← Book details Dingishin Kwado Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 14

Sashe 4

Dingishin Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yammaci ina zaune a falo ya dawo, na tashi na karbi jakar hannunsa tare da yi masa barka da zuwa. Ya jani jikinsa yana shinshinar kamshina jikina tare da tab'a gashin kaina da ya sha gyara yake tufke cikin katon ribbon. Ya dan shafi mazaunan da suke tsole masa ido da tare da yin spanking dinsu. Maimakon na ji dadin hakan sai takaici ya nemi taso mini domin daga hakan shike nan. Ba komai zan samu da ya wuce hakan ba. Kaitsaye dakinsa muka wuce na adana masa jakar na ce "Wanka zaka fara ko abinci?" Ya ce "Bari na watsa ruwa tukun". Na juya tare da ce wa "To a fito lafiya". Na ja masa kofar na nufi kicin na shiga fito da abincin ina shirya masa a dining table. Tuni mun bar gidan da muka fara zama da muka dawo Kano. Gida mai kyau na bada labari ya kama haya, kuma na shekaru uku ma ya biya, bamu jima da tarewa ba. Shi kuma cikin kaddararsa ko maganar ya sayi gida ba ya yi, don na tabbatar zai iya siyan gida ko da ba irin wanda yake hari ba. Ko maganar ya sayi fili na yi masa sai ya ce "so yake ya samu kudin da zai saya a unguwa mai daraja. Tunda ya siya a katsina sannu a hankali ma zai siya a Kano. Ni kam jinsa nake yi, domin ban gamsu da dabararsa ba. Ni a tawa dabarar ya siya a koina mana, sannu a hankali idan ka sake samun wani kudin sai ya siyar ya hada ya sayi irin wanda yake so, domin na tabbatar samun irin wanda yake so a cikin manyan unguwannin birnin Kano zai yi masa wahalar gaske tashi guda. Ya fito sanye da jallabiya ruwan toka sai kamshin turaren() ke tashi. Cikin nutsuwa nake zuba masa. Na zauna yana ci yana yi mini hirar yadda ma'aikatarsu ta Nigerian airways kullum take fuskantar kalubalen rashin samun tallafin da ya dace daga gwamnatin tarayya. Na zuba masa ido na ce "Ni fa na dauka gwamnatin na bada kulawa ta mussaman ga ma'aikatar tunda harkar sufurice ta kasa da kasa " Ya ce "Hmm al'amarin dai sai kurum cin hanci da rashawa ta shiga ko ina. Ko muma da aka buda mana muke samu ai kinsan hanya ne tunda shugaban ma'aikatar gabadaya abokin Baban Mashi ne. Idan ba haka ba ai albashina bai isa komai ba. Duk wata ma'aikata ko kamfani mai muhimmaci gwamnatin nan sai ta yi shagulatin bangaro da shi har sai ya durkushe ko sai sun cefanarwa yan kasuwa sannan hankalinsu yake kwanciya." Na numfasa na ce "Baban Amra ya kamata ka yi himma ka mana gini ka kuma saka hannun jari a kamfononi domin tsaron ko ta kwana. Ranar da aka ce babu shugaban wajen fa?" Ya ce"Kin fini tsinkaye Billy! Zan fara dan gaskiya albashi kadai ba zai rike mutum ba". Yana kammalawa ya tafi dauko su Amrah tunda sai biyar da kwata suke tashi a dalilin har da islamiya a makarantar suke yi. A daren wannan ranar bana mantawa da kaina na ballo masa magani da ruwa ya karba ya sha bai yi musu ba. Sai dai kuma yana gama sha ya kwanta barci mai nauyi ya yi gaba da shi. Sai da asuba ya bukace ni, ya yi iya abin da zai yi, ya samu gamsuwa shike nan ya tsallake ya yi wankasa ya hau shirin tafiya ofis. Ya kalle ni ina kwance tamkar ruwa ya cinye ni domin ni gabadaya ban ma gane komai ba. Wani irin abu na mamayata tare da [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Yana kammalawa ya tafi dauko su Amrah tunda sai biyar da kwata suke tashi a dalilin har da islamiya a makarantar suke yi. A daren wannan ranar bana mantawa da kaina na ballo masa magani da ruwa ya karba ya sha bai yi musu ba. Sai dai kuma yana gama sha ya kwanta barci mai nauyi ya yi gaba da shi. Sai da asuba ya bukace ni, ya yi iya abin da zai yi, ya samu gamsuwa shike nan ya tsallake ya yi wankasa ya hau shirin tafiya ofis. Ya kalle ni ina kwance tamkar ruwa ya cinye ni domin ni gabadaya ban ma gane komai ba. Wani irin abu na mamayata tare da tambayar kaina shin ita mace bata da hakkine a wannan fagen? Komin bukatarta matukar namiji baya da muradin haduwar sai dai ta yi hakuri ta yi ta fama da ciwon zuciya da kukan cikin dare? Haka nan ita mace bata da hakkin idan an hadun a tabbatar an gamsar da ita? Namijine kadai yake da hakkin ya gamsu a cikin al'amarin?" Ba ni da mai warware mini wannan tambayoyin, amma kaina ya yi matukar daukar caji. Ya ce "Ba zaki tashi ki shirya yaran ba ne?" Cikin dabara na dauke hawayen idona. Cikin nauyin jiki na sauko na nufi bayi. A gurguje na yi wanka. Na fito na saka riga na fita kicin ganin har shida da rabi. Kaitsaye na dora doyar da na fere tun daren jiya. Kafin ta dahu na je na tashe su, na yi musu wanka. Na shirya Yaya. Yayin da Amrah take shiryawa da kanta. Na tafi kicin bayan na ce su yi sallah. Na fasa kwai na hau soyawa. Na zuba musu a lunch box dinsu yayin da na hada musu cornflakes suka sha. Shi kuma ganin zasu makara sai na shirya masa doyar da tea a basket, ya karya a ofis. Ya fito yana daura agogo ya ce "Da alamun idan na tsaya karyawa zamu yi latti da yawa. Ganin na fito masa da basket ya sanya ya yi murmushi ya matso kusa da ni ya karba ya jani jikinsa ya yi mini sumba a goshina da kumatuna. Ya ce "Allah ya yi miki albarka. Daga haka ya tisa yaran suka fice. Na bisu bakin kofar falon ina yi musu addu'ar dawowa lafiya. Ba wani kuzari na hau aikin gyara kicin, din, sannan na dawo falo na gyara. Yau kusan sati kenan da tafiyar yar aikina garinsu akan Babanta ba lafiya. Kafin karfe tara na gama komai na kintsa ko ina har dakin barci da na su Amrah. Sai da na yi wanka sannan na karya. Na yi wanka na shirya so nake na yi rubutu akan tasirin da garin k'irya take da shi da yadda ake sarrafata ta yiwa mata maganin dukkan naui'in cutar daji(kansa). Tunda kan kansar mama, ta mahaifa, ta fata da dukkan naui'in ciwon daji. Amma zuciyata babu sukunin yin rubutun domin matsalar da nake fuskanta kullum sake mikawa take yi, ba ni kuma da halin da zan yi korafi ko na tattauna da wani tunda a wanccan shekarun abin kunya ne mace ta bude baki ta yi irin wannan korafin sai idan tura ce ta kai bango. Kan dole na kwanta ina fatan na samu barci ko na huta da kunan rai. Na jima ban samu barcin ba, sai dai da ya sure ni ban farka ba sai wajen karfe uku. Da azama na duro daga kan gado bayan na kalli agogon bangon da ya fada mini karfe uku saura mintina takwas kacal. Da na idar da azahar lazimi na zarce da yi har sai da na sallaci la'asar. Sannan na shiga kicin dan yin abincin da zamu ci. Domin na riga da na saba girki daya nake yi. Kwanaki suka yi ta shudewa suna haifar da makwanni, da haka a samu kwanakin wata, watanni su haifar da shekaru. Rayuwar aurena da na yi a Kano itace rayuwa mafi dadi a gare ni, domin cikin nutsuwa na yi zaman. Miji na cikin wadata, shi kuma bai mini kwangen komai ba. Ba ruwansa da samun kudina, baya kuma taba sakar mini wahalar gidansa. Komai yi mana yake yi ni da yara a wadace, ko hidimar bikin dangina ne ya taso zai bani gudunmawa mai nauyi, shima kuma zai je ya bada nasa. Dan haka kowa yake mini kallon na taki sa'a. Don hatta Abida ta yi matukar mamakin yadda Sahal yake da halin girma. Gaskiya ba ni da matsalar zahiri da za'a iya nunawa. Domin ni kaina da ace yadda yake sauke nauyin ciyarwa da tufatarwa tare da kula da lafiya haka yake sauke hakkin auratayya da na ce ba ni da matsalar komai a aurena. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Amma da yake dukkan aure da irin nasa kalubalen ni cikas din nawa mai girmane, dan har rayawa nake yi inama a abinci nake da tasgado tunda ina da kudin da zan siya mana abinci. Kan dole na cire matsalar a raina tunda tana da nauyin a fayyaceta na mayar da hankalina kan abubuwan da nake samunsu. Na tara kudade sosai a asusna domin kwarai da gaske sana'ar bakery tana kawo mini kudi mussaman shekarun baya da sana'ar bata yi yawa irin yanzu ba. Mun yi murnar cikar aurenmu shekaru takwas (wedding anniversary). Kwanaki uku a tsakani muka tashi da wani tashin hankali na rushe kamfanin Nigerian airways aka kuma sallami ma'aikatan daga aiki babu garatutu bare a je ga batun fensho. Mun shiga rudani kwarai da gaske. Amma da yake yarda da kaddara wajibine a sharadin zama mumini. Muka hakurkurtar da zuciyarmu mu karbi wannan kaddara da hannu biyu. Na taka muhimmiyar tawa wajen kwntar masa da hankalinsa a wannan lokacin. Haka aka yi ta zuwa mana jaje tare da fatan Allah ya kawo masa wata mafitar mafi alheri. Bamu shiga matsalar a farko ba domin shi mutum ne mai tara kayan abinci da yawa sosai, sannan a duk sadda zan yi cefanen kayan su samosa, spring rolls, meat pie, pizza da sauransu, cefanen ne na sosai dan haka a ciki muke diba mu yi amfani a gida. Kudin hayar gidane ya nemi daga mana hankali domin mai tsadane sosai, amma dana runtse ido sai kawai na cire a asusuna na biya. Farinciki kan farinciki Sahal ya yi tare da yaba mini. A yanzu da yake zaman gida komai tare muke yi, sannan ya ninka soyayyarsa a gare ni tare da kulawa da yaranmu, zai kaisu makaranta, idan lokacin tashi ya yi zai je ya debo su. Baya wani fita ya jima sosai. A rubuce rubucen da nake yi a kafar
Chapter 4 · 0% Book details