← Book details Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 16

Sashe 15

Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

murmushi yace sengel kenan kin kara kyau kin
kara gwarjini kin waye kin zama matar birni
banyi kokari ba dana hango ki daga nesa na
gane ki? Rabon da in ganki fa tun kina amarya
saboda na gane mai gidan bai son zuwa na
gidan shi, a zuciyata nace babu damuwa tunda
dai nasan kina so na, nayi maza nace mishi
waya gaya maka haka? Ya sake wani
murmushin yace aiyukan ki suke nuna mun
rashin jaruntakar ki a kusa da ni shike kara
baiyanar mun da asirin zuciyar ki in daga ido
don in baiwa Mahmud amsa sai kawai ga sa id
a bayan shi yana tsaye fargaba da tscro suka a
kamani jikina ya sake daukan wani rawan ganin
yanda yanayi naya sauya gaba daya yasa
Mahmud yayi saurin juyawa don ganin abin da
ke faruwa yana murmushi kuwa bai motsa ba
daga yanda yake, hannayen shi duka biyu suna
cikin aljihun shi yace mishi barka dai.
Bansan yanda aka yi ba sai na tsinci
kaina dace mishi har ka dawo? Ya zubamun ido
Cikin natsuwa yace nayi sauri ko? nayi maza
nace mishi a'a don na gane kuskuren tanbayar
da nayi mishin, yaya in kin gama mu tafi ko?
nace to na wuce na barsu shi da Mahmud ban

114

san me suka tattauna ba.
Tun daga hanya na lura shan iska yake yi
nima sai na tsira muna isa gida kuwa naje na
gaya wa uinma dawowan mu na wuce dakina
na turo kofa ta na rufe har na hau gado na na
kwanta sai gashi yazo ya tsaya mun a bakin
kofar dakina dama kun shirya zaku hadu acan
ne? bakin ciki da takaicin tanbayar yasa na
amsa cewar eh, ya zubo mun ido cikin natsuwa
yace yayi kyau, haka din ba kuma laifin ki
bane, sakarci nane ya jawomun hakan in bah
aka ba ai na dade da zargin akwai wani abinda
ke gudana tsakanin ku amma na krsa daukan
mataki mai tsanani, saboda ina tsoron abinda
zai kawo batanci a tsakanina da ke nayi maza
nace me kake nufi yayan sahura da irin wadan
nan kalaman naka? Yace abinda kika gayamun
kin san kowanne dan adam yana da jarrabawar
shi a rayuwa, ai an jarrabe ni da son wacce bata
sona duk abubuwan da kike yi tayi mun na
nuna mun kiyaiya a zahiri na kasa hakura da
ken a kasa daukan mataki mai tsanani akan ki,
saboda zuciyata ta kasa jaruntakar yin hakan to
gashi yanzu gashiii... .. yana cikin maganar ya
soma haki da sauri da sauri saboda tsananin

115

bacin rai nayi maza na isa gare shi don in kai
mishi dauki tare da fadin bah aka bane yayan
sahura ina dora hannuna a jikin shi yayi maza
ya hankade ni kar ki sake kar ki sake yin
wànnan gangancin ki barni kawai ki kyale ni ki
fita hanya ta kar ki sake taba ni.
Tsoro ya kara kamani ganin yanda sa'id
ya fita cikin haiyacin shi cikin dan takaitaccen
lokaci na taso nazo kusa da shin a durkusa
yayan sahura bafa komai tsakani na da
Mahmud da sauri yace mun karki karamun
wani bakin cikin kar ki nemi ki mai da ni wani
mahaukaci sabo da rawai kinga duk abinda
kike yina kasayin komai bayan na fara zargin
wannan al'amarin bana kama wasikan Mahmud
da yawa a gidan nan sunanan kuma ina ajiye
dasu nama dauki sabon complimentry card din
shi a cikin falon nan na kuma san bani nazo da
shi ba, na zaro ido cikin matsananncin tsoro ban
taba sanin akwai irin wannan zargin a tsakani
na da shi ba, zargi a tsakanina da mijina,
wannan al'amari ya muna na Inna Lillahi Wa
Inna llaihir Raju'un' abinda kawai nake ta fadi
kenan cikin zuciyata.
Zama na da sa'id ya shiga wani hali na

116

wani irin matsanancin tsananin da ban taba
tsanmanin zama tsakanin mace da mijin ta
yakan kai wannan matsayin ba, na rasa inda
zansa raina inji dadi nayi kamar inje in kai
maganar wurin umma sai kuma nayi wani
tunani nace to ai watakila su dukan su sun dade
suna mun irin wannan zargin dana zauna nayi
tunani mai zurfi sai naga ni karshen wulakanci
da tozartawan da sa'id zai mun kenan, shi ne
nay a zauna dani yana zargi na akan ina auren
shi ina mu'amala da wani can daban to akan
me? Akan bukata ta ta zarce tashi ko kuma
akan zai bani wani abin duniya? Ina zaune da
sa'id a haka rannan sai aka wayi gari da safe
ban ji motsin shi ba har yamman tayi bangan
shi ba babu shi babu dalilin shi, hankali na yayi
matukar tashi saboda ko bama kula juna ni da
shi amma kuma muna jin motsin shiga da fitar
juna, na tashi na fito cikin dare na bude kofar
dake tsakanin na da umma don inje in tanbaye
ta ko ta san wani abu game da shi ina shiga
cikin gidan sai na fasa yin hakan, saboda yanda
na same su dukkan su suna barci, na tabbatar
idan yana cikin wani hali babu yanda za'ayi
gidan yayi shiru haka, na juya na dawo wuri na

117

nayi alwala nayi sallah sannan na hau gadona
na kwanta. Washegari da safe wurin malle na
samu labarin sa'id ya na Senegal sai da ya cika
sati biyu ya dawo ina jin kwarainiyar oyoyon
da akc mishi ban je ba, har ya gama zaman shi
wurin umma ban shiga ba, ya shigo wurin mu
ya nufi wurin shi ban kula shi ba, ina kwance a
dakina sai naji yana kwala nin kira na taso
nazo batare da na amsa ba.
Sau nawa mahmud yazo gidan nan da
bana nan ? ban tanka mishi ba na juya zan
koma dakina sai kawai naji ya figoni ya wurgar
dani Ian kujera nayi mummnunan faduwa, ai in
riga kinyi kuskure da kika zabe ni kika barshi
tun farko da dai kinyi hikima kin dauke shi kika
bar ni a wancan lokacin to da na nuna nuna
miki halacci na don bazan taba daga ido in kalle
ki da wani kallo ba face na matar aboki na to
amma tunda shi yaga zai keta haddin aure na ke
kuma kin yardan mishi yayi hakan to zan nuna
muku iyakar ku ke da shi, ina da hakuri da
tawakkali akan al amura na amma akan wannan
cin zarafin da kuka mun zan tsaya inga iyakar
abin da kuke nufi ya juya zai bar wurin sai ga
wata takarda a yashe a kasa ya sunkuya ya

118

dauke ta ya zuba mata ido zuwa can ya juyo
yace ga wasikar ki na karba ina duba wa, ga
abin da aka rubuta:
"Na gode kwarai da alkwarin da kika
samu cika mun jiya, nima kuwa nayi kokarin
cika nawa da nayi miki in har zaki samu sarari
tsakanin gode da jibi zan so mu sake haduwa
sai dai zan shawar ce ki, da ki kula kwarai don
kin san mutumnin in har yana gari to zaisa ido
kwarai a kanki, don haka in har kinhango fitan
naki zai zamo da mas ala to kar ki damu sai mu
jira sai ya sake yin wata tafiyar
Sai mun sake saduwa
Na Gode Da Kaunar Da Kike Nuna Mun.

Na saki takardar ta fadi a kasa na daga
ido na kalli sa id nace mishi yayan sahura na
gaji da wadannan al amuran da suke faruwa,
kafi kowa sanin inda kaje ka dauko ni, in akwai
tarbiya a gidan mu ma ka sani, in ma babu
kasani, baka da hujjar zargina da abubuwan da
kake zargina inyi mu'amala da wani na miji
bayan kai, akan wane dalili? Ban taba yin
sha'awar data zarce taka ba, kaima yaya na kare
da kai balle inje ina neman wani? Ya zubo ido

119

yana saurarona cikin natsuwa lokacin da wani
sako ya shigo cikin wayar shi ya duba sakon
sannan ya miko mun wayar na karba ina
dubawa daga bankin da yake mun ajiya ne aka
turo mishi ana baiyana mishi an sake sabunta
account din da wasu zunzurutun kudi da ban
tsaya kallon sub a itama wayar na sake ta a kasa
yace wannan ba alkawarin da akace an cika
miki bane? Nace shine bazan sake musu da kai
b akan wannan al amarin abu daya dai kawai da
zan sheda maka a yanzu shine ban bukatar
zama da kai tunda har zuciyar ka ta yarda ta
amince da cewar zan 1y aikata wadannan
abubuwan da kake zargina akan su in ka manta
bari in tuna maka kaje ka daukoni ne a gidan da
ake ganin dan halal baya zina kaje ka daukoni
ne a gidan da ake gudun abin kunya saboda
kawai an baka ni ka kawo ni inda bani da kowa
kazo kana wulakan ta ni to ka maidani cikin
dangina sub a zasu taba zargina da abinda kake
yiba, hankali yakai matuka wajen tashi in banda
kuka babu abin da nake yi, sa'id ya juya zai
koma dakin shi sai kawai na mika hannu na rike
rigar dake jikinshi, a sanyaye yace mun sake ni
maryam tun ranki bai baci ba, sannan daga yau

120
Chapter 15 · 0% Book details