Sashe 3
Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
halitta su manta da wanda yayi halittar), zasu
sO sabi, wato aikata zunubi su mance da yawan
tuba, ma'ana neman gafara, zasu so mallakar
manya manyan gidaje su mance da kabarin
su. Ardo ya kalle ni cikin tausayawa yace
nayi miki sha'awar rayuwar da kika guda
rayuwa mai sauki, rayuwar da babu tsanani mai
yawa a cikin ta, tun da mukan ai jeji muke
zaune, to amma kowa da kaddarar rayuwar sa.
Mata biyar ne kawai ardo ya yarda suyi
min rakiya, abin yayi matukar batawa maizube
rai, kanwar ardo da suke yaya maza turai sai
yayar bodejo da suke daki daya daso kakata
mahaifiyar bodejo, ita kuma sai ta wakilta
kanwar ta mogurun,matarz aminin ardo altine
sai ko kanwar maizube takko shikenan sai ko
maizuben kanta suka zama shida.
Motar da ta dauke mu hudu ne, ni da
maizube a baya, sai ko Hajiya daso da tasi'u
kamin sa'idu a gaba, ta biyu wanda shi ne mai
yin tukin wai sunan shi jamilu, sai sauran
motocin suka biyo baya, wandana angone da
abokan shi, da suka tsuya-ganin wasannin da
akayi.
23
Tafiyar ba mai tsanani akayi ba, a dalilin
motar su sa'id dake biye da tamu suna ganin
tasi'u zai daga kafa zasuyi maza su tsawatar
mishi suna tanbayar shi saurin me kake yi
haka? Don haka tafiya akayi cikin nishadi,
muna tafe suna sanya mana kasunan wa'azi,
mafi yawan ci kuma suna magana ne kan aure
da kuma ma'auratan ga kuma kayan ciye-ciye
iri iri sai dai nikam ban iya cin komai ba saboda
kukan da nakeyi.
Mun shigo birnin Kano ne cikin dare
fitilu masu tsananin haske ko'ina akan tituna,
nikam hanken har haskemun ido ya rin kayi a
zuciya ta nace iko sai Allah, wato abirni ashe
ba'a duhun dare, babu zirgar motoci akan
shinfidaddiyar kwaltar, a haka tasi'u ya rinka bi
daga wannan kwaltar ya koma wancan har
muka iso inda ya shiga wani layi daya tsaya, a
kofar wani gida, abin mamaki ban san yanda
akayi ba ina bude ido sa'id na faragani a tsaye
tare damutane masu yawasuna jiran isowar mu
ko yaya akayi suka shige mu oho ?
Sannnun ku da zuwa, sannun ku da
zuwa, irin abin da mutanen ke ta fadi kenan, sa
24
hannu akayi aka bude kofar danake aka fito
dani sai dai banga wanda yayi hakan ba saboda
a lullube nake, sai da aka kaini wani wuri mai
tsananin kanshi sannan naji ance mun zauna
anan, na zauna na dan bude ido a hankali sai
naga ashe daki ne mai matukar kyau, ganin
maizube a kusa da ni ya sani naji dadi na gyara
na tankwashe ajikin ta na kwanta sai shigowa
mutane sukeyi suna yi mana barka da zuwa,
ruwan sanyi suka fara kawo mana sannan suka
fura aka kawo mana suka shigo mana da
nau'o'in abinci iri iri, wadan da ma nikam ban
taba ganjn su nayi ba, an dai yi sa'a sun yi
dabara sun hada mana da fura da nono mai
kyau, abin da yawancin mu muka ci kenan, sai
ko naman kajin. Ranar lahadi itace ranar da
iyayen sa'id suka yi wunin bukin su, abin da ya
tabbatar mun da cewar lalle sa'id dan dangi ne
daga yawan matan dake zuwa suna tsokana ta
alamar abokan wasane su na gane yawan su ba
na kadan bane.
Washegari litinin, baki na kusa kusa sun
tafi, duk wani wanda ya saura a lokacin to daga
nesa yake, mahaifiyar sa'id wacce naii suna
25
kira umma ta shigo ta kira iyaye na cewar
baban su sa'id yana son ganin su, suka tashi
suka fita suka barni kadai, sai naga wata
yarinya mai fara'a da murmushi ta shigo dakin
da saurin ta tazo ta tsuguna a gabana, ni kuwa
nayi maza na gyara lullubina na juya mata
keya, sai naji tace mun kinga ai nice sahurar da
yaya sa'id ya baki labari na wanke-wanke,
mukayi na bari nazoi don ki gan ni in gan ki,
ina jin ta fadi haka na juyo nima na kalleta
mukayiwa juna murmushi, kama da sa'id takeyi
sai dai ta fishi haske tace mun nayi murna da
kik a yarda kika auri yayan mu, kin nuna mana
kauna da son mu dama kuwa ya bamu labarin
irin taimakon da kikayi mishi mu kuma..... bata
gama ba su maizube suka shigo da gudu ta tashi
ta fita ta koma wurin aikin ta.
Maizube ce ta ban labarin abin da akayi
cewar baban su sa'id ya roke su su tsaya suga
an gama shiryamun dakina kafin su tafi, tunda
shi ardo ya dankawa kudin a hannu yace mishi
yaje ya saya mun irin abinda yake saiwa yayan
shi mata idan zai yi auren su, shine tace mishi
a'a ba sai sun tsaya sun ga wannan ba, su
26
kwana biyu ardo ya basu don lhaka gobe in
Allah Ya kaimu zasu tafi.
Umma ta shigo ta nemi wuri ta zauna
tace gaskiya maizube bai kamata kiyi haka ba,
ai in kun tsaya an gama komai shima zakuje ku
bashi labari, maizube tayi murmushi tace
seungel ai ta fita hannun ardo ta zama taku, ba
zai damu da sai yaji abin da aka yi mata ba, ku
dai kuyi hakuri da ita, saboda dalilai guda biyu,
na farko ita din yarinyace da ta fito daga jeji,
bayan haka kuma bata da kowa anan tana fadin
haka hawaye suka zubo mata, nima ina ganin
awayen maizube na kama wani sabon kukan.
Umma ta shiga baiwa maizube hakuri
tana fadin ai kuwa in Allah Ya yarda maryam
gida tazo, babu abin da zai faru sai alheri, ita
amana ai dayace, sannan in nasan bazamu iya
yiwa yarinyar nan adalci ba bazan bari sa'idu
yaje ya rabota daku ba, don haka don Allah ku
kwantar da hankalin ku, kuma ina ganin zaku
daga tafiyar gobe zuwa jibi,don ku din huta
tukunna.
Maizube tace a'a ai shima maigidan yayi
wannan maganar na gaya mishi bazai yiyu ba,
27
don umurnin da ardo ya bayar kenan tace
hakane.
Bayan salar isha'I, ina kallo umma ta
shigo da manyan jakankuna guda biyu, tace wa
maizube baban su sa'id ne yace akawo musu, ta
kuma kawo manyan kwallaye guda biyu na
kayan tsarabar buki da sukayi, tunda sun san
mu bayi zamuyi ba, don bamu sanda shi ba tace
ayi tsaraba na kalli maizube nace mata goggo
tafiyan zakuyi? tun kan taban amsa na fara y1
mata kuka ita da umma sukayi ta rarrashina sai
dai kuma na kasa yin shiru, tasi'u ya sake
shigowa dakwando nar. goro guda uku da
dabino cikin kwarya da kuma kwalayen minti
ya ajiye yace wai gashi na ardone maizube sai
faman godiya takeyi tana fadin irin dawainiyar
da akeyi dasu, shikam tasi'u murmushi kawai
yayi yace shi kuwa yaya sa'id cewa bai taba
ganin inda ake dawainiya da mutumin da ba'a
sani ba, ba asan inda ya fito ba irin rugar su,
maryam in kuwa hakane, goggo to mu me
muka yi kunyi hidima da dan uwan mu kun
kuma bashi aure ai mu bamu da abinda zamuce
muku da alheri kuma gobe in Allah Ya kaimu
28
daga yin sallar asuba ne zamu tafi, maizube da
sauran sukace mishi to Allah ya nuna mana.
Tun kafin ayi sallar asuba har sun gama
wanka sun shafa mai sun kintsa, umma ta kawo
musu abin karyawa ga kuma wasu manya-
manyan kuloli guda biyu wai maganin yunwar
hanya,nikam tunda naga haka na kama kuka,
umma ta shigo dakin tace mun ga ruwa can na
kai miki maryam, shiga kiyi wanka,nace mata
to, ta juya ta fita maizube tace mun to sengel
kin dai san mutanen da kika zabi zama dasu,
mutanene dabaki hada komai da su ba, na
zumun ci, halin ki mai kyau ne kadai zai
taimake ki a zaman da zakiyi da su, na umarce
ki da ki rike al'anura guda biyu, hakuri da
kunya, ban iya amsawa ba, saboda kukan da
nakeyi, ta dan sakaici idon mutane tasa hannu
cikin aljihun silet din ta ciro wani dan kwalban
turare ta mika mun nasa hannu biyu na karba,
tace a kirji zaki dan rinka mustsukawa, duk
lokacin da kika san zakije kusa da mijin ki
nace to, umma ta sake shigowa maryam ruwan
nan sai yayi sanyi ? nace mata to, na tashi na
shiga wanka, abin takaicin shine sai fitowa nayi
29
na samu babu su maizube, babu dalilin su, ai
kuwa ban shafa mai ba dikunkunewa nayi cikin
zani, nayi ta saman kuka, kuka kuwa mai
tsananin gaske, umma tayi ta rarrashi na har ta
gaji ban dena kuka ba, sahura ma ta shigo ta
zauna kusa da ni haba anti maryam ba aure kika
Z0 yiba? dama zaki sake bin sune ku tafi tare?
Kiyi hakuri mana, kar ki jawa kanki wani ciwo,
yauwa ni gam,a yay sa'idu ya shigo ina jin ta
fudi unan shi ban san yanda akayi ba sai kawai
naji kukan ya tsaya cak, rashin banji wani
motsiba ya sa na dan dago kaina wai in gani ko
zolayata take yi sai kawai muka hada ido da shi
yana tsaye a bakin kofar cikin dakin, sanye da
doguwar riga, jallabiya mai ruwan madara me
ya saneta take kuka sahura? yayi tanbayar
cikin wata irin murya mai cike da nutsuwa.
Sahura tsace don iyayen ta da 'yan
uwanta sun tafi sun barta yana matsowa cikin
wata irin tafiya mai cike da takama yana
magana a hankali gaya mata mana sahura nan
gidan ma akwai umma da su tasi' u sannan
kema gaki ko kuwa ? tayi murmushi tace
hakane yaya. ummata shigo yayi maza ya ja
30