← Book details Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 16

Sashe 14

Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kin e kike wani cika kina batsewa ana kallon
ki? Nace shi ne dalilin kiran nawa? Yace eh ko
yayi kadanne? Nace shi ne dalilin kiran nawa?
Yace eh ko nayi kadan ne ? nace a'a ba ka yi
amma kasan ina da abin yi in shike nan ina so
zan tafi yace to ba laifi jeki, na juya na fita na
koma wurin aiki na sai kawai na ganshi ya fito
da saurin shi yan matan da suke tayani aiki ya
kira yana rabawa kudin wata bayan banfi
kwana hudu da biyan su ba, da ya gama basu
sai yace kuje gida sai an neme ku ko, sukace to
suka kama hanyar fita ya leko dakin da nake
yace fito daga nan na hana wannan sana'ar
daga yau, sahura ta ruga da gudu ta shiga cikin
gida wurin su umma sai gasu sun shigo tare
meke faruwa ne sa'idu? Yaya zaka koran mata
ma'aikata ka hana ta sana'ar ta? Ya fito daga
ciki ta samu ta shiga ta ganni a tsaye ina kuka
kuzo nan ku biyoni muje can ni da shi muka
bita sahura kuwa ta tsaya tana kokarin ganin
munyi cake din da aka riga aka kwaba don kar
muyi asarar shi. Muna gaban umma sa'id yana
bayanin sana'ar ta ishe shi, baya anfanin taba
don taja mishi asara iri iri da bacin rai don
haka daga yau bai yarda ba, bai yarda a sake

107

yin wani abu don sayarwa ba, tunda ya lura ma
sana ar tawa tana kara bani damar raina shi,
umma ta juyo gare ni ban iya ce mata komai ba,
kuka kawai nake yi ta gaji tayi mana nasiha
tasallame mu muka tashi muka tafi bayan sa'id
ya dage kan cewar zan koma kan sana'atane
kawai bayan mun zauna mun ajiye sabbin
sharuda ni da shi.
Shikenan daga wannan lokacin na koma
irin zama na na farko bana komai daga wanka
sai yan aiyukan da basu taka kara sun karya ba,
sai ko kwanciya, a haka dai sa'id ya lallabani
muka shiry a a dalilin bani da wata hujja ta kin
daidaitawa da shi, abubuwan da suka faru
maganar sana ata kuwa yace shikam a yanzu ya
zama mishi wajibi ya kiyaye duk wani abinda
zai iya kawo mun mas'ala inna sake samun
wani cikin tunda shikam ya matsu yaga ya
samu kwanshi, to ni kaina haihuwar nake so
duk da nikam ina boyewa amma da za'a tona
cikin Zuciyata babu mamaki a tarar na fishi
matsuwa da ita, don kuwa gani nake tanfar
haihuwar itace kadai zata rage mun mas'alar da
nake ciki, gani kuma anan daga ni sai malle
kullum kuwa inna ta kan gaya mun cewar in

108

Allah Ya baki haihuwa kiyi tayi ki tara yaya da
yawa sai kiga kin fita cikin kewa.
A wannan lokacin sai muka yi matukar
zaman lafiya ni da sa'id lokaci mai tsawo babu
wani abun da ya sake faruwa a tsakanin mu
abinda bai taba faruwa ba nikamna saki jiki na
sosai ganin irin yanda yake tarairaya ta da ji
dani sai na zama akowane lokaci in banda kara
son shi babu abin da nake yi.
Rannan ya dawo daga wurin harkokin shi
da yamma naje na same shi a dakin shi nayi
mishi sannu da zuwa ya amsa na tanbaye shi
za'a kawo abinci yanzu ne? yace a'a ai, kin san
na karya kenan na fita nace eh yace yanzu dai
zo tukuna in miki bayanin fili na, nayi maza na
matsa kusa da shi na zauna yace to wannan
dana gaya miki na hanyar dan batta kudin shi
sunyi yawa don kin san na gaya miki babba ne
kwarai dari da dari wajen goma sha biyu ne
aciki ni kuma zan sone in sayi flin da zan iya
katangewa in gyara komai don in tura manbila
a debo mun shanuna in zuba in kuma bude
wurin kaji don haka zan bar wannan inje in
duba na can hanyar wudil in naga zan iya sai in
saye shi.

109

Nace to amma shi wannan din zaifi
dacewa da kiwo sosai, tunda shi yayi nesa da
garin nan, hanyar wudil aiya zama cikin gar
sannan nan din a yalwace kwarai yake ina
ganin da zaka yarda sai ka dauki kudin da suke
account di na ka hada kayi amfani da su tunda
inka hada ai zasu gama maka aikin yayi maza
yace a'a a'a, bar kudin ki kawai, na kalle shi
cikin natsuwa nace mishi akan me ? akan ni ba
abokiyar rufin asirin ka bane ? yace a'a ba haka
bane, nace to na sha ganin ka kana rancen kudi
wurin su yaya babba da yaya balaraba, wato
nice da ban? Yace ba haka bane, yayi mun
bayani mai tsawo sai dai ban gamsu ba ganin na
matsa da hakan sa' id ya amince da karbar kudi
na, amma a matsayin rance in ya samu zai
maido mun su, nace mishi to kwana uku bayan
nan ya dawo gida da rana ya kirani dakin shi
ina shiga na tarar ya juye tulin kudi akan gadon
shi dukan su takardun naira dubu dubu ne,nace
kai kai ina ka samo mana kudi haka? Ya
zubamun ido yana kallona yace wadannan duk
kudin kine seungel da kika yi ta wahala kina
neman su, kusan shekaru hudu baki taba
daukan ko kwandala ba, gashi kin bani su a

110

matsayin rance babu wanda ya sani, watakila
kuma kin taba jin labarin cin manar maza da
kuke cewa ko ince rashin alkwarin su na matan
su su tallaba musu lokacin da suke wani abu na
neman ci gaba in kuma bukatar su ta biya sai
suyiwa matan nasu tukuici da kishiya, bakya
tunanin nima zan iya yi miki haka? nace ban
sani ba, ni dai abinda na sani shine kawai alheri
nake nufi yace haka ne, to misali innayi miki
irin wannan din fa tunda nima miji ne ban kuma
banbanta da sauran maza masu yin hakan ba
yaya zakiyi? Nace Allah ba zai hanani yanda
zanyi ba, ya sake cewa hakane, 'n kara tunani in
gani ko zan karbi kudi na kawai a sayamun
wata kadara ko shiga na a matsayin rance, nace
mishi yayi amfani da su kawai.
Nan da nan aka sayi fili aka Katangeshi
aka gayara komai aka gama ni da umma da
tasi'u muka je ganin wurin umma, ta tara ce
mishi ai kuwa dah har kace zaka hakura da
wannan din, saboda kudin ka baza su kai ba
yace eh umma maryam ce ta bani kudin ta tace
in hada umma tace to Allah ya kara rufa asiri
yace amin.
Wata guda bayan nan tasi'u suka dawo

111

daga manbila, shanun da ardo ya baiwa sa'id
sukaje daukowa suka hado da nasu, ni ma ardo
ya aikomun da yanmatan shanu wadan da basu
taba haihuwa ba guda ashirin da bijimaye uku
da akuyoyi irin na manbila masu manyan
kunnuwa, suma guda goma da bunsurayen su
uku, yace a kawo mun inyi iri, shikenan sai aka
soma kiwo an riga an sanya kaji a wurin su, an
zuba leyas an zuba buroilas.
Tasi'u sa'id ya sanya a matsayin mai
kula da gonar ya kuma dibi ma'aikata su hudu
tare da masu gadin gonar suma su hudu, a haka
aka soma. Ranran ya dawo daga gonar da.
yanma hankalinshi a tashe yake yana gaya mun
wani yanayi da ya gani a jikin shanun ya kuma
kira likitan dabbobin da yake duba su ammaa
bayanin da yayi mishi shi bai gamsu da shi ba,
nace to ko zanje ne in duba in gani gobe in
Allah Ya kaimu? Yace yau wa maryam in kinyi
hakan ai kin taimaka.
Washegari da safe nayi shiri kwalliya
mai kyau nayi cikin wata doguwar riga har kasa
dinkin senegal na daura dankwali a kaina na
kuma yafa gyale na madaidaici na sanya
takalmi na lowshoe mai kyan gaske ga

112

waraiwarai da zobuna sun kama hannu na sai
daukan ido sukeyi nayiwa umma sallama muka
fita ni sa' id zuwa gonar nayi matukar jin dadin
ganin dabbobin gidan mu cikin murmushi da jin
dadi na shiga cikin su sa'id yana mun kashedin
harbi fa suke yin ace mishi ai sun sanni ba zasu
manta niba, na matsa jikin su ina duba su nace
mishi bafa wata mas'ala ban, canjin wuri ne
kawai da kuma ciwon da wasu sukayi a kofato
da za'a bani sabuwar reza da almakashi zan
gyara musu kofato da sauri, ya sa aka kawo
mun ina karba sai yace mun to bari inje nan
wurin da ake Fada mana abincin su ba bazan fi
minti taiatin ba, zan dawo sai in kaiki gida nace
ko awa daya ba laifi yace to sai na dawo nace to
Allah Ya bada sa'a.
Said yana barin wurin na shiga yin aiki
na har n agama ina kara dudduba su sai naji ina
shakkar kamshin wani turare da baimun kama
da na miji na ba, na juya maza na waiwaya don
inga waye mai wannan kamshin? Mahmud na
gani tsaye a bayana gabana yayi matukar
fadiwa don kuwa nayi ma rabon da in ganshi
tun zuwan da suka yi da sa'id nayi musu bari
sai ko yau, ya sakn mun wani lallausan

113
Chapter 14 · 0% Book details