← Book details Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 16

Sashe 5

Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

nazari, jimawa kadan tace 'manisha patel' tace
cikin dinkunan da yaya sa'idu ya karbo miki
zaki sanya ko cikin' kayan auren ki? Bari in
kawo miki kayan auren ki gani nayi maza tace
mata a'a sahura, a'ina kika ga mutum yana
kallon kayan auren shi? Ta kelkele da dariya
tace to wa zai sa miki in aki kalla ba? Hi'um ai
nikam dani za'aje yin soyaiyar kayan aure na,
nace tafdi, siket da pant din dana sanyan sune
na farko dana taba sanya irin su don haka ba
karamin dadi suka mun ba, sahurace ta tilastani
sanya brazier tunda ban taba sanyawa ba,
sannan na zaka /ata doguwar riga mai rowan
madara tasha ado ko da ban san darajar kaya ba
nasan rigace mai daraja na dinko gyaran tana
yafe a kaina bayar, sahurata nade mun gashin
ya zama tanfar gammo abaya ta dauko turare
tana fesa min tana fadin kai ashe dai yaya
sa'idu yasan abin da ya gani, bari Allah Ya
kawo yaya babba yau ta ganshi itace mai cewa
bata ga abinda ya gani ba ajikin ki da yaje yayi
wannan wahalallen aure na cin mutuncu nace
mata waye yaya babba? Tace itace babbar
yayar mu nan take sai na tuno da maganar su da
Mahmud dana taba ji ina cikin wannan tunanin

39

Sahura ta katseni ta hanyar gaya mun kinga
wadannan dogayen rigunan duk da tsadar su
Buda goma sha biyu yaya sa'idu ya zuba miki a
Cikin kayan ki, ai zaki sha ado tayi maza ta juya
ta dauko madubi ta miko mun kalli kanki don
Allah kiga irin kyan da kika yina karbi madubi
na kalli kaina ni kaina da kyar ya rage ince
mata ko dai bani bace na dai daure nayi shiru.
Sa id yayi sallama ya shigo dakin wata
yar rigance kawai kawai a jikin shi sai wani
wando tirikwata, yayi matukar yin kyau ga
kanshi shin a koyaushe a tare da shi ya danyi
Waige-waige tanfar yana neman wani abu,
sahura tana kallon shi tana murmushi ya dan
gaji yace sahura ina amar yata fa nake nema
tace ai gatanan ya bata fuska yace ina wasa
dake ne? Amarya ta ta manbila maryam nake
gaya miki ta kelkele da dariya tace ai itace ta
zama 'manisha yaya ya dan rage fara'a yace
mata ina umma? Tace mishi vanzu baba ya kira
ta tana can yace to, jeki ki gyara mun dakina,
tace to, ta karbi makullin a wurin nashi taná
barin dakin yasa hannu ya saki labulan
windunan hasken da ke dakin ya ragu ya matso

40

kusa da ni ya kamani nan take naji tanfar
nunfashi na zai dauke, saboda tsorata da nayi na
bude baki zan mishi ihu ya zare min ido yace
shhhhh!!! Nayi maza na koma cikin natsuwa ta
yace ne kike nufi da man da zakayi? Umma ta
san an daura mana aure mene ne? a tsorace
nace mishi me zaka mun saboda ganin irin
rukon da yayi mun, yace ba komai zan dan
mutsustsuka kine kawai don in fahintar dake
cewa yanzu da dah ba daya bane. Yana fadin
haka ya shiga aiwatar da wasu al'amura a
kidime na kwala kira umma!!! Yace ki kira ta
mana in ta zoma yi zatayi kamar bataga abindda
nake yi ba, da sauri umma ta shigo alamar taji
kiran da nayi mata tana shigowa taga sa id yana
kokarin maida labulayen yanda suke, tace mishi
kai sa' id kar in sake ganin ka a dakin nan, yace
to, umma tayi waje, ita kuma ta karaso cikin
dakin tace mun muje ki gaida baban ku ko?
Nace mata to, na biyo bayan ta zuwa falon shi
yana zaune kan kujera mai zaman mutum uku,
ita kuma umma ta koma kan wata kujerar ta
zauna, ni kuma na durkusa a kasa na gaishe shi,
yayita sa mun albar ka daya gama sai umma
tace mun kije ki gyara mana dakunan suyi kyau

41

ki debo gaushi a kicin ki sanya mana turaren
wata nace mata to, naje na kama aikin da tasani
sa'id ya sake shigowa zai sake yimun irin
abinda yayi mun dazu, nace mi shi zanyi ihu,
yace kiyi mana, sai ta gane na matsa dake tayi
gaggawan mayar mun da ke wurina ba shikenan
ba?
Ranarda na cika sati guda a gidan ranar
ne su yaya babba da yaya balaraba suka zo suka
hadu suka kayi aikin gyaran wuri na suka jera
mun kayan da babana ya bayar da kudi yace a
saya mun, wuni sukayi suna aikin sai bayan
sallar magariba suka tafi gida.
Kamar kullum, sa'id ya shigo yayi hirar
shi a falon umma da ya tashi zai tafi sai ya dan
rage murya yace mata umma tace na am, ya
danyi shiru jimawa kadan sai ya sake ce mata
umma tace mene ne? yace uma inace dama
rashin gyaran wurin tane yasa take zaune anan?
Tace a'a ba shine dalili ba, yace ai to sai da
safe, tace Allah Ya tashe mu lafiya. Ina zaune a
wurin umma cikin kwanciyar hankali tayi mun
hikimar dana saki jiki da ita yan kananan
aikace aikacen ta ni take sanyawa bani ruwa in

42

sha maryam, dauko mun wancan kawo mun
wannan in anyi baki tace inzo in gaishe su,
wani lokaci ma in sahura bata kusa tace inje
kicin in kawo musu abinci, shima sa'id din
yanzu in ya shigo ni take sawa inyi mishi
abinda yake bukata, tana bani umurnin inyi
mishin kuwa zata kauda jiki ta barmu mu biyu
shi kuwa yana ganin ta fita zai fara Magana
yanzu nan ke umma gata tayi miki data rike ki a
wannan tsohon dakin? Kinga yanda aka gyara
miki wurin ki kuwa? Kice mata zaki shiga ki
gani na makale kafada nace uh uh yace to muje
yawo a mota zaga gari ki ga birnin Kano daga
nan sai muje insaya miki abin nan na
shekaranjiya tunda naji kina gayawa sahura
yayi miki dadi. tace uh'uh banaso ya bata rai
yace to kiyi ta zama a cikin dakin nace mishi to
ya tashi ta fita da daddare ranar ma sai da ya
sake tanbayar umma, umma ni sai yaushene ita
maryam din zata koma wurin ta? Tace mishi sai
Allah ya kaimu anyi sallah lafiya kannan ta
gama wastsakewa ta zama 'yar-gida, yace to
Allah Ya kaimu, ya tashi ya fita ko sai da safe
baice ba, alamar ya fusata.

43

Washegari kuwa wajen karfe takwas da
rabi na dare muna cikin kallon wani fim mai
matukar kayu ni da sahura, umma ta lekoi tace
mata jeki ki hadawa maryuam rowan wanka,
taje tayi ina zaue a wurin ina jin kanshin
abubuwan da ta zuba a ciki ta fito tace mun in
shiga nace to, a tsaida kallon sai na fito, tace
gaskiya sai dai in kin fito a mayer baya nace to,
naje nayi wanka na mai kyau ga dadi saboda
irin kanshin nayi matukar fita, gashi kuma
dama tuni na kara kayau na kara 'yar-kiba a
dalilin hutun dana samu na fito na shata mai,
sahura tn tayani gyara gashi na wanda nake
ganin tanfar kullum karuwa yake yi, saboda irin
kulawar da yake samu, wani boil mai matukar
kyau umma ta baiwa sahura ta pani na sanya
dinkin shi ma yayi kyau har bai yiwu in tsaya
kwatan tawa siket ne da doguwar rigan sai
dankwali dan karami, a dalilin rigar taci yadi
maiyawa, gashi tasha adon zare abin gwanin
sha'awa, ta cire mun 'yankunne abin wuya da
wara-warai duka na zinariya na sanya tunda
nazo gidan ban taba kyau irin nayau ba, dana
gama na feshe jiki na da turare don na riga na
saba kuma na koma na zauna sahura ta na cewa

44

kan uban can, ke aima ni yau sai naga kamar
kin fiye mun manisha patel din kyau, bari in
sake kallon ki in gain dawa kuma kike mun
kama? Umma tace mata ke matsani ki bani
wuri mara kunya kawai, umma ta nemi wuri ta
zauna tace mun ga gyale mahadin kayan nann a
gefen ki yafa zan kai ki wurin baban ku yasa
miki albarka daga nan kuma sahura zata raka ki
dakin ki sai muyi fatan ubangiji ya baku zaman
lafiya dafahintar juna ke da mijin ki, inajin
umma ta soma wannan bayanin na soma kuka
ita kuwa sai rarrashi na takeyi bafa wani wuri
. ne mai isa na,ga gidan can ga kofar shigannan
a tsakar gida, duk lokacin da kike so zaki shigo
don haka bamu rabu ba, muna nan tare ina kuka
nace mata kiyi hakuri ki barni anan, kawai tace
bazai yiwu bane nima bay au naso komawan
naki ba, naso ne sai anyi sallah tukunnah, to
sa'idu yaje ya kaini kara wurin baban ku sai
kuma yace yau din nan in baiwa sa'idu
matarshi ai kuwa kin ga babu hali in kin bi
wannan umurni tashi muje yayi muna gardama
dake yayi zaton taurin kai ke gare ki akan dole
na mike na biyo bayan umma zuwa dakin

45
Chapter 5 · 0% Book details