← Book details Dingishin Kwado Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 14

Sashe 14

Dingishin Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yini ta yi ranta a bace, ba ta da shiga makaranta kwance ta yini tana tunanin rayuwarta da ba komai cikinta sai bacin rai da takaici, ba ta dauka a daran Baban Amrah zai neme ta ba, tunda yadda suka rabu da safe sai ga shi ya zo yana rage mata murya.
Shi kan shi bayan fitarsa da safe yana tafe a mota sai ya ji duk bai kyauta ba, bai kamata ya fadawa Bilki maganganu masu zafi haka ba, shi yasa yana dawowa ya sauka a wajenta yana ta Haba haba da ita, yara ma har kallo ya yi da su sai jan su da hira yake yi.

Sai da daddare sun kwanta ya tausasa harshe yafara lallashintaa.
"Bili ni fa na dauka mun wuce wannan k'adamin a tsakaninmu. Na dauka ni da ke mun zama d'aya . Abin da yake tayar mini da hankali na kasa nutsuwa da ke tunda kika yi mini gori akan kudin da nake cira a asusunki na fara baya dake, ba ki fa da tabbacin budurwa na ke kashewa kudin, a lokacin ma Hajiya ce ba ta da lafiya, amma kika rufe ido kika yi mini gori, shiyasa nake jin zafinki gaskiya tare da tsoron ki. Bana son gori nan duniya Bili ba wata macen da zan aura da zata fiki, ke ce farkona fa, me ya sa zan manta da mafari? Hausawa suka ce da tsohuwar zuma ake magani. Ke din rufin asirince, mai sonace da gaske, ki yi hakuri ki huce kada ki ga dan muna ta samun sabani wai bana sonki ko an sha gabanki ne a zuciyata. Lah har abada ke ta daban ce, ina tuna yadda kika k'i manyan mutane da suke sonki kika zabe ni duk da k'uruciyata da kuma rashin abin yi na. Ki yi hakuri da ni dan Allah!

Tun Bilki na janyewa har ta saki jiki da zuciya ta karbi lallashinsa abin mamaki, tsawon lokaci suka yi suna raya daren a karo na farko bayan tsawon shekaru ta samu gamsuwar da ke bukata a wajensa shi ya sa ta tashi cikin farinciki da sukuni duk da shaidan sai ayyana mata yake yi albarkacin amarya ta samu don kuwa kafin wannan had'uwar bai taba yin jarumta akanta irin haka ba. Ke nan ya yi riveving kansa don ya dinga gamsar da amaryarsa.
Tasan haka ne amma ta kore wannan zaton ta dinga addu'a da fatan karshen matsalarta ne ta zo.

Da safe ya lallabe ta da daɗin bakinsa.
"Bili ki siya duk abin da babu, ki rika rubutawa ni nasan abin da nake yi. Ki k'ara hakuri da ni idan Hawwa ta haihu komai zai sauya. Tunda ba batun hidimar haihuwa."
Dama ai ta saba shi yasa bata damu ba ta ce masa to a ranar kuma ta shiga kasuwa ita da Alti ta siyo duk abin da ya kamata ba ta sake bin ta kan Baban Amrah ba tun da ko da yaushe hakuri yake bata akan cewa yana sane da abin da take yi. Sannan yanzu kam ba ya yarda ya wuce sati bai take ta ba tunda ya fahimci idan ya mata wannan harkar yana saurin dankwafe borinta.

Bayan an yi haka ya wuce sai kuma ya tsiro da wani abu. A da iya makaranta yake kai amarya da daukota. Yanzu kuma duk inda zata je sai ya bar komai ya kai ta sannan ya jirata ko ya koma ya daukota.

Yana kafa kafa da ita, kamar yar gwal Balki ta ga shiga hakkin ya yi yawa ita take fama da dawaniyar kai yara makaranta ko da ba da safe zata shiga makaranta ba. Haka nan kullum ita take kwasosu.
Sai ta ce masa ya dinga kai yara makaranta da safe, duk da tana da mota, fitar na safe ne matsalarta.
Amma Baban Amrah ya kafe ya tsare akan cewa ba shi da lokaci sai dai ita ta cigaba da kai su, Bilki kuwa ta ga abin na shi ba adalci. Yana da lokacin kai matarsa duk inda zata bayan makaranta amma ba shi da lokacin kai yaransa makaranta.
Itama ta kafe ta ce ba za ta dinga kai su ba.
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: "To Alawiyya ta dinga kai su a cikin napep."
Ya fad'a da ya ga sun yi kwanaki biyu basu je ba.

Bilki ta ce sai dai ka ba da kudin drop na wata amma Alawiyya ba za ta dinga wannan wahalar ba tunda da zata d'auke ta ban fad'a kai yara da daukosu na cikin ayyukanta ba"

Kai tsaye ya ce" Ki dauki mai Napep din ba ni da wannan halin."

Bak'inciki ya kama Bilki ta kasa magana kuma abin da ya fada ya tabbata ba ya kai su makaranta. Sai da ta ga fushin ba zai haifar mata da d'a mai ido kan yaranta ba ta sauko ta dawo tana kai su, ko tana cikin maka
Sai dai ya tabbatar dukanta ba k'aramin bala'i zai rakitowa kansa ba domin duk yadda ya mata gorin ahalinsu sun dare sun tarwatse bata yi arahar da zai saka hannunsa a jikinta da sunan duka ya kwashe kalau a hannun ahalin nata ba. Duk tak'amarsa kuwa.
Tana da yaya kwamishinan y'an sanda (Asad) wanda tun asali yasan bai so aka ba shi aurenta ba. Tana da Usman soja ne wanda shima matsayinsa ya fara nisa a gidan soji. Tana da tantiri irin Ansari kuma mai d'amara ne. Bayan haka ga Farouk da yake da kud'i a hannunsa ya tabbatar zai kashe ko nawane akan Bilki. Haka nan tana da darajarta ta daban kasancewarta tsohuwar ma'aikaciyar kungiyar lafiya ta duniya (W.H.O) Wanda suke had'akar ayyuka da hukumar kare hak'kin d'anadam(Human rights). Bayan haka Munira babbar Lauya ce da take aiki da kotun duniya reshen k'asar da take zaune, sannan jamiar kare hak'kin ya'ya mata ce. Ga uwar iya Abida. Ga Yaya Hamida mijinta babban alkali ne a kotun shari'ar musulunci. Ga Basma yar karare da zata yi zugar da dukkan ahalinsu Bilki zasu yi masa d'aurin talala.
Dan haka a fusace cikin isgili ya ce "Don iyayenki masu son zuciya ki je na sake ki saki biyu, ba don uku tashi guda sakin jahilai ne ba, da na cike miki, shasha mai bak'ar zuciya da bakin k'ishi. Ki je, idan kin samu adalin da ya fini wanda ba azzalumi ba, sannan ba mai gadon abin kunya ba sai ki aura Hakima Bilkisu Isa Funtua!

Yana gama fad'in haka ya fita ya bar mata falon.
Ita kam sai ta ji kanta na juya mata kalaman Sahal na mata kuwwa a kunnenta har ma kwakwalwarwarta bakidaya.

"Ki je dan iyayen ki na sake ki saki biyu"

Tirk'ashi!
Sahal ne ya sake ta? Zai iya sakinta ashe? Duk da ta fahimci ya gaji da ita amma ba ta taɓa tunanin gajiyar zata kaisu ga wannan gwadaben ba.
Bata taɓa hakaito idan zasu rabu zasu yi rabuwa irin haka ba. Ta dauka zai yi mata alkunya ya rabu da ita cikin mutunci da fakewa bayan k'addara.
Sai ga shi ya yi mata wani irin wulakantaccen saki tare da yi mata gori mai tayar da ciwon hawan jini. Sai dai ta godewa Allah da itama ta yi masa gori mai dasa ciwon zuciya. Idan baki yasan abin fad'a bai san abin mayarwa ba.

End of book 2
Muje ga book 3
Chapter 14 · 0% Book details