← Book details Dingishin Kwado Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 14

Sashe 13

Dingishin Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Uwa kuwa mai k'ima na d'auke ki Hajiya. Amma hakan ba zai saka na ci amanar aikina ba. Ko shi Baban Amra nake koyarwa ya kin yi karatu to ba zan ba shi makin da bai cancance shi ba. Don a lahira ni kad'ai zan kwashi zunubin son zuciyata "
Hajiya ta kasa magana Balki ta gama daure ta da maganganu da haka maganata da mutu mussaman da k'anin Sahal din ya ce wa Hajiya ba maganar suna auren miji d'aya wannan daban, bangaren malama da daliba daban idan ta yi abu mai kyau za ta ga ni.
Babu adalci a tilastawa Bilki ta ci amanar aikinta, da haka zance ya k'are ba ta san yadda ya k'are da mai kuka ba. Kan dole Hawwa ta gaji ta hakura tunda ba ta samu mafit ba wato tunda suna auren miji daya bari ta kwanta a gida ta k'i karatu, tana jiran ta wuce a banza, ba mutuncinta take ga ni ba, bare ta taimaka ta cicciba ta, tana ganin yadda take hada kai da kawayenta suna gulmarta suna zundenta.
Sai da ta zo making ta tarar duk yan group din nasu basa wani ja.

Cikin Hawwa ya fito ana gani sosai, tuni ta fara zuwa awo a bakin Alti take ji domin akwai wata rana da Sahal ya sakata ta rakata shi zai kaita sai kuma aka kira shi daga wajen aiki. Ba domin Alti ba, ba ma za ta san wattanin cikin ba ta ga dai ya girma tun da har ya fara turowa a riga sosai.

Ba ruwanta da harkar da ba a saka ta ba, shi yasa ta zauna lafiya in da ta sake godewa Allah warkewarta daga cutar damuwa yanzu ba ta shan magani, sai na hawan jini kawai domin ya kamata, shi ya sa take kiyayewa sannan tana shan mgani.
Ta riga ta kama kanta da sha'anin gidan gabadaya ba ta maida kai akan wasu abubuwan, shi yasa ko wani abu ya faru a gidan sai dai ta ji a bakin yara ko bakin Alawiyya to yau ma tana dawowa daga aiki ta yi yamma a cikin makaranta. Amrah ke faɗa mata Abban su ya siyo su dankali da doya bai kawo musu ba duk an haura da kayan zuwa saman Anty. Dama tana son ta samu damar da zata bata labarin abin da ta jiyo kwanakin baya dan haka duk Amra sai ta had'a ta faɗawa uwarta abin da ta ji Anty na faɗawa Dady, akan batun cefane da mota da kuma super wax.

Wato yanzu shine ya yo mata cefane irin nata da take ga ni tunda garar da aka kawota da ita ta k'are.

Lamarin ya daurewa Bilki kai, har yana da kudin siyan su doya da dankali da kayan miya daga Jos shi ne ita bai taɓa yi siyo mata ba! Tunda ya yi aure ya ce kowa ta yi girkinta ba zata iya tuna abin naira biyar da Baban Amrah ya siya musu na kayan amfanin gida ba. Amma tasan ya kawo mata k'aramin buhun shinkafa da katon din taliya da man gyada 5litr, wanda cikin garar Hawwa ne. Ba zata iya tuna me ya kawo mata ba bayan wannan.

Ba ta yadda da maganar Amrah ba sai da ta tambayi Alti itama ta bata tabbacin ta ga sadda yake hawa da su har da ledar kayan tea ta ga ni.
Shi yake siyawa amaryarsa ita kuma bangarenta idan ba zata siya ba sai dai su hakura da shan tea din, shi yasa ba ta jiransa sannan ba ta tambayarsa idan tana da kudi siyan abin da take so kawai take yi.

Abin ya dame ta amma ta kud'iri niyar sai ta yi masa magana, ranar ko ya shigo d'akinta zai kwana kamar yadda ya saba sai dare ya tsala ya yo shirin barcinsa daga can yake shigo mata.
Har ya kwanta ta ce ya tashi zasu yi magana ya fara faɗan sai da ta ga zai kwanta sannan za ta ce za ta yi masa magana.

Ta hakurkurtar da zuciyarta ta ce "maganar ba za ta daɗe ba sannan fa ya tashi ya zauna.
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: "Baban Amrah kana yin wasu abubuwa da ban gane musu a cikin gidan nan ba.'

A hassale ya ce" Kamar na me fa? "

"Kamar na yadda kake tafiyar da mu tsakanin ni da yaranka da amaryarka mu ba ka yi mana cefane, tunda ka yi aure sisi na dawainiyar abincin bangarena ba ka bani ba, duk ni ce nake yi, yanzu fa ba da ba ne Allah ya rufa maka asiri dama saboda ba ka da shi ne nake yi, na dauka yanzu za ka yi tunanin karbar ragamar da Ubangiji ya dora maka, amma sai na ga ba haka ba. Ita kana yi mata cefane ni kuma ko oho ni da yaran ka. Ai ya kama ta ka daidaita bisa adalci na yadda ko wanne magidanci yake yi. Kuma ni dai a sanina a farkon aurenmu kai adali ne ba abin da baka yi a gidanka na bajinta ma amma yanzu ka sauya mini gabadaya Baban Amrah!

Ta fada cikin taushin harshe ainun.
Kai tsaye ya ce" Kin taɓa ce mini baku da wani abu ne kika ga ban kawo ba Bilki?
Ya k'ura mata ido yana kallonta sosai.

"Ban gane ban taba fada maka ba. A matsayin ka na megida ai ya dace kasan duka hakkin da yake rataye a wuyanka. Ba bukatar a tunasar da kai."
Ta fada kaitsaye don ta fara harzuk'a.

Ya jinjina kai kafin ya ce" To ai ganin ba kya magana shi ya sanya na dauka kina da komai ne. Hawwa kuma tana fada mini abu kaza ya kusa k'arewa tun ma kafin ya k'are shi yasa kika ga ina siya mata, ke ma idan kin koyi yin hakan zan siya miki ai hakan ba matsala ba ne "

Baki bude Bilki take kallonsa kafin ta samu zarafin magana ya cigaba da fadin" Duk abubuwan da kike yi ke kika saka kan ki. Ni ban tab'a rokon ki alfarmar ki yi ba, saboda haka ba ki da ikon magana. Ko lokacin da ba ni da aiki, ke da kanki kika kika fara abubuwa kan ki tsaye ban roke ki ba, bayan na samu aiki na ga kin cigaba daga inda kika tsaya, kin ga ita ta tasan nine zan bata don bata da sana'ar da zata nuna mini bata buk'atar hidimata sannan ba ma'aikaciyar gwamnati ba ce. Ke kuwa fa?"

Kalamansa sun daki Bilki k'warai da gaske ta kasa magana saboda mamaki.

"So kar ki zargi kowa a kan wannan abun. Ki fara tuhumar kan ki."

Daga haka ya juya ya yi kwanciyarsa ya bar ta, tana binsa da kallon mamaki da tu'ajjibi.
Wato shi Sahal ya mayar da ita wata shashasha, kidahuma kuma sakarya, ba ta sani ba.
Sake kiran sunan shi ta yi yana daga kwancen ya katse ta da fadin" iya gaskiyata na fada miki. Ki bar ni na yi barci don Allah."

Hawaye suka kawo mata amma ba ta barsu sun zuba ba. Sai ta jinjina kai kafin ta ce" Shi ke nan na gode. Zan gyara a gaba."
"Better."
Ya amsa mata yana daga kwance, ranar kwana ta yi cikin takaici kuma tun daga ranar ta ce an yi an gama daidai da ruwan sha idan babu ba zata sake saka ko sisinta a cikin cefanen gidansa ba.

Ko sati ba a yi ba indomie ɗin yara da kwai tare da lemun da suke tafiya makaranta suka rage sauara na kwanaki biyu su k'are. Tunda ya ce ba a sanar da shi, shiyasa baya siya. Sai ta fad'a masa ranar da ya waye a wajenta da safe, yana karyawa.

"Ki ranta cikin kudinki, a siyo komai, zan ba ki anan gaba. Yanzu duka kudaden hannuna na bawa Hawwa zata fara rage siyayyar haihuwa tunda ana saka rai karshen next month ne haihuwar ".
Bilki ta saki baki tana kallonsa saboda yanzu Sahal ya daina bata mamaki al ajabi da tsoro yake bata.

"Ban gane ba?"

"Yadda dai kika ji?"

"Ban gane ka bata ta yi siyayyar kayan haihuwa ba! Haihuwar yau ne ko gobe? Saboda haka so kake yi mu zauna da yunwa saboda hidimar haihuwa?"
Bilki ta tambaye shi cikin karaya da lamari.

Daga faɗin haka ya juyo a fusace kamar zai kai mata mari.

"Dakata Bilki ni fa na gaji da hallayarki a cikin gidan nan tunda kika ga na yi auren nan bakincikinki da hassadarki suka taso a kaina. Na fada miki gaskiyata ko so kike yi na zauna har sai an yi haihuwar sannan zan tanadi abin da ya kamata! Idan kina da adalci ai kema haka nake yi miki, amma saboda son zuciya har kina da bakin magana"

Bilki ta saki baki da hanci amma ta kasa magana.
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: "Kin ce abu ya kare na ce ki ranta, ki siya zan baki shima duk bai yi miki ba, kina so ki tsiro da wata magana. Ina ce da ke kike siya? Me ya sa duk ba ki damu ba sai yanzu da aka kawo wata? Ki kiyaye ni kar ki kure ni na gaji da korafinki fa".

Yana gama faɗin haka ya wuce fauu ya sauka kasa, ya bar Balki da ciwon zuciya da kyar ta iya rarrafawa ta sauko ta koma dakinta sai da ta yi kuka. Idan ta ce ba ta gaji da Sahalu da gidansa ba ta yi karya.
Ta gaji tana bukatar natsuwar zuciya da na gangar jiki.
Amma matukar tana gidan nan to ba za ta samu haka ba.
Chapter 13 · 0% Book details