← Book details Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 25

Sashe 18

Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manager wannan wana irin jaraba ne? Daga gani mace ka fado jikinta? Sannan kuma ka dinga ikirarin cewa kai na Allah ne? Har kana Aibata wasu da kiransu yan iska?bacin shine dan iska
Gaskiya ba zan taba tolerating ba, tayi magana rai bace ta zo zata wuce, Manager ya dakatar da ita yace siyayyar fa? A hassale tace na fasa tana fadin haka ta bar gun,

Wani Alhajee yabi bayanta yana bata hakuri sai kace shi yayi mata lefin. Ganin yadda ya dage yana binta tace na hakura Alhaji nagode..

Alhaji yace to mu koma ciki ki gama siyayyar..

Tasleem tace gaskiya ba zan iya komawa ciki ba sabida ai abin da ciwo, ba dama mace ta fita on her own sai adinga harassing inta?

Alhaji yace kiyi hakuri nasan anyi maki ba daide ba amma ni nace muje zan biya, jin yace zai biya taji wani dadi a kasan makoshin ta, tace Alhajee bawai ban da kudin biya bane raina ne ya bace, Alhajee yace to ki jirani yana fadin haka ya koma ciki ko 5mins beyi ba sai ga shi rike da laidoji yace to gashi nan..

Kin amsa tayi tace ka barshi kawai, Alhaji ya cigaba da insisting da kyar ta yarda ta amsa tayi masa godiya, yace Idan ba zaki damu ba zan iya rage miki hanya?

Jimm tayi na dan wani lokaci tana kare masa kallo kamar tana kokarin gano wani abu, murmushi yayi yace A'ah ni ba barawo bane balle na sace ki, ya'ta Zanje nayi surprising a school sunyi hutu shine nace bara na tsaya nayi mata siyayya, ke ina kk yi? Tasleem tace Samaru, yace nima Samaru na nufa yace muje, bin bayansa tayi suka shige motar, ya ja motar ya bar gun, yace my daughter what you did there was absolutely amazing Inason mata irinki, how I wish Farhan could do something like you did dana nafi kowa jin dadi,

Da mamaki take kallon sa jin ya ambaci sunan Farhan, ya kara dacewa most young men of now a days are philanders, especially da su ga young and beautiful... Murmushi tayi wanda bai kai ciki ba....

What's your name? Shuru tayi tana tunani amsar da ya dace ta bashi can dai tace Tasleem Muhammad Shittu, yace wanne Muhammad Shittu bade Air Force brigadier Chief commander ba? Tayi saurin nodding head da A'ah bashi ba.. Yace ok ni Sunana Lut I.A yana fadin haka taji gabanta ya fadi, yace ga card nan you can call me anytime coz zanso na hadaki kawance da ya'ta, daga gani ki daga gidan mutunci kk fito ga tarbiyya da sanin ya kamata, wanne school kk?

Tasleem tace ehm ehm ABU,

Yace Masha Allah, watakila ma kun san juna da ita bara na nuna miki pix inta...

Tasleem tace ni new student ce ban Fara sanin mutane ba tayi magana tayi saurin cewa nan zan sauka..

Yace I thought school zaki? Tace A'ah Nanny ba lafiya ne naje Almadina siyan Magani shine na biya Mall yanzu haka can haka na nufa,

Yace Ayyah Allah ya bata lafiya, parking yayi, ya sauko ya bude gidan baya, ya bata kayan nata sannan ya mika mata kudi, kin amsa tayi tace tagode ta bar gun ta tsayar da dan achaba, ta haye da sauri ta koma gida, Allah yaso ba wuta ta shige da kayan daki ta boye...

Ali Cuba da tunda ta mare shi yayi mutuwar tsaye bai ce komai ba harta gama zaginsa, kallonsa kadai zaka yi ka gane irin yadda ransa ya matukar bacewa.

Gwiwa a sache suka bar Mall din, ko driving ya kasa yi, Hydar ne ya tuka shi maganar da tayi sai dawo mai ya keyi, mai fuska biyu gashi shiga ta kamala amma kuma Dan iska, shi marin bai dame shi ba kamar zaginsa da tayi kuma ya kasa yin komai..

Hydar yace she's my student don't worry I'll teach her a lesson, jikinta sai ya zama price for what she did, da sauri Ali ya juyo yana kallon sa yace mai kk nufi da haka Hydar?

Hydar yace bazan Bari tayi graduating ba yadda zan nuna mata karfin ikoh na, she'll reap what she sow, har kai zata kalla ta gaya ma maganar banza?

Sauke ajiyan zuciya Ali yayi yace, ban so kayi mata komai ka kyaleta dani I know how to get back at her, ni tayi ma lefin,na san abin da ya dace nayi mata so karka damu abokina.. Hydar yace if you said so Cuba..

Ali yace ni abin da tayi min bai damaini akan tashin hankali da nake ciki Hydar,

Hydar yace tashin hankali kuma?

Ali yace Eh Hydar, dama nazo ku nema min mafita, aurena watan gobe and haryanzu ban samu solution ba...

Solution kuma? Solution din mai Ali Cuba?

Kallonsa ya tsaya yi, can yace bar magana Hydar..

Hydar yace don't you trust me Ali? Don't forget that problem share is half solved, feel free to talk to me Cuba, I might be able to help, karka ga I'm flirting with girls ka dauka ban da hankali I know what I'm doing Cuba..

Sauke ajiyan zuciya Ali yayi yace to Idan mun issa Emerald zamu yi magana but sai nayi swimming har abubuwa kaina sun ragu..

Hydar yace OK muje ba matsala..
Suna tare a Emerald Hotel har bayan isha, da kyar Ali ya iya gathering courage ya kalle su yace shawara nake nema guys, pertaining my health

Health ?Zayd yayi magana yana jiran Karin bayani..

Ali yace Yes health..! I've a very low spe.. Bai karasa ba yayi shuru yana kallon expression insu...

Zayd yace dama rashin lafiya ka as d'a namiji muke maka kallon Misogynist?

Ali yace yes. I don't have that feelings of wanting girls...

Mikewa tsaye Hydar yayi yace shittt and you are telling us now? Gaskiya ba kayi wa kanka adalci ba, to zama mai mu keyi? Let's go see a doctor..

Ali yace I've one, kuma ban so kowa yasan Matsalata shiyasa bana zuwa nema magani, ba wadda ya san da sirrina face ku biyu nan sai Dr Kelvin so I believe my secret is safe with you guys?

Suka amsa da yes, but Yanzu mai solution shin zaka yi auren a haka ne ko ko sai ka samu sauki? Zayd yayi tambaya yana kallon Ali..

Ali yace solution dina shine samu body match na, Idan na samu mace da jikina yayi na'am da ita to I can be a man for 20mins saide I don't think Khadijat is my body match..

If I get you right kana numfi Idan ka samu mace da ta dace zaka iya mata ciki?

Daure fuska Ali yayi kafin yace something of that..

Zayd yace zama mai mu keyi ? Bara mu nemo mata afara gwajin..

Hydar yace Idan angwada ya samu shin kana tunanin za abarshi ya aureta ne? bayan ga wacce aka zabar masa? nide ina da shawara tunda yace Idan ya samu body match insa he can last for 20mins to shawarar nan shine, ranan daze angwace ranan zan samo solution to his problem zai je ga Khadijat as a man yadda reni baze shiga tsakanin su ba...

How are you going to do that Hydar? Ali yayi magana yana nema karin bayani?

Murmushi irin na yan duniya Hydar yayi yace Allah ya kaimu A Daren Auren(sunan wani Hausa book wai A Daren Aurena) ranan ko zaka agwance abokina....

Thanks
MissDmk✍🏻
09074267236
[20/12/2022, 17:13] MissDmk✍🏻: *🌍D U N I Y A🌍*

BY

MissDmk ✍🏻

Page 20

Zaune take dakin Meems, tace walh kuwa K'awa a sa'a na fita jiya, daman tun da ya wulaqanta ni nake nema Allah ya kara hadani dashi na koya mai hankali sai ga shi ya zo hannu na cikin ruwan sanyi, shewa suka yi suka kashe tafi

Meems tace kk mare shi kuma ya kasa yin kome?

To kin dauka ni na wasa ne? fado min a jiki yayi kuma ya damke min waist fa? Kema kinsa bana yarda da wannan iskanci K'awa.

Amman cemin kk yi bugewa yayi shi yasa ya fado jikin ki K'awa, Meems tayi magana tana murmursawa..

To sai akace ya damke ni don ya fadi? Ke nifa ban yarda dashi ba, daga gani sa Shima dan iskane amma yai ta nuna ma duniya shi na Allah ne kuma bai kallon mata Mtchews K'awa mubar maganar sa Don Allah,

Meems tace amma Abban Farhan bai san da tafiyar ku zuwa Dubai ba?

Oho masu K'awa nide burina shine Kawai kafin adawo ace Ina da 3mil a kasa, mikewa tsaye Meems tayi,tace Ka'wa Miliyan uku? Sata zakiyi koko fashi?

Murmushi Tasleem tayi tace election is around the corner kuma nasan duk spots da yan siyasa ke zama a wannan gari, yau in shaa Allah suya spot na nufa ba boka ba malam in just 2months zan tara kudin...

A'ah K'awa ban baki shawara bin yan siyasa ba, suna tafiya da asiri zasu iya kwashe albarkan ki, don Allah ki canza shawara, Tasleem za tayi magana wayar ta ya fara ringing dubawa tayi taga unknown number, picking tayi da salama, jin voice din Alhajee mai kudi tace saukar yaushe?

Alhaji dake dayan bangare yace yau, please kizo ina meeting point in mu, I've a surprise for you...

OK, gani nan zuwa tana fadin haka ta yanke Kiran gyara jikinta tayi ko minti biyar ba tayi ba tayi ma Meems sallama, karasawa tayi gun da yayi parking, bude mata yayi ta shige..

Cikin kunya da ladabi ta gaida shi, amsawa yayi da i missed you baby.. Rufe fuskar tayi da tafin hannunta alamar kunya.. Mika mata Leda yayi yace ga tsaraban ki..

Amsa tayi tace nagode,

Mention not baby, amma ki bude ki ga abinda yake ciki, amsawa tayi da toh kafin ta bude taci Karo da box din iPhone 14, ware Manya idanuwa ta waje tayi tace are you for real?

Murmushi Alhajee yayi yace just a little gift you know?

Ji tayi kamar ta rugume shi tsabar farinciki amman ta kasa, sai godiya ta baki...

To bara na koma hotel na dan huta anjima zan dawo yayi magana yana kare mata kallo, kin kusa zuwa hannun yarinya yayi maganar cikin zuciyarsa a bayane kuma yace Idan nazo anjima zaki rakani cin abinci?
Chapter 18 · 0% Book details