← Book details Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 16

Sashe 16

Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

zan miki kashedin inma shi ya bakı shawarar in
muna maganar dake ki rike ni to kar ki sake
sakemun rigata nace bazan saki ba sai ka
salla.....ban karasa ba ya juyo cikin sauri ya
dauke ni da wani gigitaccen mari sai da ya kifar
da ni a kasa ya wuce yayi tafiyar shi ya shige
dakin shi ya turo kofa ya rufe, na gama
kwanciyata anan har na gaji na tashi na koma
daki na kama shirye-shiryen tafiya manbila zan
koma gaban 1yaye na zan koma rayuwata ta
farko ta fimun wannan rayuwar da nake yi a
yanzu, na kara gane gaskiyar ardo da yace mun
babu komai cikin rayvwar birni in banda
kwarauniya da kwamacala na kammala shiri na
tsaf sai dai kuma abin takaicin shine ban
mallaki komai ba in banda naira dubu daya da
dari bakwai a dakina na tsaya ina tunanin ina
zan samu kudin mota'? Nayi ta tunani na rasa
sai nace to bari tunda tafiya zanyi bari inje in
tunawa sa'id rabon da ya bani kudin aiwatar da
hidimar gida kusan kwana arba' in ne in yaso in
ya bani sai inyi amfani da su kawai, ina išowa
dakin nashi sai kawai naji shi yana cewa aikin
sun da itan kika bugomun wayar a yanZu tunda
kuwa tsoron da kike magana akai bai hanaki

121

bugomun wayar dare ba nima kuwa ai bazai
hanani amsawa ba da sauri na bar wurin saboda
wani abin da naji zuciyata tana yi ban taba jin
maganar sa'id da wata mata ba tsawon zaman
da nayi da shi sai ko yau har gari ya waye ina
tsaye a dakina ban samu zama ba balle inyi
tunanin kwanciya malle ta shigo ta sameni a
tsaye gaishe ni kawai tayi ta juya zata tafi nayi
maza nace mata zo mana malle ta dawo ta
tsuguna tace ganı nace mata zani manbila yanzu
kizo mu tafi amma karki gaya wa kowa tace
a'a, bazan biki ba, nayi maza nace mata akan
nme malle? Na zauna ina rarrashin ta ta yarda ta
bini mu tafi, tace mun a ajiya da daddare tayi
wa yaya sa' id alkawarin zata zauna da shi na
sake kallon ta nace alkawari malle kina
haukane? Tace mun kiyi hakurI amma na gaji
da irin sabinda kike mishi ace shi da gidan shi
amma wai jiya ya kwana a waje sabaoda gudun
fitinar da zakiyi mishi bayan daga tafiya ya
dawo kuma ai baffa yace mana abinda duk
muka san bama so ayi mana to muma kar
muyiwa wasu da matar yaya jauro take koro shi
waye yake kwana ai tashin hankali kuka rinkayi
da ita to yaya ke kuma zaki so kina Koran yaya

122

sa'id? Da sauri nace mata ke malle wane irin
maganar banzane wannan nice zan iya Koran
yayan sahura daga cikin gidahnan? In baki sani
ba jiya har duka na yayi na kuma ji shi yana
waya a dakin shi suna hira da wata mata nan
take ta kama kuka dadi ya kamani don ina
ganin kukan tausayi na take yi sai kawai naji
tace mun Allah sarki da-da in zaki mance da
komai ai bai kamata ki mance da nasihar baffa
ba ko don soyaiyar da yake miki shi kuwa
nasha jin shị yana cewa mafi munin abinda dan
adam zai yi shine fadar maganar da ba gaskiya
bace kinre mun ya þuge ki kuma kin jişhi yana
hira da wata a waya bayan kumá ni yaya sa id a
dakin mu ya kwana yana gaya nmun ya bar nan
dinne sabodd gudun fitinar ki, a kidime nace
mata a wurin ku yayan sahura ya kwana malle?
Tace kwarai kuwa nace to waye ya bugenswaye
naji yana hira da mata a dakin shi? Tace uhun
ta juya tayi tafiyar ta ta barni nan a zaune tsoro
ya sake kamani ha tabbatar al'amarin dake
faruwa dani don haka babu abinda ya kamace
ni illa in koma gaban iyaye na, a yau dinnan ko
bani da kudin mata da sauri na tashi na dauki
akwatina na saci idon mutanen gidan na nufi

123

tasha na dauki shatar mota zuwa manbila har
cikin iugarmu na cewa direba to ai zaka shiga
ne ka dan huta sai gobe ka tafi ko? Yace a'a ni
yanzu zan juya nace to bari in shiga in miko ma
kudin ka yace a'a aini an riga an biyani nace wa
ya biya ka? Yace a'a w2ce irin tambaya ce
wannan nace to bari ina zuwa nayi maza na tafi
na kira yaya jauro don yazo ya tanbaye direban
motar mutumin dayake cewa va biya shi muna
dawowa muka ga babu shi habu dalilin shi, na
kalli yaya jauro cikin matsanancin tsoro da
fargaba nace mishi yaya jauro anan fa direban
motar ya tsaya yace ashe har ya ar nan wurin
ya bace daga tsaunukan nan da suke kewaye da
mu? Yaya jauro vace ke suengel nifa dama ban
wani ji motsin wata mota ba ganin ki kawai
nayi kin shigo da jakar ki.
Ina jin yaya jauro ya fadi haka na yanke
jiki na fadi a kasa na suma.

Masu karatu sai ayi mun hakuri abiyo ni
littafi na hudu don jin karslhen labarin ayi
hakuri kwarai don kuwa ban so jan labarin
haka ba, bai zai kammalau bane cikin littafi
na uku ba.

124

Na Gode. Taku
Hafsat Chindo Sodangi.

SADAKA GA MATA DAKE DA MAS ALA DA
MAZAJEN SU
Su yawaita karanta wannan ayar
dake cikin Suratul Yusuf (Alaihis -
Salam):
"Rabbi Kad Ataita Ni Minal Mulki
Wa Allamtani Min Ta'awilil Ahadis
Fadirus Samawati Wal Ardi Anta
Waliyyi Fidduniya Wal Akhira
Tawaffani Musliman Wa Alhikni
Bissalihin"
Ubangijin Mu Allahu Yasa Mu
doge Amin Sunma Amin. In Kika
Dimance karanta ta Allah Zai Baki
Zaman Iafiya Da Mijin Ki.

125

SAKO
Ga wadan da suka samu mas'alar
rashin fahintar wani abu cikin littafin
matn da kicin dinsu suna iya aiko da
tanbaya ta cikin wannan layin dana bayar
cikin wancan littafin. 07035586299,
Allah Ya taimake mu amin.

126
Chapter 16 · 0% Book details