← Book details Dingishin Kwado Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 14

Sashe 9

Dingishin Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gaskiya Baba Babba ya yi tunani kuma ya cika ɗanuwa na gari, gwara a raba a bawa kowa haƙƙinsa haka addini ya tanadar"
Ni dai har ya gama magana ya tashi, ban sake wani motsi ba me ya sa yake murna? Saboda na ce za a raba mana gado, a kullum al'amuran Baban Amrah mamaki yake ba ni, ba ya gyarawa kuskuransa sai ma ƙoƙarin sake wasu yake yi, ajiyar zuciya na sauke amma abin da ya yi ya tsaya mini cak a zuciyata sai dai ban iya faɗa wa kowa ba sai washegari da Maman Abdul ta zo, ban yi mata wata magana ba, saboda na
san ko na faɗa mata sharhi da magana kawai zan jawowa kaina ita da Abida har gobe ba sa iya boye adawarsu akan Baban Amrah shi yasa na yi shuru da bakina amma dai na ji daɗin zuwan ta mun yini tare muna hira kuma ta saka ni na saki jikina har na manta damuwata.
Tun daga lokacin da na yi ma Baban Amrah maganar rabon gado ya dame ni bini-bini sai ya tambaye ni wai ya ake ciki ne har yanzu ba a kiramu ba? Tun ina mamakinsa har na daina na gama fahimtarsa kuɗin kawai yake hange, tun da ranar ma muna karyawa a gaban yara yake ce mini." Kai gaskiya za ku sha kuɗi Balki, ko gidan gonar nan kaɗai ai sai ta yi miliyan dubu da doriya."
Kawai sai na saki baki ina kallonsa, au shi da man ya kwanta ne da gidan gona yana lissafin zan samu kuɗi ya sake komawa ya naɗe hannu ni kuma na sakin masa kuɗi ina masa hidima shi da ƴaƴansa da iyayensa, tun da na riga na sabar masa, a lokacin ban ba shi amsa ba sai da ya sake yi mini zancen kai tsaye na faɗa masa gaskiya.
"Gidan gonar da kake mgana ba ta Baba ƙarami ba ce shi kaɗai, duka dukiyar tare ne da na Baba Babba. Ko mu y'ayansu bamu san yadda dukiyar su take ba."
Tun daga nan na kashe masa baki amma duk da haka bai daina tambayata har yanzu Baba Babba bai kiramu ba?Ranar da daddare har mun kwanta ya sake yi mini mganar na harzuƙa na miƙe ina faɗin" Bai kiramu ba, don Allah Baban Amrah ka ƙyaleni da wannan maganar. Mu fa ba gado ba ne a gabanmu mutuwar mahaifinmu ta fi yi mana ɗaci, sannan lafiyar Yaya Sulaiman ta fi damunmu fiye da tunanin wani gado."
Ganin na buɗe masa wuta ina masifa sai ya yi ƙasa da murya yana faɗin" Sorry ni ma ai mutuwar tafi damuna amma ina so na ga an sauke ma Baba ƙarami nauyi, ai Allah ne ya ce a raba ko Bilkis? Kuma ke matata ce duk abin da ya shafe ki ai ya shafe ni."
Saboda haushinsa da ya kama ni ko magana ban yi masa ba na koma na kwanta na juya baya ya san ya yi laifi shi ya sa ya mirgino ta gefena yana kiran sunana, ta gefen kunina da dama yana yi mini raɗa, da ya ke ya iya kalamai sanyaya zuciya Idan ya so, tuni ya shawo kaina da azama muka tallafi juna sai dai kamar ko yaushe bai wani daɗe ba, ya matsa gefe ya fara barci ni kuma ya bar ni kwance cikin hawaye, na daɗe ina kallon shi ina tunanin wai haka sauran maza suke? Ba su damu da damuwar matansu ba sai kan su? Ban gane komai ba amma ba ni da yadda zan yi haka na ja jikina na shiga tiolet na yi wanka na tsarkake jikina na zo na sauya rigar barci na raɓe ta gefensa na kwanta ina tunanin makomar rayuwata, shike nan ni a haka zan ƙare, ba zan iya ɗorar da komai akan jin daɗin aure ba, a wajen ana mini kallon mace a cikin sahun matan da suka yi dacen samun gwarzon miji, kyakkwa Kuma marar hayaniys, ni kuma a cikin gida ni kaɗai na san inda ɗakina yake yi mini yoyo, na daɗe kafin barci ya kwashe ni cikin tunani da zullumi.
Tun da muka yi haka da Baban Amrah ya kiyaye ni da maganar rabon gado, nima jin Mami ba ta sake yi mini maganar ba, sai na cire abin a raina sai kwanaki biyu tsakani Ansari ya kira ni a waya yana faɗa mini wai Baba Babba shiru har yanzu bai ce komai ba? Takaici ya kama ni amma sanin da na yi Ansari da Mami bakinsu ɗaya
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Lokacin da Upper ɗin ta fito da kansa ya shirya ya zo gidana, na yi mamakin ganinsa amma sai murna ya danne mammakina, na yi ta rawar jiki da shi, na rasa ina zan saka shi na ji daɗi, ga shi yara ba sa gida baban Amra ma baya nan ya shiga cikin gari. Na share hawaye a ɓoye saboda shi kadai ya ke damuwa da lamarina a yanzu. Ya Hamida da gaske take ta yanke alak'a da ni, ba ta k:irana ko na k'ira ta sai ta ga dama take ɗauka. Su Saddiqa ba kasafai muke mgana da su ba, Duk ta zuge su. Ya Sulaiman ɗin ne kaɗai na ke gani na ji daɗi, lokacin da ya damƙa mini upper ɗina ta aiki bansan ya aka yi narumgume shi ina fashewa da kukan dan nake ta danne shi ba. Murna da tausayin kaina suka dabaibaye ni. Ina kuka ina faɗin" Na gode sosai Ya Sulaiman, na gode Ubangiji ya yiwa rayuwarka albarka, ya tsare ka ya sanya albarka a dukiyaka da ya'yanmu, Allah ya jiƙan iyayenmu."

Ya amsa da Amin kafin ya ce" Ba komai Bilkina ni dai fatana ki nutsu, ki yi haƙuri, ki rungumi mijinki da ƴaƴan ki, ki koyi juriya da yadda za ki iya tsayawa kanki ko da ba ki kowa a duniyar to ya zama kina da Allah kina da kanki!
Sai na ji maganganunsa masu kama da yana barin wasiyya ne.
Hankalina ya tashi kar ya zo shima mu rasa shi kamar yadda muka rasa Mami da Baba ƙarami.

"Yayw Sulaiman waɗanan mganganun fa? Ina za ka je?"
Na faɗa cikin damuwa da tashin hankali
Sai ya yi saurin ce wa" Ba komai Bilkina, wata yar tafiya zan yi amma kar ki tayar da hankalinki, idan da rabo za mu sake haɗuwa."
In jin ya ce haka na fara kuka ina faɗin" Na shiga uku Ya Sulaiman kai ma barinmu za ka yi! Don Allah kar ka tafi ka bar ni."
Hannayena ya riƙe cikin nasa kafin ya ce" Na ce ki kwantar da hankalinki ba zan daɗe ba, zan dawo, ke dai kawai ki koyi dauriya da jarumta, komai zai wuce, kina da ƴaƴa da mijin da wata rana za su iya zama garkuwa gare ki"

Duk yadda na so Ya Sulaiman ya faɗa mini k'udurinsa bai yi ba, ban dauka ganin k'arshe na yi masa idan a ce na san haka da ko za a mutu bazan bari ya bar gidan nan ba. Ganin yadda nake ta kuka yasa ya ɓata lokaci wajen lallashina har sai da ya ga hankalina ya kwanta.
Har abinci sai da na yi masa kuma ya ci mun d'ade muna hira yana ta mini nasihohi yana ce mini na kula da rayuwa, na kuma saka ido sosai akan yara. Ni kam na gama tsorata da jawabansa ya yi mini fatan alheri da fatan nasara sannan ya ce zai tafi.
Na ce ya ɗan jira su Farha sun kusa dawowa.
Ya kalleni kafin ya ce" Farha kaɗai sauran yaran fa?
Na yi shuru ban yi mgana ba.
Ya numfasa ya ce "Ki daina danganta Farha da ni Bilkina, d'aya take da su Amra a wajena, ba tawa bace ta kice tun kafin ta zo duniya kowa ya tabbatar da cewa Farha taki ce don kuwa na fi Abida cancantar na ba ki ita".
Na ba shi haƙuri ganin ransa ya ɓaci sai da na tabbatar da ya hakura sannan na sakoasa batun Abida tare da fatan ya dauke ta Su tafi inda zashi don na tabbatar hakane kadai zaisa hankalinsa ya nutsu. Ya girgiza kai ya ce "Bilkina ban saki Abida ba, amma matukar sai na nemi ta dawo gare ni to la shakka na haramtawa kaina ita. Bamu samu matsala da ita ba, ban mata komai ba, Baba da Yaya Asad suka zuba mata ido take yin yadda ta so, saboda kawai ba ni da Baba k'arami. Muryarsa ta karye. Ni kuwa kuka nake yi sosai don na gane ba k'aramin ciwo lamarin yake yi masa ba jarumta kawia yasa ciwo Bai kada slazzphi ba saboda tsananin damuwowin da suka yi masa k'awanya. Ya hadiye kukan dan ya so k'wace masa ya ce "Da ikon Allah sai na samu damar da zan tozarta Abida fiye da tozarcin nan da ta yi mini. Sai Allah ya ba ni dama na nunawa Asad iyakarsa. Saboda Yana da kud'i shiyasa ya shake Baba a maimakon ya tsaya ya daidaita komai a matsayinsa na babban wanmu"
Na yi shiru don ba ni da bakin magana don na lura Yaya Sulaiman'zfishinsa akan Yaya Asad fiye ma da Baba Babba akan batunsa da Abida. Na dinga ba shi hak'uri har ya d'an nutsu sannan muka yi sallama har harabar gidan na raka shi muka yi sallama cike da kewa.
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Ganin ya ruɗe yana ta wasu surutai yasa na s lalubo jarumta na yi ta masa nasihan da jan hankalin cewa tunda mutuwar Mami ta zame masa wa'azi ka da ya karaya, ya yi haƙuri ya cigaba da harkokinsa kowa iya kwanakinsa zai yi a duniya ya ɗauka ita Mami kwananta ne ya ƙare, da irin kalaman da na yi amfani kenan na lallashi Ansari ya bar kuka ya samu natsuwa.
Chapter 9 · 0% Book details