← Book details Dingishin Kwado Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 14

Sashe 2

Dingishin Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kadu kwarai da gaske da furucina. Ya ce Bilkisu ke nan. Dama an sha fada mini zan fuskanci haka, sai ga shi kuwa na fara ga ni. Ki fito ki ce kin gamsu da hudubar da take yawan fada miki na ce wa ki daina hada aljihunki da nawa saboda naki mai nauyi ne."
Karon farko da ya fadi hakan ban ji gabana ya fadi ba, ban kuma ji fargabar bai fahimce ni daidai ba. Na yi gajeran murmushi tare da ce wa "Ba dan nawa yafi nauyi ba ne. Watakila tana jiye mini tsoron faɗawa yanayin nan na k'ato da shan bugu kura da cinye wa."
Ya zuba mini ido sosai cikin son ya fahimci azancina.
Nima din na zuba masa dukkan nawa idanuwan cikin rashin tsoro ko zullumim kada ya yi fishi.
Ya ce "Kina nufin ina shanye romon wahalar ki ne Bilki?"
Jin ya fadi Bilki nasan yana cikin rashin sukuni.
Dan haka kaitsaye na ce "Kusan hakane domin kuwa kana yiwa wadanda basu cancanta ba hidima da wahalata. A tunanina baka da son zuciyar da zaka yi haka, sai dai da yake kai din dan Adam ne kuma jinsin namiji ba abin mamaki bane idan ka yi fiye da hakan."
Ya fusata ya mik'e ya dauko walet dinsa ya fito da ATM dina ya jefo mini. Ya ce ",Ga shi nan matukar ina shakar numfashi ba zan sake taba abin da yake na ki ba ne. Mafi munin kuskurena shine yadda da na yi imanin zan yi yadda nake so da abinki kaitsaye domin na dauka mun riga mun zama abu guda. A sadda nake da dama ba abin da ban miki ba mai asalin tsada ba garabiti irin wanda kike yi mini ba."
Na kada kai na ce "Tafi nono fari domin kuwa ban yi lalacewar da zaka yiwa budurwa hidima da abin da yake nawane ba alhalin ni tuni ka y'anta kanka da ga yi mini hidima kowacce iri tun shekaru masu nauyi da suka shud'e."
Ya fusata ya ce "Tabdi jam! Wato halittar mace da gori take da kuma manta alheri take!
Cikin nutsuwa na ce "Namiji kuma da son kai da zalunci yake ba.! Na fada a matukar zafafe.
Ganin na fara fusata sai ya sassauta fishin ya ce "Dan na yi aure a yanzu ai na yi miki adalci. Shekaru sha biyar zuwa sha shida dan zan k'ara aure sai ya zama zalunci?"
Na hadiye na ce ba zalunci bane. Amma a sanin da na yi maka baka da lafiyar da zaka iya gamsar da mace biyu. D'ayar ma ya ya ne? Sannan aljihunka ma bai cudi bayanka ba."
Nan da nan ya muzanta ya ce "A da duk hasashe kike yi da tsananta bin diddigi a kaina. A yau kuma ina mai tabbatar miki ina neman aure, wanda zai tabbata a kusa kusa".
Na kafe shi da kallo mai tsananin gaske murya babu amo na ce"Sai yanzu ne ya kamata na sani Sahal?"
Kaitsaye ya ce "Tunda ban bari sai bayan na yi auren kika ji ba, ai kuwa na mutuntata ki"
Gabana ya fadi sosai murya na rawa na ce "Tsakanin ka da Allah kana da lafiya da halin kara aure?"
Ya murmusa ya ce "Ba ki da hurumin wannan tambayar. Domin ba matsalar da ta shafe ki bace "
Murya babu amo na ce To ba zan lamince na cigaba da zama a gidana alhalin ka samu sukunin bani muhalli ban sani ba".
Ya girgiza kai ya yi kwafa. Can ya numfasa ya ce "Kamar d'azu na na yi ta jaddada miki cewar duk abin da kuke nufi da ni na shirya masa. Kin sani Abida ma ta hak'ura ta bar ni da dukkan nak'asun da take jigina mini, bare kuma yar karere irin Basma!
Na hassala na ce "A da ba Sahal, a lokacin ina sonka, ina ganin adalcinka".
Ya rausayar da kai ya ce "Shike nan lokaci zai fayyace komai."
Daga haka ya juya ya yi kwanciyarsa cikin nutsuwa.
Yayin da ni kuma hawaye ya balle mini. Na kasa daina kukan nawa duk da marar sauti nake yi. Irin na sharbe mai sanya nauyin kirji.
Ba'a dauki lokaci mai yawa ba, ya fara sakin munshari tabbacin yana cikin nutsuwar zuciya.
Na zura masa ido sosai. Ina ayyana al'amura masu yawa a kansa, sashin zuciyata har ce mini yake yi na dauki filon na danne masa kansa har sai ya daina numfashi. Nan da nan na zabura na mike ina ta'a'uziya tare da istigifari. Ina neman a tsare mini zuciyata da hankalina mummunan kishi da tunzurin zuciya mai sawa a halaka a kuma kafirta.
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Na doshi kofa na fice na doshi dakina. Na zauna a bakin gadon. Idona a bushe yayin da da zuciyata ta yi nauyi kwarai da gaske.
So nake na yi kuka ko zan samu sassaucin yadda nake jin kishi na babbako mini tare da bin dukkan ilahirin jikina yana soke ni.
A fili da kuma k'arfi nake ambaton Innalilahi wa inna ilaihir rajiun.!
Duk yadda na kunna a c da fanka basu yi tasirin da zufa ta daina yanko mini ba.
Na dinga safa da marwa a tsakiyar dakin.
Ina ta kokarin karfafawa kaina guiwa ta hanyar yin tunani na gaskiya tare da son na tursasa zuciyata k'aranta mata damuwa. A fili na ce "Bai kamata na bari k'aramin tashin hankali ya sake tarwatsa zaman lafiyar zuciyata ba.
Domin na yi amanna na shiga wanda ya wuce shi tsanani. Abin da ya faru a gidanmu ya fi k'arin aurensa firgici a gare ni. Ya kuma wuce, duk da ba'a samu daidaito ba har yanzu. Dan haka ba abin da zan ga ni na jarabawar rayuwa yafi wanccan al'amarin tashin hankali.
Tunda kuma har zuciyata bata buga ba a wanccan lokacin, to kuwa ba abin da zai sa na bari ta buga a yanzu.
Na fada bandaki na doro alwalla. Sallah nake yi ba tare da wata nutsuwa mai yawa ba. Amma a kalla na yi raka'a goma. Na kasa addu'ar komai. Kawai nasan ina ta ambaton Innalilahi wa inna ilaihir rajiun, Hasbinallahu wa niimal wakil.
Har tsakiyar dare ina zaune kan sallaya ina ta lazimin da ya zo bakina. Yi nake yi domin na samu sukunin zuciyata domin na kasa rokon Ubangiji komai. Sai goshin asuba barci ya fara fizgata, na sanya jarumta na tashi na sake alwalla dan na wartsake sosai, ban zauna ba sai da na sallaci asubahi.
Na samu saukin tunanin da ya yiwa kwakwalwata k'awanya. Amma gabadaya na sake tsunduma wajen son sanin inda zai ajiye amaryar da ya kudiri niyyar yi.
Zuciyata ta harba da tsananin gaske a dalilin na tuna muna daf da kammala gini. Tabbas fili nasa ne sai dai kuma kaso casa'in na kudad'en da aka yi ginin daga lalita ta suka fito, filayena guda muka siyar aka fara aikin ginin, bayan kudin sun kare, kullum cikin zuba kudade masu nauyi nake har muka kai da fenti da k'ananun aiyuuka ne suka yi saura.
Tirk'ashi na furta a fili tare da hasashen girman dabarwar da take gabana.
Da na ga kaina ya dau caci sosai sai kawai na hau hailala a fili.
Cikin ikon Allah sai nutsuwar zuciya ta same ni domin akan sallaya barci mai nauyi ya yi gaba da ni .
Na ji dad'in barcin nan domin rabon da na yi barci mai nauyi kuma cikin nutsuwa na mance. Ban farka ba sai wajen tara saura na safe. Na yi matuk'ar mamakin yadda ko motsin shige da fice yara ban ji ba. Tabbas na tabbatar sun shigo, Amrah da Alti ne zasu hanasu tashina. Na sa ni kuma ba k'aramin lallaba Farha aka yi kafin ta yarda ta tafi ba tare da ta gan ni ba.
Na yi salati na yunk'ura na fad'a bayi
Kaitsaye wanka na yi. Na fito na shirya cikin riga marar nauyi. A haka Alti ta turo kofa a hankali ta leko, ganina a tsaye har na yi wanka ya sanya ta shigo dakin gabadaya. Da kuzari tare da walwala ta ce "Kin tashi Mahmah? Na ji dadin barcin nan da kika samu. Da kyar dai yarki ta yarda ta tafi makaranta".
Na murmusa na ce "Farha duniya. Ni da kaina na tabbatar ba karamin wahalar da ku ya yi ba."
Cike da kulawa ta ce "Na miki kunun gyada. Na soya miki awara ne? Na dafa miki tun dare na saka a firij".
Na murmusa na ce "Sannu da kokari Alti. Allah ya taya ni gode miki".
Walwalar fuskarta ta karu. Tare da ce wa "Ameen Hajiya Mamah. Allah ya ninka miki walwalar zuciya da ta fuska."
Na amsa da fadin "ameen ameen, zan yi walaha yanzu, wajen goma saura sai ki fara soyawa".
"To "
Ta fada da azama sannan ta juya ta fice tana fadin "Alhamdulillah!.
Bayan na kammala karyawa da kaina na kwashe kayan na kai kicin. Na zauna a falo yayin da Alawiyya ta shiga dakina dan ta tsabtace. Gabadaya tamkar wanda aka cire mini Sahal a raina domin ko ganinsa ban ji ina son yi ba.
Na cigaba da zama a falo har ta kammala ta bazawa dakin daddan turaren air freshener.
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Jimawa kadan na koma dakin, akan kafet din na zauna ba akan gado ba. Sai dai na dauko filo guda daya daga kan gado.
Haka kawai nake na jin d'okin cigaba da hakaito rayuwarmu ta baya dan na sake nisanta kaina da tunanin Sahal da kudirinsa na karin aure wanda yake ganin zai iya muzanta ni matukar na ce zan yi adawa da hakan.
Na numfasa na janye filo na jingina da shi.
Na lumshe ido na sake kutsawa tiryan tiryan ina hakaito abubuwan da suke zaune daram a kwakwalawata da wanda bayyanasu zai zama darasi da gargadi.
Chapter 2 · 0% Book details