← Book details Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 16

Sashe 12

Duk Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ya dan kalleni yace kar ki gayawa kowa,
nace haba yaya jauro ai yanzu nib a yarinya
karama bace, yanzu yace hakane seungel, jume
ne take damuna da fitina, gashi yanzu tace wai
ni din bani da lafiya bana haihuwa har ma ta
matsamun sai da muka je wurin wani mai
magani ya bamu magani yace in dinga sha ni
kadai wai abin a wuri na yake, ya sake dan
waiwaya don ya rada mun magana kuma mai
maganin yace wai shanu biyar za'a bashi nace
bazan iya ba, don ardo ba zai yarda ba, ita jume
tace wai za'a iya diban shanun shi ardo bai sani
ba, to kuma naga kamrr kafar shanu tayi cikin
duwatsu shin e nace ko har sun diba ne? ban
sani ba shi yasa rannan naje kasuwar kara don
in gani ko zanga shanun a can ban gani ba.
Na zubawa yaya jauro ido cikin
tausayawa nace kai yaya jauro kai kam baka
dace dasamun mata ta kirki ba, ina ganin
maganin abin kawai shi ne akara aurar maka
wata matar su zama su biyu watakila kadan
Samu sassauci, yaya jauro ya kama ihu yace kai
seungel wannan shawaran naki na banzane, ni
inacema zaki ce ne a mayar mun da kitso na

93

kawai dama jume ta koma gidan su amayer?
Maka da kitsonka yaya jauro? Ka koma
saurayifa kenan? A ina kaga ana yin haka
bayan ka riga ka tsufa kuma kace kana son ka
dawo saurayi, ai bazai yiyu ba, kai dai bari
zanyi tunanin abin da zamuyi akai yayi maza
yace amma kar kice zaki zage ta don tace inna
hadata dakewa wai zaki tafi ki barmu nace to
yaya jauro.
Ina hira tare da bodejo dadi ya kamata sai
faman murmushi take yi tace mu muna nan
muna jiye miki zama cikin bare ashe ke kina
can abinki Allah Ya hadaki da miji mai kirki,
na kalli bodejo kawai na taya ta murmushin
cikin zuciyata ji nake tanfar in dan fada mata
wani abu game da irin zaman da muke yi da
sa' id, amma na kasa fada mata, ji nake tanfar
zan huda ciki nane in yiwa kaina, su dai su
bodejo a yanzu babu wani wanda suke so fiye
da sa' id in an tanbaye su mutumin da yafi kowa
kirki a duniya yanzu zasu iya cewa sa'id ne, to
in gaya mata laifinshi wuri na to akan me? Nayi
maza na sake tsuke baki na nayi shiru muka ci
gaba da hirar mu mai dadi har na samu na sako

94

maganar dake damu na ta yaya jauro da matar
shi, inna tayi maza ta yamutsa ido tace kul!!
Kar ki sake kawomun maganar shin ace Allah
sarki inna in baki taimaki yaya jauro ba wa zai
taimake shi? Tace uh uh zai sa raini ya shiga
tsakanina dasu kan fitowar da yakeyi yana
kwana a waje dana mishi fada sai yaje ya
kwashe ya gaya mata haka da nayi mishi
maganar yaje yaga wata yarinya yar gidan su
takko innace zan rinka sa ido akan su raina ni
kawai zai sa ta rinka baci na sake lankwashewa
ina baiwa inna hakuri nace in kin yi niyyar
taimakon shi inna kinsan abin da zakiyi.
Satin mu guda a manbila sai ga sa'id da
malle sun iso maimakon sai munyi sati biyu da
yace, gaba daya hankalin mutanen gidan mu ya
koma kan malle saboda yanda ta canza musu
tayi matukar yin kyau ta girma ta zama 'yar
gaye kwalliyar English wears take yi, don shi
sa'id irin kayan da yake sai mata kenan, ga
kanta akowane lokaci bai rabo da kanannan
kitso ga ribbon masu kyan gaske.
Na samu sa'id a sabon dakin da ardo ya
gina don saukar shi nace yaya akayi kuma yau

95

na gan ku? Ni da na dauka sai sati mai zuwa
zaka zo ya kalleni cijkin natsuwa yace ai gidan
ba dadi in bakya cikin shi, basa hakuri, nayi
nace bari dai inzo muyi zaman bakuntar tare na
kalle shi kawai nayi murmushi cikin zuciyata
kuwa cewa nayi kamar da gaske, in ina nan
kaki yarda a zauna lafiya yanzu da na barma
gidan kabiyoni kana fadin gidan babu dadi.
Duk da sa'id baizo da shirin bukin
sumaye ba amma hidima sosai yayi ya kuma
kyaleni dai da aka gama bikin sarai na raka
sumaye gidan mijin ta har muka maida ita daga
yada sawun da tayi wanda tun daren farko tayi
shi sannan yayi mun maganar yaushe nake
ganin zamu tafi? Nace aiko gobe kace mu tafi
sai kawai mu daga, tun da an gama komai yace
to zanje in samu baffa zan gaya mishi ina so
zuwa jibi in Allah Ya Kaimu sai mu tafi, nace
mishi to ina shiga gida na gayawa maizube don
nasan itace zata shirya mun tsaraba.
Ina zauna tare da inna ta a cikin dakin ta
dambun naman da nazo musu da shi na samu
tanaci na bude jaka ta na debi kudi masu yawa
na bata ta karbesu tana kallonsu tace a wannan

96

jejin namu me zanyi da wadannan kudin in dai
ba shanu kike so in kara ba, nayi maza nace
mata a'a inna ina baki kudi ba shanu nake so ki
kara da suba, kashe su nake so kiyi ki rinka cin
dadi ta kalle ni tayi murmushi tace in rinka cin
irin wannan abin kenan da kika kawo mana?
Nasan inna gatse tayi mun don kuwa babu
abubuwan dana kawo musu ariga takaici ya
kama ni ina ma dai kusa dasu nake da kuwa na
jiyar da su dadi da irin girke-girken da na iya.
Rannan a dakin ardo na tare don hira,
kusan raba dare muka yi mu biyu, muna zaune
ardo ya kalle ni yace mun yaya dai seungel ke
da jauro shiru babu wani motsi? Allah dai Ya sa
mas' alar ba daga wurin ku take ba, bance mishi
komai ba sai da naji yayi shiru sai nace mishi
baffa baza ku taimaki yaya jauro ba? Ardo yayi
murmushi yace ai jauro bani a cikin al' amarin
shi kuma tun da bodejo ta zuba mishi ido kowa
ma zai gaji ya zuba mishi ido. Sannan ina so ki
gaya wa mijin ki yayi kokari ya dibi shanun shi
a wannan lokacin nace mishi to.
Sa'id da kanshi ya samu ardo yayi mishi
bayani kan shirin da yake yina zuwa diban

97

shanun nashi, sai dai yana bukatar ardo ya dan
kara hakuri kadan yace to Ubangiji ya nuna
mana lokacin yin hakan yace amin.
Tsarabar ruga sosai aka shirya mana nayi
sallama da yaya jauro cikin tausayawa na kawo
kudi masu yawa na bashi nace mishi ya kai
cikin yashi ya boye ya rinka diba kadan kadan
yana bata kar ya yarda ya bata lokaci daya yace
ai ba zaiyi haka ba.
Mun dawo gida da kwana uku nayi barin
ciki wata uku hankalin sa'id yayi matukar tashi
baran ma da likita ya bayar da dalilin barin
akan tafiya mai nisa da nayi da 'dan karamin
ciki ina kwance kan gadon asibiti amma bai
fasa fadanda yake yi ba, wannan ma ai
ganganci ne da rainin wayo, ai kin san kina da
shi kika kama hanya kika luluka wannan tafiyar
kikaje kina ta kaiwa da kawowa a jeji.
Umma tace to maryam kuwa inda tasan
da haka ai bana zaton zata yi wannan tafiya
tunda ita ma ai zata so ta ga kwanmta yaya
babba tace a'a umma infa yarinyar nan tayi laifi
ki rinka bari ana nuna mata kuskuren ta, hauka
kenan take yi in har zata dauki ciki wata har

98

uku a jikinta bata san da shi ba, haka fa
kwanakin baya akace mun wai tayi barin sati
shida sanadin barekatan da ta sha, shima
kuskure ne? bata fi kowa sanin irin wannan
abin a tunda ita ai "yar magori ce.
Umma ta mike tsaye tace mata bar
asibitin nan tunda ke baki iya kwantar da fitina
sai dai tayar da ita, wuce ki tafi ki bani wuri,
yaya babba ta wuce ta tafi tana fadin soyaiyar
da kike yiwa wannan yarinyar tana sawa kina
rufe idonki kan cutar sa idu da takeyi inma
hidimar da take yi kike dubawa ai tana wanke
kaifi.ne da ruwan jikin shi, tana fita umma ta
koma kan sa'id ta rufe shi da fada kai kam
abinda kake yi har kunya yake bani ni ban san
abinda yake bani in ban san abinda yarinyar
nan take maka ba da kowane lokaci kake fusace
da ita me take maka ne? Me take maka da yake
hanaka tausayin ta? A irin wahalar da maryamn
tayi yau ace wai bar kana iya yi mata tashin
hankali ai kuwa abin da ban mamaki yace
umma cuta ta takeyi tuni kuma na dade da sanin
tana nadamar aure na wannan bari-barin da
takeyi duk da gangan take zubar da cikin don

99
Chapter 12 · 0% Book details