← Book details Dingishin Kwado Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 14

Sashe 8

Dingishin Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin da ta fara faɗa mini ke nan ko gaisawa ma ba mu yi ba, farinciki ya cika ni na yi hamdala a fili da sarari, mun ɗan jima muna hira, tana tambayana ya su Mami da mutanen gida?
Na ce "kowa lafiya da godiyar Ubangiji, a baya dai muna cikin zullimi amma yanzu sai godiya. Ta tambayi yara, na ce su suna nan lafiya, mun ɗan jima muna hira ta ce mini za ta ɗan kwanta tun zuwan su ba ta samu barci ba.
Ranar yini na yi murna da farinciki na kira Basma na faɗa mata itama sai murnar farinciki take yi. Baban Amra ma da rawan jiki na tare shi da labarin har sai da ya ɗan rumgume ni yana faɗin" Alhamdulillah."
Nima na riƙe shi ina mai bayyana farincikina har fararen haƙorana suna bayyana tsabar murna.
Yara ranar kaf sun san Mahma na cikin farinciki saboda yadda na yini tare da su. Mutuwar Baba karami ta gigitamu k'warai da gaske mussaman da ba jinya ya yi ba. Sai kuam aka had'a mana da kila wa Kala na rayuwar Sulaiman dole dukan sai ya yi mana yawa, ace ba Baba ƙarami sannan ba Yaya Sulaiman, tabbas zukata za su raunana sai dai da ya ke Ubangiji ne mai yin abin da ya so, idan ma hakan ne ya so ya faru sai dai mu yi haƙuri ba mu isa mu ja da hukuncin Ubangijinmu ba. Labarin farfaɗowar Yaya Sulaiman ya zo mana da kwana ashirin da isar su ƙasar Germany. Yaya Faruku ne da kansa ya kira ni ya sanar da ni, bayan shi Abida ma ta sanar da Ni an kawo shi ɗakin hutu amma dai yana ta barci ne ba su samu shiga wajen nasa ba. amma tabbas ya dawo hayyacinsa. Na samu K'warin guiwar tafi ganin Mami tunda an samu cigaba sosai . Hakan ya sa na ce wa Baban Amra gobe ina son zuwa gida bai hana ni ba. Washegari na tattara yara muka zo Funtua kamar na sa ni gida cike da matansu Yaya Faruku da yara ana ta barka da arzikin da aka samu.
Baba Babba kuwa kofar gida ya fito aka tara masa almajirai ya riƙa rabon kuɗi sadaka domin godiya ga Ubangiji, mu kam mu a cikin gida kowa ka ga ni ya d'an samu k'warin jiki har Mami na ga ta d'an samu kuzari.
Yaya Asad daga can lagos ya nemi visa sai dai kawai da suka kira mu Video call suka haɗa mu da Yaya Sulaiman muka gan shi a can kwatsam ba tare da kowa ya san tafiyarsa ba. Allahu Akbar Allah mai gagara misali, sai ga Yaya Sulaimam zaune a kan gadon majinyata ga rigarsu ta asibitin kafafunsa da ya samu karaya an ɗora shi kansa da wani bandeji, amma yana zaune yana mgana kamar ba shi ne aka kai shi rai ƙwaƙwai ba, kowa ya gaishe shi kuma ya amsa sannan ya kira sunan kowa alamun dai ya dawo hayyacins sosai a Allah abin godiya.

Ni ina ganinsa sai kawai na ji kuka ya zo mini. Farha na jikina ta lafe. Abida ta leƙo da kanta tana kallona ina ta sharan ƙwalla, sai kawai ta kaɗa kai kafin ta ce" Sola ke wai me ya sa ba kya girma ne? Gaban ɗiyar ta ki, kike b'are baki kina kuka?
Ina jin ta ce haka sai na sake fashe wa da kuka don gabad'aya tausayinsa ya yi mini k'awanya Bai san mahaifinsa ya rasu ba.
Baba Babba ne ya kalle ni kafin ya ce" Bar kuka Maigado yi magana da ɗant'uwanki kin ji!
Na gyaɗa masa kai, kafin na yi magana Yaya Sulaiman ya murmusa kafin ya ce" Bilkkina ba ga ni kin ganni ba? Ki daina kuka kin j! Kar ki saka Farha ta fara gata nan idanuwanta ya kawo ruwa." Sai da ya faɗa na juya ina kallon Farha ta kusa kukan itama.
"Ya jikin ka Ya Sulaiman?
"Na ji sauƙi Bilkina. Alhamudulillah mun gode ma Allah"
Kallonsa kawai nake yi duk ya rame ya yi baƙi sai na tuna dr rasuwar Baba ƙarami kawai sai na sake fashewa da kuka kamae wata ƙaramar yarinya na ɗauka bai sani ba ashe ya sani sai ji na yi yana ce mini "Maigado ya ƙarin haƙurinmu!? Allah ya jiƙan Baba da gafara Allah ya kyautata makwancinsa"
Gabaɗaya muka amsa da Amin Yaya Usman ne na ji yana faɗa mini Yaya Asad ne ya sanar da shi bayan ya isa a jiya. Su Abida ba su samu wannan ƙarfin zuciyan sanar da shi rasuwar Baba ƙarami ba.
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Har wayar ta gama zagayawa hannun kowa ban daina kuka ba, Mami da Momi suna ƙwalla amma na farinciki ne Baba Babba faɗi yake yi" Allah na gode maka da ka karɓi ɗan'uwana, sannan ka bar mini ɗana Ubangiji na gode maka."
Muryarsa ta karye mutuwar Baba ƙarami ta sake dawo mana sabuwa dama tana jika, ba ta gama fita ba, kuma har abada ba za ta fita ba, ba za mu manta ba, don da yanzu ina tunano abubuwan da suka faru amma ina jin kamar a yau ne muka rasa Baba ƙarami. Mutuwa tana da d'açi, sannan mutuwa mai tonon asiri mutuwar Baba ƙarami ce ta yi sillar ta tarwatsewar gidanmu, kaina na saka a cikin tafukan hannayena duka biyu na sake fashe wa da kuka ina jin wani irin nauyi a samam k'irjin irin nauyin da na riƙa ji lokacin da gidanmu ya hirgitse, Ubangiji na ke fata da roƙo ya daidaita kan ahalina

Na cigaba da hakaito rayuwarmu washegari muka koma gidajenmu cikin sukuni da salama, sannan yanzu muna mgana da su sosai, barin ma Yaya Faruƙu yana yawan kirana saboda har gobe Yaya Faruƙu nawa ne, ina girmama karamcinsa a gare ni. Abida ma muna waya sosai sannan Yaya Sulaiman ma suna haɗa mu da shi, kuma jikinsa sai godiya yana ta samun sauƙi.
Ya Asad sati ɗaya ya yi ya juyo zuwa gida Nigeria. Abida da Yaya Faruƙu za su cigaba da zama tare da shi har sai an sallame shi, Abida ko an ce ta dawo ba za ta yarda ta dawo ba. Baba Babba ya ce a barta ta zauna ta samu ladan jinyar mijinta, ban ɗauka haka Abida ke son Yayana ba sai a wannan lokacin aikin ta ta ajiye ta ta tafi jinyar Yaya Sulaiman kuma da aknsa ya faɗa mini da jikinta da zuciyarta take wahala da shi, kusan ita ke yi masa komai sai na ji tausayinta ya kama ni, shi da man Yaya Faruƙu Ladi farm ne kuma ba matsala akwai masu kula da wajen shi ya sa ba shi da wata matsala.
Gabaɗayanmu mun koma bakin aikinmu tunda hankula sun kwanta ni kuma a gida na cigaba da karɓan aikin snacks sannan a bangaren aikina na W.H.O, mun cigaba da wayar waa da mata kai wajen kula da cikin da raino da kuma muhimmancin yin rigakafi ga yara bayan haihuwa.

Ba tare da shawara da kowa ba Baba Baaba ya fara tattara dukkan wata dukiyarsu shi da ɗan'uwansa idan a baya ba wanda ya san shiga da fitar dukiyarsu, yanzu mutuwa za ta yi sillar fallasar komai. Idan a baya dukiyarsu tana haɗe ne a waje ɗaya ba wanda yasan tsakaninsu yanzu dalilin mutuwa yasa dole komai ya bayyana, ya shiga har bangarenmu ya yi magana da Mami da Ansari tun da Yaya Sulaiman baya kusa.
Ya ce 'an fara tattara dukan abin da Baba ƙarami ya mutu ya bari idan an gama tattarawa lokacin su Yaya Sulaiman sun dawo za a zauna a raba gado domin a sauke masa nauyi, wannan maganar rabon gado, wannan gadon shine silar dambarwan da ta faru a gidanmu dambarwar da ta yi silar da na rasa Abida na rasa Ya Munnera.

Bansan da mganar ba Mami ta kira ni da kanta a waya tana faɗa mini abin da yake faruwa.
Sai na ji hawaye ya goce mini, yanzu shike nan mun rasa Baba ƙarami, har ga shi ana mganar rabon gado Allah sarki rayuwa Allah ya kyautata makwancinsa ranar yini na yi kamar marar lafiya. Baban Amrah yana can bangaren Hajiyarsu sai da ya shigo ne ya ganni zaune a falo na shiga zurfin tunani ban san ya shigo ba sai da na ji hannunsa a saman kafaɗata sannan na dawo hayyacina.

"Lafiyarki kuwa?

Ya faɗa yana kallona cikin kulawa, na sauke ajiyar zuciya idanuwana suka kawo ƙwallah, gidan da ma ya yi mini shuru yara sun tafi islamiya, Basma ce ta ce mini za ta shigo to ta kira ni ta ce ta fasa zuwa Baban Abdul ya yi baƙi sai dai zuwa gobe.
"Na sha faɗa miki ki daina zurfafawa kanki tunani. So kike na rasa ki na shiga uku?
Kalamansa na ƙarshe yasa sai da na yi dariya, kusa da ni ya zauna ya ɗan rumgumo ni da sigan lallashi yana ɗan buga bayana.

"Komai mai wuce wa ne, Allah ya jiƙan Baba,. Shi kuma Yaya Sulaiman da ikon Allah sun kusa dawowa"
Na gyaɗa masa kai cikin gamsuwa domin na yi lamo a jikinsa na kuma karɓi lallashinsa, ban san me yasa ba sai gani ina bashi labarin wayar mu da Mami, ina ƙoƙarin mai da hawayen da suka cika mini ƙwarmin idanuwana, amma ga mamakina sai da ya ɗago ni cikin nuna murnarsa kamar na ba shi labarin wani abin daɗi.
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: "Ma sha Allah."
Ya faɗa yana kallona, na yi kasaƙe ina kallon sa, faɗa masa fa na ke yi mutuwar mahaifina ta dawo mini sabuwa saboda an yi maganar rabon gado, amma yana kallona da farinciki a muryansa har ya bayyana a saman fuskarsa.
Chapter 8 · 0% Book details