabar ado da suka caba, bawai a fuska ba A'ah,ajiki tun daga kan shoes and handbags zaka gane cewa they're expensive and Hot..

Bayan lectures suka wuce yin lunch a Cairo,
Tasleem tace exams is fast approaching let's study hard, tunda Saura sati biyu kafin nan mun gama jerking handouts and Pqs..

Tabe baki Fa'eeh tayi tace, Allah ya bada sa'a nide count me out, Saura ma duk su kace baza su iya fitar dare ba sabida karatu,

Ita kam Tasleem tace yau zan fara shiga library in shaa Allah, Allah ya bada sa'a suka yi magana atare... Suhyma tace karki manta da tafiyar ana Hutu da sati biyu zamu wuce..

Tasleem ta yi murmushi da bai kai zuciya ba tace OK,

Bayan sun gama suka koma school,
Kowane su na harkokin gabansa, bayan sallah isha Tasleem tayi ma Farhan sai ta dawo, ta wuce kill inda taga dundaso students, Allah ya so da nosemask ba wadda zai gane ta haka ta shiga ciki, tayi karatu ba ita tabar gun ba sai after 10 nadare...

Ita kadai ta dinga takawa amma sai kuma ga wata tana ta bin ta a baya, Da mamaki ta juyo tace lafiya?

Yarinya tace, sorry I stopped you, daman ina so na gaya miki that you're stained, Idan ba zaki damu ga jacket na ki rufe gun, a dan tsorace Tasleem ta amsa jacket tana godiya duba da cewa faran white jumpsuit ne ajikinta..

Yarinya tace bye..!

Tasleem tace thank you so much, amma a ina zan ganki na baki jacket din?

Murmushi yarinya tayi, tace kibar shi kawai na baki, cike da mamaki Tasleem ta kallonta coz ta san this leather jacket is expensive, Tasleem tace no I insist, your room number..

Murmushi yarinya tayi kafin tace I live off-K, don't worry we'll meet tomorrow I studied here everyday.. Tasleem tace to Allah ya kaimu, yarinya tace bara na rage maki hanya

Tasleem tace nan kusa nake, worry not, exchanging numbers su kayi nan take ta ji karan text ya shigo, dubawa tayi taga 10k airtime, da mamaki take kallon ta kafin ta furta who are you? As if she finding it hard to speak...

Kiki tace Just a Study friend, I hope you'd accept me as friend? Tayi magana ba tare da jiran abinda Tasleem za tace ba tayi wucewar ta, Tasleem tana tsaye agun har kiki ta fito da motar ta, sauke glass tayi kafin tayi mata bye ta wuce.. Da mamaki Tasleem ta issa dakin, bayan ta gyara kanta ta hau kan net, duba kiki tayi a IG, taga irin designers da take sawa kamar irin su Hermes collection, kuma most of her photos a kasar waje ta keyi yinsu, sakin baki Tasleem tayi tana calculating abubuwa da kiki ke posting, ba ta san lokacin da ta saki ihu ba.tayi saurin rufe bakinta kafin tayi following inta on all social media, kiki ko minti biyar Tasleem ba itama tayi following inta..

SOME DAYS LATER
Shakuwa ce Sosai ke tsakanin kiki da Tasleem, coz during the weekends kiki ba ta shigowa school, sai yau Monday, sai gashi ta kira Tasleem da ta fito ga ta a wajen hostel dinsu...

Tasleem dake tare dasu Farhan tace, girls be right back.. Suhyma tace ban gane ba keda yanzu zamu fita Ina zaki? Karde ace da gaske ne maganar da nake ji a school cewa ana ganin ki da class rep hakane?

Tasleem tace ido ba mudu ba amma yasan kima, Suhyma ke ki auna maganar ki man? Nide bara naje tana fadin haka ta fita koh minti ba tayi ba sai ga ta dawo da katon shopping Leather, budewa tayi taga Hermes handbag and shoes da wasu expensive perfumes..

Da mamaki suke kallonta, Fa'eeh tayi breaking silence din da cewa Hermes lunch collection da ake siyayya in Europe and dollars? Please where did you get this from?

Murmushi Tasleem tayi tace, I bought it myself tana fadin haka tace shall will? Tasa kayan cikin locker ta ta Rufe...

SOME DAYS LATER
Akwana atashi yau su Tasleem suka gama exams kuma ayau driver ko wane su yazo ya tafi dasu, acewar su Tasleem ta shigo KD next week sai su wuce Abuja daga nan su wuce, Tasleem ta hadiye wani abu mai daci ,kafin tace toh sai nazo... Kamar karsu rabu haka suka ji..

Itama Tasleem ta kwashe kayan ta kaf, tana jiran isowar kiki, ko minti Ashirin ba ayi ba sai ga kiki(wai waccece wannan kiki ne? 🤔)

Tasleem tayi mamaki yadda Kiki tasan gidan su, tace ya akayi kk san a nan nake?

Kiki tace 🆔card naki ya nuna min, tace karki damu kowa nada wanni rayuwar da yake boyewa nima kaina I came from poor family, da mamaki Tasleem ke kallonta, tace but you don't look poor? Murmushi Kiki tayi tace you don't look either yaushe kk free muyi hangout and get to know each other?

Tasleem tace ko anjima ai, coz a dan zama su da ita tasamu alkhairan sama da Miliyan agun Kiki, kuma gashi Kiki tace itama tallaka ce zata so tasan ya akeyi take spending that much...?

Thanks
MissDmk✍🏻
[25/12/2022, 11:37] MissDmk✍🏻: *🌍D U N I Y A🌍*

BY

MissDmk ✍🏻

Page 22

_ZAN DAKKATAR DA POSTING DUNIYA HARSAI NA KAI PAGE 20 A DAREN AURENA SAI NA CIGABA DA POSTING IN SHAA ALLAH_

Kamar yadda suka yi da Kiki zasu fita yau, Kiki ta zo tun 4pm suka fita, can Joclarif Hotel suka nufa, a garden suka zauna..

Kiki tace lemme start, I'm Chinyeye Ogo, I'm originally from Imo but based at Lagos..first daughter of the family, Ni Christian ce, iyayena talakawa ne, wadda yasa kulum sai mun fita mu nema kafin mu samu mu ci,

A kwana a tashi na zama budurwa wadda haka yasa na fara fuskanta barazana gun maza sabida kyawun halitta na, at my young age I was raped by gang of men, lokacin I was only 15,da mahaifina ya samu labarin nan take ya fadi ya mutu,i was unconscious at the hospital, bama san mahaifina ya mutu ba, lokacin da na farka na tarar da Mamana na kuka don ance idan ba ta kawo kudi za a kore mu daga asibiti..

Gashi bamu da kudin kai report police station, hankali tashe ta fito asibiti tana kuka absentminded itama nan take mota ya kashe ta, a lokaci daya na rasa iyayena, mu uku kawai muka rage, sauran kannen na duk yara ne basu da wayo alokacin.. A wulaqance aka kore ni daga hospital din wai naje na nemo kudin sai a karasa treating na, a wannan halin na fito asibiti ina kuka ina tafiya dakyar, gashi nasan kannen na nacan na fama da kuka...

Nazo wajen asibiti na zauna, a Inda na hadu da wata mata, zan ce kawai Allah ne ya aiko ta gun don ta taimaka min... To cut the story short, ita ta dauki nauyi na harna samu sauki Inda ta dauke ni nida kannen na muka koma gidanta da zama,yaren mu daya kuma adini mu daya.,

A hankali muka fara samu ingantaccen rayuwa agun ta, muka zama abin sha'awa, a lokacin da na kammala secondary ta daura ni akan business inta,wato business dake kawo kudi masu sunan kudi a lokaci daya,

Goge hawaye na nayi Ina kallon ta..

Kina son kisan irin business din?

Na amsa da eh.

Tace I'd show you tonight and trust me you gonna like it,

Jin ance tonight yasa gabanta fadi, tace badai karuwanci bane?

Murmushi Kiki tayi tace No. Ki bari goma yayi zaki ganin ma idonki..

Suna tare har dare, sallah ne ke raba su, Tasleem ta zulla ma Inno karya cewa ta fara rage kaya ne amma bata gama exams ba, wannan ya bata daman kasancewa da Kiki har dare, goma nayi Kiki suka shiga GRA, wanni kafataren Gida..

Yammata ne cike a gidan kamar ana biki, Hajiya na ganin ta, tace Kiki har kin dawo?

Kiki tace eh Hajiya, ina wuni Tasleem itama ta gaida ta kafin suka wuce ciki, suna shiga wani daki ta sauke nosemask, tace naga wacce na sanni acikin yammata... Murmushi kiki tayi tace bara Hajiya tazo, suna cikin haka Hajiya ta shigo

Bayan sun sake gaisawa Hajiya tace, Kiki yarinya ta hadu fa, gashi baza ta wuce 17 ba,

Kiki tace A'ah na kawo ta nan ne don tace tana son ta san irin business da na keyi da yake kawo min kudi ba wai don tayi register ba,

Hajiya tace oh I see.. Kafin tace ya'ta shide wannan business na sirri ne, Idan ka shiga ba fita sannan kuma ba ka ba yin ciki. Freedom daya kk dashi shine Idan kinyi aure ko kinyi migrating to another country..

Sauke ajiyan zuciya Tasleem tayi tana kallon Hajiya,

Hajiya ta kara da cewa we've 3 book list
1, Mummy's and Riches
2, Daddy's and Riches
3, Dance and Riches
And each has it own criteria, for example Idan nace ki zabi guda daya Wanne zaki zaba aciki?

Shuru Tasleem tayi kafin can tace I'd go for no3

Murmushi Kiki tayi tace Wow!

Hajiya tace no3, shine you'd be giving thousands of money to dance for men just to arose there sensational feelings..

Da mamaki Tasleem take kallonta..
Chapter 20 · 0% Book details