← Book details Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 25

Sashe 12

Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shikam sai janta da hira ya keyi, kince ainihin sunan ki Tasleem right? Nodding head tayi alamar Eh, taga an wuce Shika Teaching Hospital, tace Alhajee baka ce Area G zamu ba? Murmushi yayi yace gidan gona zamu, a tsorace tace gidan gona kuma Alhajee? Nide tsoro nike ji don ALLAH ka mayar dani gida.. Gida kuma Tasleem? Haba mana ke kuwa mintin nawa ne har kin gama awaran? Hawaye ne suka fara sauka daga idonta tace Don ALLAH ka sauke ni, na koma gida tayi magana tana fashewa da matsanaci kuka, can yayi parking yana kallon yanda take kuka yace haba Tasleem ba fa sace ki zanyi ba, Dayen waran na fridge fitowa za kiyi dashi ki soya mana sai gizzard source, cikin shagwaba tace cemin kayi gidanka, nasan Area akwai mutane aman gidan gona ba kowa, kalla ka gani mu kade ne anan please ka mai dani gida,

Dakka mata Uban tsawa yayi yace ke ban son shanshanci man, ko dan kinga ina lalabaki? Ke bara kiji zuwa kamar Kinje azuciye ya fizge motar.. Kuka ta keyi da gaskiyar ta har suka issa farmhouse insa, mai gadi ya bude masa kofar suka shiga ciki, cikin lalashi yace Tasleem I'm not going to hurt you, ki fito man kina gamawa zan mayar dake, Alhaji kayi alkwarin zaka mayar dani gida? Murmushi yayi yace Eh, goge hawayen tayi ta sauko, itadai bata ga alamar akwai kitchen balle kuma wanja dahuwa, daki daya kacal ta hango yace mata muje man, cike da tsoro take kallonsa tace ina zamu? Yace ga kitchen din nan ai yayi pointing dakin, cike da tsoro take takawa harta kai daide dakin aman saita tsaya cak tana raraba ido kamar beran da ya fada Randa,

Don ALLAH Alhaji ka mayar dani gida nasan Inno na can tana jirana tayi magana tana kokarin goge hawaye da su kasa tsayawa..

Wanni shu'imin murmushi Alhajee yayi kafin yace ya naga duk a tsorace kk? Haba tala I mean Tasleem yayi magana yana kokarin kai mata hanu fuska tayi ma za ta matsa, ki shiga man time is going, a hankali ta fara takawa za ta shige daki sai kawai....

Thanks
MissDmk✍🏻
09074267236
[11/30, 19:52] MissDmk✍🏻: *🌍D U N I Y A🌍*

BY

MissDmk ✍🏻

Page 13

kawai su ka ji hayaniya mutane waigawa yayi ya ga yan daba sunyo kansa, ai baisan sanda ya zube a kasa ba..

Roja yace dan mai kaza kaza kanwar tawa ka dauko zaka lalata? Alhaji cikin rawar voice yace A'ah awara zata dafa min, Roja ya maka mai gora yace uwar warace kaji koh, ku koya mai hankali ke kuma taho nan za kiyi bayani, cikin tsoro tace yaya shi yace na bisa nan idan na dafa mai wara zai bani dubu hamsi,

Roja yace Wattt? Wato wayo zaka yi mata koh? Toh Dan kaza kaza ina kudin da kace zaka bata? Alhajee da yaci duka yasa ya fito da wallet jiki na rawa ya Mika masa ya kwashe kudin, daya daga cikin yaran yace Roja wannan ba kansila bane? karkata Kai Roja yayi yana kallon sa, yace Bafson shine fa, Ashe kai karamin kwaro ne to tsaya kaji ko chiyaman garinku bai issa yace zai batamin Kanwa na barshi ba, balle kai kana jina koh? A kame dai bazan kamu ba nafi karfin hukuma yana fadin haka yace ka kuskura na sake ganin ka da K'anwa ta sai nayi ma kachiya yana fadin haka ya tallabo keyan Tasleem suka wuce, Napep da suka zo dashi su ka shiga, saida su ka kai daide ganga uku su kayi parking,

Tasleem tace aiki yayi kyau masoyi, dauka kason Ka ka bani nawa, Roja yace A'ah tawa, dauki iya abinda zaki dauka ai baki da case, amsa kudin Tasleem tayi taga 40k ne, 20k ta dauka ta basu Saura, godiya su kayi, tace Roja Saura dayan amma shifa yafi wannan kudi da gogewa Idan na kasa dashi saina hada daku..

Ba Case Talatu, ai indai kece ko ba kudi za muyi aiki tare.. Murmushi tayi tace godiya nikeyi Roja, kafin ta sauka ta tsayar da napep, direct gida ta nufa inda ta tarar da dasu Inno da mai waina sunyi ciko ciko dasu,

Sallama tayi kafin ta gaishe su sai kawai Inno ta fashe da kuka tace Talatuwa kinga dan Adam koh? Tasleem tace mai ya faru ne Inno? Inno tace Yar Baiwata ce mai gidan ya Kore su daga gidan wai students zai saka acikin gidan,mai waina tayi carab tace cewa fa yayi mun ishe gidan sa da kazanta don haka mukwashe Kayan mu, mubar masa gida shine Yar baiwa tawa ta bamu masauki anan..

Tabe baki Tasleem tayi tace Cabdi to ku mai ya kaiku yin kazanta agidan haya? Kaniyarki ce ta sani nace Kaniyarki ta Sani, Kyalkyalce da dariya Tasleem tayi tace gata nan ai kunfi kusa tana fadin haka ta shige dakinta..

Can ta Kira Meems a waya bugu daya meems ta amsa, Tasleem tace K'awa har nayi screening anyi uploading na nayi making payments na cire admission letter harnayi clicking hostel Mam Nazeef ya bani full assurance zan samu, Meems tace K'awa na ta yaki murnan Sosai kam, Tasleem tace Nagode K'awa gobe zaki rakani kasuwan sabo sabida next week Inaji zan fara zuwa school.. Meems tace toh ALLAH ya kaimu kafin sukayi salama..

Washe Gari dasafe,Tasleem ta fito da wani shegen rigan barci da ake hango komai na jikin ta, shaf ta mance da yanzu basu kadai bane a gidan ta fito kenan taci karo dasu Inno a tsakar gida tare da Nura, Maimakon ta koma kawai sai ta dauki buta, wanni Uban salati Inno ta dakka tace oh oh jama'a na bi ina na ga haske? Talatuwa mai kk shirin zama ne? Tasleem bubuga kafa tayi ta zumburo baki tace toh Mai nayi? Inno tace uwarki kk yi in banda rashin hankali Tasleem kya fito haka tsirara?

Kallon kanta Tasleem tayi kafin ta mayar da dubanta izuwa su ganin tayi ya Nura ya saki baki sai kallonta ya keyi, tace lafiya ka saki baki kana kallona? Saurin kawar da idonsa yayi, Mai waina tace Kee bama son shanshanci kin fito waje da luka lukan abu saikace kawuna mutane ana magana kina fisara wato ke wiyan ki ya issa yanka koh? Inno dauko ice tayi ta nufe Tasleem da gudu Tasleem ta shige daki tana kurma Uban ihu,

Habi ta amshe icen daga gun Inno tace, ki barta kawai karkiyi mata lahani, Baiwa tawa ALLAH ki barni na koya mata Hankali man, ace mutum ya girma baisan ya girma ba? Koh Asiya da bata kai Mace ba zata fito haka ba bale wannan da take da cikan halitta, maza dauki hijab Karna sake na ga kin fito ba Hijab, kunkune Tasleem ta dingayi tana kuka ai daga sati mai zuwa saide ki nime ni don bazan zauna daku ba.. Dan ubanki kunkune mai kk wa mutane Inno tayi magana tana kai mata duka.. Kara fashewa da kuka Tasleem tayi ta fito aguje ta nufa bayi, Asiya sai dariya ta keyi Tasleem takai mata uban duka da yasa ta fadi warwas a kasa tayi maza ta shige bayi, Shikam Nura yaga abinda yafi karfin sa..

Sai wanja 10am ta gama shiryawa batayi karin kumalo ba tace ma Inno ta wuce tayi maganar cikin fushi, Inno tace haba Talatuwa ba ki huce ba? Nafa baki hakuri kuma bazan sake dukan ki ba ama kema karki sake Kinji ko? Nodding head alamar to kafin tace sai yamma zan dawo, Inno tace to Talatuwa ta ALLAH ya bada sa'a

Direct gidan su Meems ta nufa, Alhj mai kudi duk ya adabe ta da kira amma taki dauka, kawai haushi yake bata, saida ta jira Meems ta gama shiryawa kafin suka fito suna labari suna dariya, har suka kai bakin titi inda motar ya paka a gaban su, Dan matsawa su kayi daga gun motar Alhj Mai kudi ya fito da sauri yana kiran sunan ta, yace haba Tasleem Lefi mai nayi ake azabtar dani haka? Batace masa kome ba taja hanu Meems zasu tsallake titi yayi saurin dakatar dasu, Meems tace ina kwana? Amsawa yayi da murmushi a fuskar sa yace lefin mai nayi Tasleem?

Tasleem tace nace ka daina rike min hanun Aman ka ki.. Cikin jin kunya yace am sorry Gimbiya a yafe ni, yanzu ina kk yi? Meems tace Sabo kasan K'awa ta samu admission, Masha ALLAH Tasleem to idan ba zaku damu ba sai na kaiku.. Murmushi Meems tace to kafin su ka shiga gidan baya, abokin Alhajee ya hango Meems shi dama kalan mace da yake so kenan, Fara yar siririwa da fillanci ya gaishe su, Meems kadai ta amsa, abokin ke Jan motar har suka isa sabo, first shagon da suka fara shiga shine, Abayas And Bags.. Wanni milk color abaya Tasleem ta taba tace wannan fa? Mai shagon yace size 65 sannan kudinsa 20k, zaro da manya idanuwa ta waje tayi tace what? Wannan yafi karfina matosawa Alhaj yayi yace yayi miki? Cikin jin kunya tace eh, Alhaj yace dauko mata, kafin yace sai me? Tasleem ta tabo wani Dior bag tace nawa wanna? kudinsa 30k...haba mana Malam?Alhaj yace sa mata su, making payments yayi kafin sukar ba shagon yace sai ina? Wanni boutique da ake siyar da English wears ta nufa, jeans biyu da sneakers biyu ta dauka, taje gun masu dinka hijabai ta dinka kalla kusan 12,siyayyar da sukayi yakai almost 150k kuma ba ko sisin ta aciki, itama Meems ta samu rabonta, Alhajee yace ya kamata muyi lunch koh? Tasleem tace A'ah kawai mu tafi gida..

Abokinsa yace nikam yunwa nake ji ya kamata naci wanni abu yana fadin haka ya nufa "Cairo" gidan cin abinci tun shigar su take jin Kamshi balango Rago, Alhaj yace ku sauko man? Nodding head sukayi alamar A'ah, da kyar dai suka sauka daga motar sabida magiyan dasu Alhajee su keyi, suna fitowa taci Karo da....

Thanks
MissDmk✍🏻
09074267236
[12/1, 19:51] MissDmk✍🏻: *🌍D U N I Y A🌍*

BY

MissDmk ✍🏻

Page 14

Suna fitowa suka ci Karo da Yasir da matar sa,gaisawa cikin mutunci su kayi da Alhji,Yasir ya mayar da duban sa gun Tasleem yana aika mata da mugun kallo..
Chapter 12 · 0% Book details