← Book details Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 25

Sashe 10

Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tasleem tace Hmmm aye Warr, ba afimu wanka kuma baza afimu gayu ba, don haka banga abinda zaisa ina kula Wacce ba sa'ar yina ba, Zahra Agaida gida koh... Idan sabo ai k'wayensu sun Saba da gani fadar Ummi da Tasleem.. Masu goyan Tasleem sukayi shewa su kace warr..

Ummi tace nide da uba nake ado bada rigan ado ba,kuma nafi karfin nayi takama da kudin saurayi wasu fa? Ba su can ba su can dande kawai they wanto look good like us.. Tasleem za tayi magana Meems tayi saurin rufe mata baki tace K'awa dan mu suka zo fa, Don ALLAH kubar maganar haka, Ummi mungode koh taja Tasleem suka shige ciki...

Bayan sallah magrib Alhajee yazo, dauko abinda ta ajiye mai na sauka tayi, ta nufa inda ya paka motar sa, tsayawa tayi a jikin mota, cikin girmamawa tace ina wuni Alhajee? Alhamdulillah Gimbiya, ya taro ya tashi? ALLAH ya sa anyi na tsoran ALLAH. Ta amsa da Amin,yace ki shigo man? Tace A'ah Alhaj sauri nake yi,

Haba Tasleem kinsa daga idan nake ne? I came all the way from kaduna just to see you, ba dan ta so ba ta shiga motar...

Tasleem kenan Yar shagwaba,idan kina wanna shagwaba sai inji kamar..Tayi saurin Juyowa tace kamar kayi mai? Murmushi yayi kafin yace saina ji kamar na baki dukan kaina, Tasleem tunda nake ban taba ji na so abu lokaci daya ba kamar yadda nayi miki.. Cike da mamaki take kallon sa kafin ta kawar da idonta daga gareshi, ya kara da cewa kin koh san cewa ke kalla matar Manya ne? Girgiza kai tayi alamar A'ah.. Lumshe ido yayi kafin yace ke matar Manya ce Tasleem, yaro baze iya rike ki ba sa bida ke din Yar Baiwa ce..

Murmushi da be kai ciki ba tayi tace, kakata na jira na ya kamata Na koma gida, yayi saurin ruko mata hanu yana caressing, tace kace ba zaka sake taba jikina ba ya haka kuma? Murmushi yayi yace coz I've a surprise for you, nan take ya fito da Pearl of bracelets and necklaces ya mika mata. Kin amsa tayi tace bazan iya amsa ba za ayimin duka a gida tayi magana cike da yaranta.. Ki amsa ko nayi kissing inki..

Ware Manya idanuwa tayi wanda suke fari dasu Kal kamar ruwan madara, tace mene? Za kayi mai?

Dariya yayi Sosai kafin yace ki amsa to, koh nayi? Tace bazan amsa ba Idan ka kuskura kayi abinda kace,za kayi mamakina... Gani how serious she looks yace I was only pulling your legs, ki amsa Kinji Baby na... Amsa tayi rai bace tace Nagode,tace Gashi can na ajiye ma a back seat... Ta kosa taje gida ta sake tunkara Inno da maganar..

Mintin goma yakai ta gida, zama tayi a tsakar gida ta saki wannin kuka da iya karfinta, Inno dake tahiyar karshe tuni ta salamai tazo a guje tana tambayar ta koh lafiya? Kin cewa komai Tasleem tayi ta cigaba da kukanta harda shureshure takeyi kamar wacce ta hau bori,

zama Inno tayi kusa da ita ta fashe da kuka tace daga walimar sauka sai ku shiga jikinta? Gaskiya ba kuyi min adalci ba Don ALLAH ku fice daga jikinta.. Shuru Tasleem tayi tana sauraron abinda Inno ke cewa,

Tasleem tace nifa ba Aljanu ne dani ba Ina son sanin Usilin na ayau, Dakatawa da kukan Inno tayi tace mene kk ce Talatuwa? Tasleem tace Inason sanin su waye iya...
09074267236
Thanks
MissDmk✍🏻
[11/27, 19:00] MissDmk✍🏻: *🌍D U N I Y A🌍*

BY

MissDmk ✍🏻

Page 11

Bata karasa ba taji saukar Mari a fuskarta, sakin wanni wawan kara Tasleem tayi tana birgima a kasa, Inno tace ba kuka koh mutuwa za kiyi saide ki mutu walhy na sake jin kin bude baki ki yimin wannan tambaya sai na kusa sumar dake,

Tasleem tace Walhi saide ki kashe ni ama yau bazan yi shuru ba harsai kin gayamin suwaye ne iyayena da dangi na.. Dauko muchiya Inno tayi tuni Tasleem ta mike aguje ta shige daki,

Ta turo kofar tana kuka tace, kulum ni shikenan sai ata kirana da Shegiya, wasu ma cewa su keyi a yawon karuwanci kk samo ni.. Jin ta fadi haka yasa Inno fashewa da kuka mai cin zuciya, tace amana aka barmin ke Talatuwa kuma nayi alkwarin rike ki da amana ba tare da kinsa Usilin ki ba.duk wanna maganar da Inno keyi da Zuciyarta ta keyi kafin tace Talatuwa ta to bude kofar na gaya miki Usilin ki..

Tasleem tace Walhi wayo za kiyi min kamar yadda kk Saba, don haka bazan bude ba.. Inno tace sunan mahaifiyar ki "Jamila Bulama"

Jiki a sanyeye Tasleem ta bude kofar tana hawaye kafin ta rugume Inno tana kara fashewa da kuka mai tsuma zuciya, Inno ta riko mata hanun suka zauna, tace sunan mahaifinki Muhammad Shittu kuma ta hanyar aure aka same ki Talatu saide bazan iya cewa komai ba harsai...

Harsai mai Inno? Tasleem tayi magana tana kallon expression Inno, Har Lokacin da ya dace ki sani,Inno tayi magana tana fashewa da kuka mai cin rai, tace Don ALLAH Talatuwa kiyi min alkwarin ba zaki sake bijiro da wannan maganar ba, Idan Lokacin da ya dace ki sani zan sanar dake komai Kinji,

Tasleem taji dadi Sosai jin ance ta hanyar aure aka same ta,cike da tausayawa Tasleem tace to shikenan Inno ba zan sake ba aman ya ainihin Sunana yake?

Nide walhy ban sani ba, ranan talata aka hyfo ki shiyasa kk ci suna rana hyhuwar ki, Don ALLAH Talatuwa ki bar wannan maganar Inno tayi magana tana sake fashewa da kuka da har ba ajin maganan da take yi, numfashi ta ya fara yin sama kamar zata sume, aguje Tasleem taje ta dibo ruwa ta kawo mata ta sha,a hankalin numfashi ya dawo daide

Tasleem tace Inno ki gaffirce ni Kinji daga yau ba zan sake kawo wannan maganar ba,

Inno tace ba komai Talatuwa ta kiyi hakuri karki bar wannan ya zama damuwa agareki Kinji ko? Ban damu da maganar mutane ba,indai zan ganki atare dani, ni burina shine nagan kinyi karatu mai zurfi kin zama mai dogaro dakai.. ALLAH yayi miki albarka Talatuwa ta.. Amin Inno kiyi hakuri kin sa min suna, na canza izuwa wanda na keso Tasleem tayi magana tana goge hawaye dasu kasa tsayawa..

Ba komai yar'nan ai suna mai kyau ce, Lokacinda kk aji hudu a firamari ticha ku yazo har gida ya same ni yace kince masu sunanki Tasleem ba Talatu ba.. Nayi dariya kawai nace masa Eh.

Kwanciya Tasleem tayi a cinyar Inno with alot running through her mind, ta kasa barci sam ta rasa ina zata sa kanta taji dadi karshe de daukar buta tayi ta fita tayo alwala ta shimfida sallaya ta gabatar da nafillah ta dade tana adu'a, dakyar ta samu ta kwanta kusa da Inno dake faman buga munshari....

Washe Gari da safe
Hiran da Inno keyi da Mai waina ya tashe ta, Inno tace in bada Suwaiba Dodi Minal Dodi ce ya za'ayi ace an koya miki yanda za kiyi ragadada aman ki kasa, diba ki gani yar baiwa tawa, kana sha ruwan na biyo ma hanu gashi ba dadi gaba bana baya..

Mai waina tace Kede bari Yar Baiwa tawa, ai Nura na fama da kazanta aini tuni na fita harkan su, wannan ma amsa nayi dan ya dage akan sai na amsa...

Tasleem tace ALLAH yayi gari ya waye anfara gulman kenan,Habi tace Shegiya mai duwaiwe a sama kin saki nonunka fatai kamar kawuna mutane, ALLAH yar Baiwa tawa kiyi mata aure ki huta waze ga wanna yarinya yace tsaran auta ta ce? murmushi Inno tayi kawai..

Ba Habi,kalla ki gani girgiza tayi kafin tace kin gani kin gani kwalalen ki, Inno ta watso mata wani mugun kalo kafin tace gaisuwar kenan?

Sunkuyar dakai Tasleem tayi kafin ta durkusa har kasa ta gaishe su, toh bazan amsa ba fisarariyar yarinya jeki kiyi ta fama da ruguza ruguza abinki, gwalo Tasleem tayi kafin ta mike ta nufa bayi, rage muryar Habi tayi,tace ALLAH yar baiwa ki aurar da ita, ki san ba wayo ne da ita ba karsu ganta da garin jiki ayi mata wayo... Murmushi Inno tayi tace muna adu'a kuma ina ja mata kune, in shaa ALLAH za ta kare karatun ta lafiya..

Amin to Yar baiwa bara na koma na tsabtace gidan kafin bakin kunya su zo nashiga uku..

Inno tace keko ALLAH ya hadaki da Dodi Minal Dodi, ALLAH ya kawo miki mafita ai kazanta beyi ba,ke ni ko ruwan leda ta bani ALLAH ba zan Sha balle naci wannan ka zami ragadada inje kawai na barke da zawo...Habi tace Kede bari ai Nura na daukar hakkina. Sai anjima na leko, Inno tace to..

Tasleem ta fito wanka kenan wani yaro ya shigo yace Ance ana salama da Talatu inji wani a mota, ware ido Tasleem tayi tace bade Alhajee bane ya binciko gidanmu...?

Har sun koma UK abinsu, suna ta shirye shirye yadda zasu dawo Nigeria Shikam Ali kokari ya keyi yaga ya fara planning Nigerian Arewa Restaurant, Aman Abby yaki bashi goyan baya wai baze taba barin ilimin sa yayi wasting a gidan abinci don haka suna gama abinda ya kawo su zasu koma gida..

Wannan dalilin yasa Ali shiga cikin wanni hali, 2 4 7 he's indoor har yakai da baya fitowa yaci abinci dasu.. He doesn't know why all upon people his father choose to be like this? Is it a crime for architect to run a restaurant or is it a must to work at the company? Yana cikin haka yaji cikin sa ya fara murda masa, da kyar ya samu ya mike ya nufa inda flask yake ya zuba coffee don yasha Aman ina ya kasa sha sabida azaba da yake ji, kafin kace mai har ya fara yunkuri amai da dan karfin dake jikin sa ya shige toilet sai Amai yafi minti biyar kafin amai ya tsaigata, ya wanke face insa ya fito rike da cikin sa daide Lokacin da Ammyn sa ta shigo rike da lunch ta same sa cikin wannan yanayi idonsa a kafe kamar wanda yake shirin sumewa a razane ta saki tray dake hanunta tayo kansa tana salati,
Chapter 10 · 0% Book details