Sashe 5
Dingishin Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
sadarwa ta Facebook ya ja hankalin mahukuntan hukumar lafiya ta duniya(W.H.O.) Suka gayyace ni ofishinsu, suka tattauna da ni, suka bukaci sanin matakin ilimina. Na tabbatar musu na yi karatuna na firamare har zuwa matakin digiri. Sannan na karanci ilimin abincin da ya dace da kowanne rikunin Dan Adam. Suka ce washagari na koma tare da dukkan takarduna. Na fito na tarar da shi a mota. Na shiga ya ja muka tafi. A hanya ya kalle ni ya ce "Ya ake ciki?" Da walwala na ce "Sun bukaci na kawo credentials dina gobe". Ya fadada murmushinsa ya ce "Alhamdulillah! Ina ji a jikina Ubangiji zai sake kawo mana dauki" Na taya shi murna tare da ce wa "Allah ya biya bakinka". Washagari tare muka fita da yara. Sai da muka fara ajiye su sannan muka wuce. Cikin sa'a kuwa bayan mun shafe awanni biyu na fito dauke da takardar daukata aiki na tsawon shekaru uku. Abin burgewa sau biyu zan fito a sati, sai na yi musu rubutun da zasu dinga dorawa shafinsu cikin harshen Hausa da turanci sau daya a sati. Ba karamin murna muka yi ba domin albashina mai tsoka ne matuka da gaske. Dan haka bamu wani shiga zullumin rashin aikinsa ba. Ba wani abin da ta canja mana. Sai dai shi tunda mai son ya yi alherine sai ya takura, duk da ban shata masa layi da komai nawa ba. Ko biyan kudin makarantar yara na shekara na biya musu dan haka komai lafiya lau. Watanni takwas da rashin aikin Sahal. Mun je hutu gida Funtua ni da yara zamu yi sati guda, domin na kwana biyu ban je ba. Na tarar da Abida da su Baba ana artabu domin kuwa daga Baba babba har Baba karami sun hade mata kai sosai akan ba yadda za'a yi su bari ta tafi uwa duniya babu aure da sunan zurfafa ilimi. Dama ace digirin farkone da sauki, amma yanzu tana da aikinta tunda likitace a babban asibitin Funtua tun shekarar da gabata take aikin. To matukar sun isa da ita aure suke so ta yi idan tana da auren ta tafi birnin Sin ma ba Ingila ba. Ba Abida ba, ni kaina mamakin yadda Baba babba ya shafawa idonsa toka ya yi nake yi, domin kuwa kowa yasan baya iya takure ta. Watakila kuma ya yi hakane don Baba karami ya kafe ba zata tafi uwa duniya babu aure alhalin tana da shekaru ashirin da bakwai tana shirin cika da takwas. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Cikin fishi sosai na tarar da ita, bata shiga shirgin kowa, kullum tana dakinta, ruwan shayi kawai take sha. Amma ganin Amrah yasa ta dan sauko take hira da ita. Yanayin da take ciki sai ya sanya ban ji dadin hutun ba. Domin tun filazal ita da Yaya Munira sune cikon farincikina a gidan, nafi shakuwa da su akan yayan mahaifina. Tun Mami na mini sababi har ta hakura ta kame bakinta mussaman da a yanzu duk cikin yaranta babu wanda yake gatantata Irina. Yaya Sulaiman ne yafi ni dama a cikinmu shi kuma ba'a kasar yake ba, yana Germany. Tunda ya kammala karatunsa ya zama likitan ido gwamnatin Kasar Germany ta rike shi na shekaru uku dan ya yi mata aiki. Amma ya dawo sati hudu da suka shude, dan haka zuwan nawa ma har da yi masa barka da zuwa. Dan da ya kammala wa'adin shekaru ukun sun so ya sake zama amma ya bijire tunda ya nemi aiki a nan Nigeria. Ya kuma samu da gwamnatin jihar Katsina. Yana cikin likitocin asibitin cikin gidan gwamnatin Katsina. Haka nan Yana da ofis a cikin babban asibitin Katsina. Dan haka idan zai mata aike kudi yake turo mata. Ni kuwa komai take so yi mata nake yi, haka bana raba ta da kayan ciye ciye kala kala, domin a kai, akai akai nake yin samosa da da meat pie na aiko mata ta saka a firij tunda a wanccan lokacin babu matsalar rashin wuta a Funtua. Na dauke mata gudunmawa, haka nan ina mata dinkuna sosai. Ina hadawa na yi musu da Momi amma dai na Mami ne sha kundum, dan haka na samu sassauci sosai a wajenta, ta daina tsananta mini akan sha'anina da su Abida, ta daina mini shagube, ta daina bagarar da lamarina. Tunda ya gamsu lamarinta shine gaba a wajena har mahaifina kuwa. Daren ranar da muka je muna dakinmu na sashen Mami. Na kalli Abida na ce "Yanzu Abida menene abin fishine har haka? Ki huce ko kuma ki fitar da mijin tunda idan har mijinki zai barki ai kuma ba sauran ace za'a hanaki yin abunda kike so". Ta ja k'aramin tsaki ta ce ",Ban samu wanda nake so ba. Ni dai kawai su Baba sun takaice ni. A wannan marrar wanne namijine zai yarda da ga yin aure na tsallake na tafi na bar shi? Su sun kasa fahimtar aure fa ba wajibi bane matukar mutum zai kame akan me za'a mini dabaibayi irin hakane?" A tausashe na ce "Suna son ke ma ki yi naki iyalin, aure ai sutura ne, rufin asirine ta hanyarsa kadai zuria take yaduwa" . Ta kaurara murya ta ce "Kun haifa mini, naku sun ishe ni". Na ce "To tunda kin samu a A.B.U din ki yi anan din mana" A takaice ta ce "Nan din ma sun ce sai na tsayar da miji sannan zan yi. Ni kam gaskiya an takure ni, ni fa jina nake yi dakila ce don kuwa yana wahalar gaske na ji sha'awa bare har na gundura da zamana haka. Menene a cikin aure ne ban da jidali, haka kawai ina cikin zamana na jefa kaina a garari. Ba dama kuma ka zo gida a saurare ka sai dai ace ka yi hakuri, suma hakurin suke yi. " Dariya ta so subuce mini wai tana zaton ita dakila ce. Amma na maze domin a halin da take ciki idan na yi kuskuren yi mata dariya zamu hau sama mu fado ne. Na cije na ce "Ke ba dakila ba ce Abida! Dan dai kin kulle zuciyarki ne akan rijalu amma da zarar kin samu wanda ya yiwa zuciyarki kutse na ban mamaki zaki tabbatar ke din ba haka kike ba" Ta zuba mini ido ta ce "Sannu Maigado masaniyar komai akan mace da namiji". Na tuntsire da dariya domin gabadaya a kufule take, kuma so take sai na gasgata ita bata cikin jerin mata masu sha'awa.