← Book details Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 16

Sashe 10

Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

murmushi don Son ganin yanayin ta bata canza
ba, sai kawai naji tace to tashi ku koma can din
yanzu, nayi maza nace kiyi hakuri umma tace
a'a ai. kinga yanzuma ba wani karyawa yayi ba
kuje .can ki shirya mishi abin karyawa Allah Ya
kiyaye na gaba yace amin, umma Allah Ya kara
girma ta tashi ta fita yace to tashi muje mana
maryam nace a'a sai da yanma yace haba
maryam bayan umma tace mu tafi yanzu nace
gaskiya ina jin kunyar umma yace to bari in
leka miki tsakar gida in gani in bata nan sai
kawai ki wuce abinki a hankali ba mai jin takun
kin ace mishi to yayi maza ya tashi ya leka yą
gani sannan ya dan yafutoni da hannu nazo kin
gani ba kowa yi ki wuce nace to nayi maza na
lwuce na shiga wurin mu.
Sa'id yana shigowa yasa makulli zai
kulle kofar da dan key nace a'a yaya zaka kulle
kuma? Yace sai kinyi adadin kwanakin da kika
yi can baki shiga gidan ba, nima ramawa zanyi
badai ke komai aka miki sai kije ki kai kara
gurin umma ba? Ita kuwa tace miki kiyi
zamanki ba tare da tayi binciken abinda kikayi
ba, saboda ke tana son kin a zuba mishi ido ina

77

kallonshi cikin tsoro yai yi muirmushi yace kar
ki rinka jin tsoro na maryam girmamawa ne
tsakani na da ke, kin gane? Nace uh ba tare da
na saki jiki ba muje kiyi mun abin karyawa,
kinji ko? Baki lura kwanakin nan na dan ragu
ba? Ban tanka mishi ba na shiga kicin ina
shirya mishi shima ya shigo yana tayani, wunin
ranan bai fita ko'ina ba, muna tare a gida duk
kokarin shi bai wuce nason ganin dashi mun
koma kamar da ba wanda ba'a wani dauki
lokaci mai tsawo ba, hakan ya yiwu.
Kammala karatuna na yaki da jahilci da
kuma koyon girki sai na zama babu abinda
nakeyi in banda zaman gida naso kwarai ace
sa'id ya bar ni na shiga makaranta, don ina
matukar sha'awar karatu amma sam yaki bisa
hujjar da bai wuce kishi ba. Wai wannan ma
abinda yasa naga ya sanyani don matane ke
tafiyar da dukkan al'amuran inna tashi da safe
kan kace meye wannan? Na kanmala dukkan
aiyuka na bani da wani abinyi sai ko in dan
dauko littafi ina karantawa wajen buda baki,
wannan dalili ya sanya shawarar da hajiya
salma take yawan bani na in nemi sana' ar da

78

zan rinka yi yayi matukar karbuwa a zuciyata
sai dai sa'id ne bai yarda ba, babu yanda banyi
da shi ba, babu irin rartashin da ban yi mishi ba
yaki, rannan dai na yanke shawarar zuwa in
samu umma kan maganar nayi mata bayani tace
to bari sai ya dawo zata hadamu muyi maganar
nace mata to.
Da daddare kuwa yana falon ta malle
tazo ta kirani nasan maganar ne don haka da
zan tafi sai na tafi mishi da abincin shi ina shiga
na ajiye mishi tare da yi mishi sannu da zuwa
sannan na nemi wuri na zauria nace wa umma
gani, umma tace maganar da kikazo kika mun
ne nayi mishi maganar shine yace yana son
sanin abin da yasa kika matsu sai kinyi sana' ar
akwai wani abinda ya rage miki ne?
Na sunkuyar da kaina kasa cikin ladabi
nace mata a'a, umma ba abinda nake nufi kenan
in ranshi y abaci yayi hakuri ni dai kawai na
gane wuni nake yi a zaune bana aikin komai, ni
kuma ban saba haka din ba, bana jin dadin
zaman ina bukatar wani abinda zan rinkayi don
in rinka motsa jikina, ni shine kawai bukata ta.

79

Umma tace to kai kaji bata raina abinda
kake mata ba, saboda haka in kaga baka son yin
sana'ar iat a to ka barta mana ta rinka zuwa
makaranta tare da su sahura tunda gashi hart a
dan fara iya karatu da rubutu, ai ina ganin ba
zai mata wahala ba, yace zanyi tunani tukuna
akai, tace to Allah Yayi mana zabi na alheri
yace amin.
Rannan da yanma ina tare da shi a dakin
shi, shagwaba nake mishi ya zuba mun ido yana
kallo na cikin natsuwa, jimawa can sai yace ke
maryam muyi zaman mu haka kina taraita ta
baifi miki dadi. ba? Ki fiso sai kin kinkimo
wani aiki da zai dauke hankalin ki daga gare ni?
Kofa amarci baki gama ci ba, kwata kwata yau
watan ki tara ne a gidan nan, na sake langwabe
a jikin shin ace mishi sana'ar da nake son yin
ba zata shafi komai game da abinda na saba yi
maka ba shi ya sa ma nake so in gaya maka
aduk lokacin da ka amince da yin sana'ar to
zanyi tane bisa sharuddan da zaka kafa mata,
kuma maganar amarci yayan sahura ai kace
mun amarcin nawa ba zai taba karewa ba, yayi
murmushi yace haka ne maryam, amarcin kin a

80

har abada ne, nace to ai nima bazan yarda ya
shafi amarcin mu ba, kana ganin za'ayi hakan
sai ka dauki matakin hanawa yace to shike nan.
To da haka na fara sana'ar yin cake, meat
pie, cin-cin da dai sauran abubuwa da suka
shafi bekin, ana kaiwa shagon hajiya salma ana
ajewa duk da akwai kudi na wurin sa'id bai
yarda nayi anfani dasu a matsayin jari ba, kudin
shi ya zuba ya saya mun dukkan kayaiyakin da
nake bukata, wai in sana'ar taci gaba shike nan,
inma ta tsaya a hanya sai kayan su zama kayan
anfanin gida, hakanan su flour, sugar, butter da
dai sauran su duka da kudin shi ya saya.
Mun fara ne da kadan sai gashi tana
aiken a kara yawan abin da akeyi, kowanne sati
kuma zata aiko mun da kudi na, ni kuma duk
kwana uku zuwa hudu nake aikawa da sabo a
hankali sai ya zamo ana bukatar in bayar
kowanne kwana biyu, na hada kudin ajikin da
akayi na watanni biyu na kawa sa'id nayi mishi
bayanin komai yayi matukar jin dadin ganin
yanda abin yake tafiya ya kalleni cikin
murmushi yace dadi na dake ke din jarumace,
na taya shi murmushin nace mishi sai dai

81

gaskiya bukatar taimako, don aikin ya soma
mun yawa, inka yard azan nemi mai aiki zan
kuma sanya sahura da jamilu a cikin abin ya
kalleni kamar yaya? Nace tunda akwai samun
alheri a ciki zan jawo sahura mu rinka yi tare
muna raba ribar da ake samu shi kuwa jamilu
ya zama shine mai zuwa kasuwa ya rinka sayo
mun abubuwat da nake bukata, in an gama
kuma ya dauka ya kai mana, shi sai a rinka
bashi nashi kason.
Sa'id ya kalleni cikin jin dadi da alama
yaji dadin yanda zan jawo yan uwanshi cikin
lamarir yace bari kiji yanda zakiyi, zaki rinka
tara riba ne a wata kiga nawa aka samu, sai ki
cire kudin ma'aikata tunda kince kina bukata
har da masu aiki in kin biya su abin da ya saura
sai ki kasa shi kashi hudu daya ki ajiye, saboda
kayan aiki kin san dole wata rana kya bukaci
sabbi ko kuma kari nace eh yace to kashi daya
ki rabawa sahura da jamilu sauran kashi biyun
kuwa sai ki rike tunda kece mai sana'ar nace to
amma in ka yarda a rinka rabawa kashi uku
kawai kayan aikin daya, ni daya, sahura da
jamilu daya, yace to shike nan.

82

Shigarda sahura da jamilu da nayi cikin
harkar ba karamun dadi yayi mun ba,na farko
dai ni da sahura sai muka kara dunkulewa muka
zama abu daya ko umma bata sanin abin da ke
tsakanin mu, shi kuwa jamilu sai ya zama
kullum a cikin nemo mana sabbin kostomomni
yake, kan kace meye wannan sai abu ya zama
gagarumihar bai yiwu wa kazoo kai tsaye kace
kazo saye yau ka samu sai dai kayi bukin, nan
da nan sai gani da yan aiki har guda biyar, aikin
yayi matukar bunkąsa, kasan kowanne sati sai
na baiwa sa'id kudi nace akai mun banki. In
wata yak are kuwa dauko takardąr da mke
rubuta ciniki abinda muka saya da wanda muka
sayar nakeyi inji lissafi in san biyan ma'aikata,
ta nawa ya kamata in baiwa su jamilu na maida
umma ta zama tanfar mahaiti yata, kusan
kowanne lokaci a cikin yi mata hidima nake, in
mata dinki in bata kudi in sai mata abin da na
gani ya bani sha'awa.
Rannan sa'idu ya dawo gida da yamma
kamar kullum nayi maza na wanke hannu na
cire rigar sApron dake sagale a wuya na, na
rataya na barwa sahura aikin da nakeyi nazo na

83

same shi yana tsaye da alamar dai wani abu
yadan sosa mishi zuciya, nayi mishi sannu da
zuwa tare da tanbayar shi lafiya? Naga kamar
yadan canza? Yace mun lafiya kalau, banyi
baki yi baki ba bayan fita na? nace mishi a'a a
sanina dai babu wanda yazo, zaka ci abinci
yanzune ko sai ka huta? Yace sai na huta nace
to, na zauna tare da shi ina yi mishi abubuwan
da suka dace inyi mishi don wastsakar mishi da
damuwar dana hanga tare da shi sai dai banga
alamar gamsuwa ba a tare da shi, na gaji nace
mishi me ya faru ne naga kayi wani iri? Ya
daga ido a hankali ya kallen cikin natsuwa a
hankali ya bude baki cikin wani yanayi mai
kama da na maijin tausayin kanshi yace mun
jna Sonki maryam wata irin matsananciyar
soyaiyar da nake bukatar gaskiya da amana a
tsakanin mu na danja jiki daga gare shina koma
gefe na zauna ina kanllon shi cikin natsuwa
nace abin da kake bukatar shine a tsakanin mu
yayan sahura in banyi maka gaskiya ba ban rike
maka amana ba to wa zanyi wa? Yayi maza
yace yauwa, abin da nake so ki gane kenan don
haka gaya mun gaskiya daga shekaran jiya
zuwa yau su waye suka zogidan nan? Na lissafa

84
Chapter 10 · 0% Book details