← Book details Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 25

Sashe 15

Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tasleem tace Which of the novel and why did you bring this up?

You remember my crush in the novel Hazrat Mohell right ?

"Yes we all do so is there any connection between the Hazrat Mohell and this lecturer? Coz Farhan we're not understanding you anymore...

Farhan za tayi magana kenan wata tsohuwar mata dake goye da yaro a baya ta zo gun daga ganin kasan irin masu aikatau nan ne..

"Laaa wanga ba Talatu bace yar gidan Inno Mai Kose ta fadi magana tana wangale baki hade da rike haɓa..

"Talatu Talatu!! dake nake magana kika dauke Kai oh Wato sabida ki zauna da yan gayu shine zaki Yi kamar baki sanni ba ah bashaka Talatu.."

Wata elegant woman ne tazo gun da tsohuwar mata take, tace Mai Waina kinsa su ne?

Eh Hajiya na san Talatu yar wajan aminiyata ce Inno wacca na baki labarin itama tace a nema mata aikin Aikatau sabida Yanzu bata wani samu ciniki kosan
Ita kuma Talatu nan da kk gani awara take siyarwa a kofar gida amma kin ganta zaune cikin Mayan mata tana mirsisi da ido kamar a murje gyada..

"Tasleem I think this woman seems to know you look how she's pointing fingers at you Fa'eeh ta fadi magana disgustingly..

Me this woman? Oh come on girls I've never met this woman in my whole life maybe I looked like someone she knows Tasleem ta fada tana watsa ma mata mugun kallo..

Rayhana tace Kai Tasleem naga fa yadda ta dage akan ta sanki maybe..

Tasleem tayi saurin katse ta dacewa maybe irin almajiran nan ne da suke zama bakin Main gate kinsa suna dayawa bazan iya gane wacece daga cikin su...?

Haba Tasleem tare take da Hajiyan nan I don't think this woman is a beggar Farhan ta fada in a fed up way..

Toh Talatu tace ba Tasleem ba don ALLAH banso ciwon kai tsohuwar tace Yanzu Talatu ni kk zaga? Ah bashaka an shigo ya'ya masu kudi dole a wulaqanta ni... Hajiya tace Mai waina wata kila Kama sukeyi..

Kwarankwasa Hajiya koh kaffara bazanyi ba wannan Talatu ce...

Fa'eeh ta kalle Tasleem da tamke fuska tace but this is not the first time da muke jin ana Kiran ki da Talatu Mai awara

Ban gane ba Faee? Kuna numfi kun yarda da abinda suke fadi?
Wai na tambaye ku man, banan bane wata taga Rayhan tace Tana Kama da cousin nata dake Cyprus har hoton Munka gani

Rayhan tace Yes.but Mine is better tunda wacce nake Kama da ita she's classy unlike you da ake kira da Talatu Mai awara

Tasleem tayi gasping tace Whatever..! Kafin ta bude Christian Dior bag inta ta ciro 5k ta Mika ma tsohuwar mata tace sai akara gaba koh..

Sakin baki Mai Waina tayi tace indai ce ba jarin waran kk damka min ba? amma bana ki karba ba nagode Idan naje gida nayi ma Lanti godiya sai anjiman ku ta fada tana Washe baki kafin tabar gun...

Augh...!
Farhan tace Hmmmm nide ba wannan ba let's get back to business

I'm done... Inji Tasleem

No we're not done ku tsaya na gama baku labarin man The new lecturer

Uhm what a day OK go on..! Tasleem ta fada in a pissed off way...

He looks like Hazrat mohell in fact he's more handsome than Hazrat mohell oh girls sai kun ganshi.. a office din Dr Hydar na hadu dashi na gaishe sa,
Kunsa mai yayi min kuwa?

Suka amsa da No.

He repudiated me ta fadi maganar kamar zatayi kuka..

How? Inji Fa'eeh dake Son jin Karin bayani..

I mean koh kallon na bai Yi ba sai bayan fitar sa, Dr Hydar ke ban hakuri akan cewa haka yake
That he's Misogynist and Solo' shiyasa ma aka kawo shi lecturing zuwa A B U Don yayi socializing with people kafin Dad insa yayi Mai handing company sa, sannan yace min gaba daya rayuwansa a turai yayi.."

Wow! Tasleem ta fada in amused way..

Toh ina ruwan mu Farhan da wani Solo kema kinsa bama harkan da irinsu inji Suhyma..

Girls you need to see him he,'s so damn Handsome amma ya bini bashi kuma dole sai ya biya

How?

Ina so ya fada cikin tarkon mu duk wacca tayi nasara akansa tana da 2.5mil meaning kowane mu zai sa 500k as a bet duk wacca tayi nasara saita kwashe amma fa valid only for 3days

Tasleem tace Wow I like that..!

So let's toss the names on a paper and who's first..?

RAYHAN
SUHYMA
FA'EEH
FARHAN
TASLEEM

Wow nice ta karshe nasan ni zanyi winning sabida ba ɗa namiji da zai kalle ni batare da ya zauce ba Tasleem tafada tana gyara kayanta da issa da batsewa..

Fa'eeh tace Aifa mun ga alama, da wannan bakin fuskar da matsesen hanci ki agun shine zaki ce za kiyi winning Tasleem?

Toh Faee sai akace miki namiji fuska ya dame? Bara na tashi ki ganni, kinga wa Innan boobs da wannan hips nawa sunne namiji ke bukata bawai farin fata ba..

Hahhah says Who ? Sai kin hada da kyaun fuska da fata kamarni
Darrrr Fa'eeh tayi magana cikin shakiyanci..

Toh we shall see Then..!

Thanks
MissDmk✍🏻
09074267236*🌍D U N I Y A🌍*

BY

MissDmk ✍🏻

Page 16

Waye tawa waye nawa, Inno tace Yar Baiwa tawa, Habi tace to Yar Baiwata dazun na hadu da Talatu, cike da farinciki Inno tace a ina? Karkada Kai Mai Waina tayi irin tana jimamin tace uhmmmm yau ni naga Idi zindir,cikin tashin hankali Inno ta mike tace wani abune ya same Talatuwa ta? Habi tace A'ah koh daya Yar Baiwata,

Wai yau ni naga TALATU na nuna mata Sani yarinya tayi min cin kashi a gaban jama'a wai bata sani ba. Da mamaki Inno take kalonta tace wacce Talatu? Mai Waina tace Talatu dai yar Wajanki nagan ta gidan abinci tare da wasu manya yammata,na yiwaTalatu kiran duniya taki amsawa, murmushi Inno tayi tace in banda Abin ki Yar Baiwata kema kinsa bason sunan ta keyi ba da kin kirata da tasalam da zata amsa, Mai waina tace Uhm nunawa tayi bata sanin ba harta na gaya wa kawayen ta wai watakila ni almijra ce agaban hajiyata tayi min cin kashi nan, harta na dauko wannan kudin tana bani mai waina ta fito da kudin tana nuna mata, hakuri zakiyi kinsa daman baku jituwa da ita, toh Yar Baiwata wannan kudin ina ta samo su? Murmushi Inno tayi tace wa'inan da kk ganta dasu suke taimaka mata, baki ga yanzu sai tayi sati biyu bata lekoni ba ke bari zance nan,

Habi yau suwaiba duk ta bata mana gida da karni amai kai wannan yarinya akwai kazanta, ke ko ruwa na kasa sha sabida kazanta, wai haka ta daura maku girki,Mai Waina tace Cabdi aiko saide mijinta yaci ba daini ba, in banda ita Dodi minal Dodi ce kiyi amai kuma kizo kiyi girki, abin takaici ma ko tayi girkin sai kofa, sabda ba dadin gaba bale na baya,

Inno ta kara dacewa girki kamar a wanke Kai, Yar Baiwata kuna fama da kazanta yo dole Alhajee ya Kore ku daga gidan sa.. Habi tace wai ina sukayi ne? Inno tace asibiti man..

Suna cikin haka Tasleem ta fado cikin gidan rai bace, da murmushi Inno tace Talatuwa ta mai akayi miki ne? Cikin shagwaba tace haba Inno taya mai waina zata gani cikin Kwayene ta wani kirani da Talatu mai awara?

Da mamaki Habi take kalonta tace to ba Sana'a bace? Ko karuwa na kira ki dashi? Da zaki nuna baki sani ba?

Inno ki gaya mata duk ranan da ta sake gani na a waje ta daina nuna ta sani, ta bari ina zo gida mayi zuminci walhy Idan ba haka ba sai nayi wata ban leko ku ba, tana fadin haka ta mike ta shiga daki, bin bayanta Inno tayi tace haba Talatuwa ta, Habi fa aminiyata Idan kin wulaqanta ta ai kamar ni kk yi wa, Don ALLAH ki fita ki bata hakuri ni kuma na miki alkwarin baza ta sake nuna ta sanki a waje ba, zumburo baki tayi tana kunkune kafin taje ta bata hakuri ta dawo, tace Inno idan anyi Hutu zamu yi tafiya a school ana Kiran tafiyar da field trip" kuma muna dawowa zamu fara shirin exams, Inno a taya mu da adu'a, Inno tace in shaa ALLAH saide mu kara akan wanda muke yi, wai ya maganar Mal Nazeefi?

Tasleem tace tuni ya kama gabansa ya gane ruwa ba sa'ar kwando bane tayi magana tana bude wani Ghana must go, ta ciro wayan ta, ta kuna kai tsaye tayi dialing number Meems, bugu daya Meems ta amsa, Tasleem tace kina gidane? Gani nan zuwa kit ta yanke Kiran ta kalle Inno tace ni zan koma.. Da adu'a Inno ta bita dahi har ta fice...

Direct gidan su Meems ta nufa, tace Yar Baiwata ba na baki labarin Dubai trip da zamu ba? Meems tace eh ya akayi? Kin samu 500k din ne?

Tasleem tace ina fa? To Abin yazo min da sauki harda na fara tunanin Kiran Mulas koh zan samu Abu aman yanzu an wuce gurin tunda Ansa gasa duk wacce taci gasar zata kwashe 2.5mil..ware ido waje Meems tayi tace what? Tasleem tace yes and ina ji ajikina ni Zanci gasar, Meems tace what if baki ci ba ya za kiyi da wacce taci?

Meems indai ban ci ba to ba wacce zata ci a cikinsu, sun girme ni aman nafi su wayo da bude ido duk cikin su ba mai saurayi hasalima basu taba tsayawa da wani ba kinsa auren masu kudi arranged marriage ne..

Sauke ajiyan zuciya Meems tayi tace ALLAH ya baki sa'a K'awa ta, murmushi Tasleem tayi tace sa'a tawa ce tunda ina da wa'inan makamai.. Tafawa sukayi cikin shewa, Tasleem tace bara na wuce suna jirana..

Har bakin titi Meems ta rakata, kafin su kayi salama,10mins ya kaita cikin school, gobe ne Rayhan zata fara gwada sa'an ta, abinda baka Saba koh karatu ta kasa yi, gashi gobe suna da test mai zafi..
Chapter 15 · 0% Book details