← Book details Dingishin Kwado Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 14

Sashe 12

Dingishin Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Domin ta fahimci ya fi ɗokin haihuwar daga bangaren amarya tun da yadda yake b'arin jiki kan cikin nan ko a lokacin da ta yi cikin Amrah ba ta ga ya yi wannan ba'rin jikin ba. A yanayin da ta ke ciki bata ma fatan ta sake haihuwa to ta ina ma ta ga mijin ballanta har ta sake samun ciki? Mutumin da yanzu sun fi wata biyu bai neme ta ba tun samuwar cikin matarsa, ranar kwanan ta ma yanzu ba ta ganewa domin a sati bai wuce sau biyu yake kwana a dakinta ba shima a tafe yake kwana haurawa sama yana duba yar gwal, asuba na yi idan ya fita ba ya sake dawowa. Gabadaya ta rasa ma ina tsarin gidan yake kawia tana cigaba da binsa da ido ne Amma akwai ranar kin dillanci. Yana ta karakaina a kanta, haka ƴan'uwansa ma kullun cikin zuwa gidan suke da sunan duba amarya. Haka nan itama Hawwan k'annenta biyu sun zo daga Kaduna sun fi sati sannan suka tafi, ita dai sai dai ta ga ana shiga ana fita. Wanda ya shigo wajenta su gaisa wanda bai neme ta ba, ta yi kamar bata san ma ya zo gidan ba cikin irin rayuwar da take ciki ke nan.
Shi kan shi maigidan tamkar wanda aka yi musu farraku abin kullum hauhawa yake yi, ta kuma tabbatar ba wani farraku kawai sabbin bita yake mata cikin littafin kitabur ra'asi. Dan haka bata jin zafi domin ƴan'uwansa sun nuna rashin kulawa a kanta. Ba ta ɗorawa kanta damuwarsu a zuciyarta ba. Ta tabbatar wulak'ancin Baban Amra yafi jan kaso mai yawa na ciwon damuwar da ya kamata fiye da kason damuwar abin da ya faru cikin ahalinta.
Tunda tun kafin ya yi aure yake nausa mata bak'in ciki, yanzu da ya yi aure tozarta ta yake yi ta hanyar fifita yarinyar da bata wuce ta zo a mai yi mata hidimar gida tana biyanta ba.

Ana cikin haka semister ta yi nisa har an yi gwaji, sai ga Sahal ya zo yana yi mata magana, akan darasin da ta ke daukar su Amarya. Wai ta yi musu gwajin(test )kuma ya ga ta bata karamin maki 6 a cikin 20 me take nufi da hakan?"

Ya fada yana wurga mata takardan gwajin a jikinta. Lokacin tana cikin ɗakinta tana duba wasu takardu ne na makaranta ya shigo yana yi mata wannan jawabin.

Ko ɗagowa ma ba ta yi ba, ta cigaba da duba takardun hannunta. Idan shi ba adali ba ne to kar ya yi tunanin kowa ma irin sa ne, wato tunda tana matarsa ta bata maki 20/20 saboda shi, lalle Sahal ba shi da kunya to ai bai tsinana mata komai na abin arziki ba tun bayan auransa ballatana yarinyar ta ci darajarsa.

"Magana fa na ke yi miki kin yi mini banza?"

Ya fada a fusace Bilki ba ta son hayaniya shi ya sa ta dakata da abin da take yi ta dago tana kallon sa.

"Akan me ka ke magana?
Ta tambaya cikin nuna kamar ba ta gane in da ya dosa, duk bai sa ya fahimci ba ta da lokacinsa ba sai ma ya sunkuya k'asa ya dauko takardar yana nuna mata.

"Kin kyauta ke nan abin da kika yi Bilkisu?"
"Me na yi Baban Amrah?
Itama ta tare shi da sauri.

"Au ba ma kin san laifin da kika yi ba ko?"

Ya fada cikin harzuƙa.

"Ban sani ba, idan na sani ai ba zan tsaya ina tambaya ba."

Ya mika mata takardan yana fadin" Duba ki ga ni."
Ta karba ta duba sannan ta kalle shi tana fadin" Wannan kamar darasina a ina ka samu?"
Ta fada har tana bayyana mamakinta.

Baki ya saki yana kallon Bilki tana nufin ba ta san ko takardar wace ce ba?

"Duba sunan?

"Hawwa Hamza!

Bilki ta karanta a bayyane sannan ta mayar da fuskarta gare shi ta ce
"Wace ce ita? "

Ta tambaya cikin mamakin. Sahal ya yi wani sororo, wuyansa ya lamgwabe kafin ya ce" Kina nufin ba ki ma san ta ba?
"Ban gano wace ce ba, kasan daliban nawa suna da yawa ba zan iya rik'e sunan kowa ba."

Ta fada tana mik'a masa takardar hannunta amma ya kasa karɓa saboda mamakinta.

Ajiye masa ta yi a gefen gado ta d'au takardunta ta cigaba da dubawa.

"Kina nufin ba ki san sunan matata ba Bilki? Amma dai ai kinsan kin fara daukarsu darasi?"
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: "Don Allah fa?"
To ban ma taɓa lura ba, kuma ita ta fada maka ina daukarsu? Idan na shiga ajin bana tsayawa tantancesu abin da nake yi basu darasi da tabbatar da sun fahimcin darasin da kyau. Bayan haka bana sanin komai akansu illah zakwakuran cikinsu, Wanda hazakarsu ta wuce gigiggiwarsu. Bana ji itama ta dauke ni malamarta mai daraja don ban tab'a ganinta a aji ko a makaranta ta yi mini gaisuwar da zan shaida ina koyar da ita ba"

Ta fada tana kallon sa.
Kafin ta sake ce wa" Ka fada mata ta mai da hankali gaskiya, ta rage rawar kai a tsakanin kawaye if not , ba zata kai labari ba."

Sahal ya kai k'ololuwar fusata wato da gangan Bilki ta yi wannan muguntar?

"Ke nan da gangan kika kayar da ita a gwajin ko?

"Allah ya tsare ni, abin da ta rubuta shi ta samu."

Bilki ta amsa masa, a ɗan zafafe domin ita kam ta gaji da wannan ihun da ya ke yi mata a saman kanta.

"Ko da ba ta ci ba ai darajata sai ki bata maki mai d'an dama Bili"

Ya fada yana wani rage murya har da fadin sunan da rabon da ya ambace ta da shi ta manta.
Ta kalle shi shekeke kafin ta ce" Ai ba na haka, duk inda na ke adalci na ke yi ba zalunci ba, bana k'arawa mutum hak'kin da ba na shi ba."
Sai jikinsa ya yi sanyi domin sai ya ji kamar shagube Bilki ta yi masa.

"To ki d'an k'ara mata ko zuwa goma ne ga ta can tana kuka."

Haushi ya kama Bilki ta mike ko magana ba ta yi masa ba ta shige tiolet ta bar shi nan da ya gaji ne da tsayuwa ya fice sai da ta ji fitarsa sannan ta fito amma ta kwana cikin mamakin Baban Amrah, da ba ya jin kunyar aikata duk abin da ya ga dama. Ban da k'arfin hali har ya zo ya same ta da wannan maganar? A a ba kuka take yi ba, ta yi na jini ma, yarinyar sam bata mayar da hankali wajen karatu kwakwalwarta ba ta ja, sannan kusan kullum sai ta ga tana nunawa mutane ita suna zundenta. Bata taɓa nuna ta gane ba bare ta tanka a bata rashin gaskiya. Shine kuma ta k'i yin karatu, sai kuma ita dan tana tsoron kada ace ta yiwa kishiyarta mugunta sai ta k'ara mata makin din da bata cancance shi ba? Wato ta turo shi ne ya yi mata dole shi kuma ba tunanin komai ya zo zai yi mata tilas. Ta dade tana mamakinsa har Basma sai da ta bawa labari da suka yi waya. Basma ta buga wani zagin Katsinawa sai da Balki ta kashe waya tana dariya. Ashe zance bai k'are ba da aka yi jarabawa ma sai da ya zo ya same ta akan ta bawa yarinya sakamako mai kyau ta ce to babu musu illah iyaka ta kud'iri ajiyar ba zata taimake ta ba, haka nan ba zata danneta ba. Ai kuwa sakamako na fitowa Hawwah ta samu F a darussa biyu ciki har da wanda Bilki take daukarsu wato pharmacology. Sannan sauran ta haye ne irin da k'yar din nan dan haka gabad'aya GDP dinta ya yi k'asa matuƙa da gaske.

Ta dinga kuka sosai tun a hanya yake rararrashinta tare da cewa yasan tana da kokari lififin cikine ya hanata hayewa dan haka ta kwantar da hankalinta yana tare da ita kuma zai yi kokari komai ya daidaita mata.
Cikin rishin kuka ta ce "Ban ci na wacce kake da iko da ita ba sai na wani ne za'a gyara mini? Ni Wallahi ka bude mata k'wanji ta gyara mini sakamakona, na gane bak'inciki take yi da ni tunda ta ga ina da ciki shike nan ta daura aniyar sai ta kai ni k'asa. Duk ajin ni da kawayena kawai ta kayar har wanda muka fi su k'ok'ari duk ta ciccibasu sun haye amma ban da ni da duk wanda nake mu'amala da su."
Suna dawowa gida kaitsaye wajen Bilki ya dira yana neman ba'asin kayar da Hawwa da ta yi.

Bilki da bata son jan maganar ta mik'e ta ce "abin da ta yi ne ta ga ni".
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Rikici har wajen Hajiya, itama wai Hajiya kamar ta manta da zaman da suka yi tana goyon bayan Sahal da matarsa.

"Haba Balki abu duk na gida, ai ko don darajar Sahal kya bari ta wuce tunda kina da damar yin haka"

Mamaki ya hana ta magana sai da Hajiya ta ce wai idan ta isa da ita to ta gyarawa abokiyar zamanta jarabawarta.

"Kin ga ciki ne da ita har ya fara girma damuwa kadan zai saka a samu matsala."

Bilki ta gyara zama tana kallon Hajiya ido cikin ido kafin ta ce" Ai ba ni da wannan ikon Hajiya na riga na bawa makaranta duka sakamakon jarabawar komai na hannunsu yanzu, ita ce za ta gyara carryover ɗin ta wata shekaran amma ni ba ni da wani taimakon da zan iya yi mata."

Hajiya ba kunya tafara fadin" Haka za ki ce Bilki? Ashe ba kamar uwa kika dauke ni ba?"
Chapter 12 · 0% Book details