Sashe 8
Deen House Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda ya shiga ɗakin yake kaiwa da komowa ya kira wayar Zainab tafi sau ɗari daga jiya zuwa yau bata ɗagawa abin ya fara girmewa tunaninsa zama yayi ya tsara mata test tana kwance tana zubar hawaye taji shigowar saƙon ta juya ta ɗauko wayar ta buɗe saƙon ganin number sa yasata jan tsaki ta sake lafewa a gadon zuciyarta na tafarfashi Zain kawai takeson gani gashi yafi ƙarfinta likitansa yace ba'a buƙatarta kusa dashi wannan abu nayi mata suya a zuciyarta inda tasan wata mafita da tabi don ganin muradinsu ya cika tunda itama Zain shine zaɓinta.
Ƙarar shigowar wani sakon ce tasata jan tsaki ta buɗe cikin ƙunar zuciya ta fara karanta sakon.
_“Nasani Ni me laifine a wajen ki ƙanwata saidai ina mai kwantar dakai domin baki hƙr ki karɓeni matsayin zaɓin da Allah yayi Miki ba wanda kika yiwa kanki ba Zainab kada ki wahalar dani inasonki da gaske wlh ba sha'awa bace kamar yanda kike tunani saidai inaji a raina kece zaki iya dani a yanzu da nasan kaina, Zainab ƙarfin feeling nawa ya zarce tunaninki kinsani tunda kin ɗan san wani abu game dani please ki bani dama don Allah ki manta da wani Zain"_
Wani mashin takaici taji ya caki zuciyarta batasan sanda ta ɗauki hannu ta rubuta masa _“Yafika cancanta azzalumi me son kansa"_ duk da ba kalma mai daɗi ta faɗa masa ba Saida yaji sanyi a zuciyarsa yaja numfashi tare da rungume wayar a ƙirjinsa yanajin ƙamshin turaren challenge da Zainab tafi amfani dashi yana ziyartar hancinsa har wani lumshe idanu yakeyi saboda shauƙin son kasancewa da ita.
Wannan dare baiyi bacci me daɗi ba Nafisa kishi ya hanata zuwa gareshi Zainab kuma dama ita yasan sai yayi aiki akanta sauƙinsa ɗaya dake tana zuwa b.u.k zai samu damar ganinta in yaso.
Washegari Zainab ta sake tashi jikinta yayi tsanani don ko tsakar gida bata fito ba wajajen ƙarfe 10:00am ya shigo gidan cikin Sa'a kuwa babu kowa sai Zainab da Bahijjah a ɗaki hakan ya bashi damar shiga ɗakin da sauri, ganin yasa Bahijjah miƙewa tana gaisheshi ta fice yaja ajiyar zuciya ya matsa ga Zainab dake kwance tana numfarfashi ya janye hijjab ɗin data ƙudundune da sauri ya birkitota yana cewa “Subhanallahi zazzaɓi me zafi haka Little meye kikasa a ranki haka?"
Baisan ta farka ba Saida yaji tana ƙoƙarin janyewa ya ƙara ƙanƙameta yace “Please ki bari meye yake damunki mijinki likita ne fah...." ,“Ubanka ke damunta Shamsu kaji ko nace harda uwarka duk suna damunta zaka tashi ka fice ko saina rotsa maka kai da muciya...." Tana maganar tana ƙarasa shigowa ɗakin ganin tabarya a hannunta baisa ya firgita ba saima ƙara riƙe Zainab daketa ƙoƙarin ƙwacewa da yayi yana shirin yin magana batare da yayi aune ba yaji ta kwantsama masa a ka aikuwa jini yayi tsartuwa ya fallatsa jikin Zainab wadda ta miƙe da sauri tace “Kay Umma meye haka...." Faɗuwarsa ce ta janyo Bahijjah dake shigowa ta saki ihu tace “shikenan Abba shigo kaga Umma ta kashe Ya Deen mukam mun shiga uku mun lalace...."
_Kuyi hƙr gwaji ne inason tantance yanayin ƙarfin idon ne🤗_
[9/20, 9:17 PM] AM OUM HAIRAN: *DH*
_Paid page_
_17-18_
Da gudu Abba ya ƙaraso ɗakin ya faɗi gaban Deen yana cewa “Ya subhanallah Amina garin yaya zaki bugeshi aka haka?" Itadai Umma saboda yanda take mugun jin haushin Deen juyawa tayi ta fice Abba ya kinkimesa ya fice cikin tashin hankali suka nufi asibitin da yake aiki ganin babban likitan nasu cikin critical condition yasa likitoci rufuwa akansa suka fara dubashi tare dayi masa bakin ƙoƙarin wajen ganin matsalar bata girmama ba.
Har dare wajen takwas sannan ya farka ya ɗauki hannunsa ya ɗora akansa jinsa a daure yasashi tuno da abinda ya haddasa masa ciwon ya cije leɓe zuciyarsa cike da ƙunci to shi meye aibinsa don ya cikawa zuciyarsa burinta?" Motsin da yaji yasashi buɗe idanunsa ganin Abba ne yasashi kafeshi da manyan idanunsa ya tako fuskarsa babu yabo babu fallasa yace “Ya jikin?" A sanyaye ya amsa da cewa “Da sauƙi Abba" shiru taci gaba da gudana can ya kawar da shirun da cewa “kuyi hƙr Abba ku daina fushi dani akan Zainab wlh zanbata rayuwa me inganci fiye da wacce kukeyi mata tunani a gurin ɗan'uwana.....
Zubansa Idanu Abba yayi yana dariyarsu ta manya ya juya yace “tunda ka samu bakin magana Ni zan tafi gida mu kwana lafiya" Abba bai jira cewarsa ba yayi ficewarsa" ya furzar da iska ya yunƙura ya miƙe jiri na dibansa ya fice daga ɗakin nurse ɗin da sauran ma'aikata sunata yi masa sannu baya iya amsawa saboda zuciyarsa ba daidai take ba, a napep yaje gidansa koda shigarsa baiga kowa a parlourn ba kai tsaye ya wucce ɗakinsa ya kwanta ransa dukka a jagule yarasa gaɓar laifinsa cikin abinda ya faru baiga abinda zaisa don ya auri Zainab iyayensa su juyansa baya ba.
Buɗe ƙofar da yaji yasashi zubawa ƙofar idanu ta shigo sanye da hijjab a jikinta idanunta akansa tana kallon uban naɗin bandejin dake kansa ta isa ta tsaya gabansa tace “Accident kayi ne?" Kawar dakai yayi yaci gaba da tunanin abinda zai fissheshi ta zauna kusa dashi tace “Ina amaryar taka?" Sake buɗe idanu yayi alamta ya rufe ta buɗe baki zatayi magana ya ɗaga mata hannu yace “Ya isheni haka ki barni da abinda ya dameni karki ƙaramin ciwon kai"
Dariya ta tuntsure da ita tace “Abin dariya ango mijin amarya wanne ciwon kai zan ƙara maka kaida kake da sabuwar amarya dal wanne ciwon kai ke gareka...." Tsaki yaja ya tashi ya shige bayi da gaske baya buƙatar surutu ita kuwa ficewa tayi daga ɗakin ta ɗauki wayarta ta kira Zainab dake kwance a parlour tana karɓar yanayi..
Kamar bazata ɗauka ba kawai dai ta daure ta ɗaga da sallamarta, amsawa Nafisa tayi da cewa “Amin karamar mayaudariya munafuka wato dama aikin da kikazo kenan ki auremin miji ko? Tabbas kin shammaceni ban ankara da hakan ba amma dai ki sani duk abinda kika gani kema ya zama shiryayye a gareki kuma Deen indai mijina ne dole ne ki barmin abina, Zainab bantaɓa tsanar wata halitta kamar yanda na tsaneki ba kuma banajin zan taɓa tsana Kinga kenan za'a buɗe sabon shafi Ni nice matar gida ke kuma kamar yanda kika bar gidannan to ki rubuta ki aje kinbar gidannan ne har abada domin bazaki shigesa da sunan mata ba.
Duk da ba kowacce kalma Zainab ke ganewa ba sosai kalmomin sun taɓi zuciyarta tayi murmushin yaƙe tace “Allah sarki kiyi hƙr Aunty Nafisa bantaɓa hasaso hakan zata faru ba ko a mafarki kuma banyi zaton faruwar ta ba kazalika banzo gidanki don mijinki ba sai don taimakonki mijinki baikai ba baya da nagartar da zanyi munafurci don mallakarsa, da wannan nake ƙara baki hƙr da shawarar ki ƙarawa mijinki tsaro"
Kashe wayar tayi Bahijjah dake kallonta tace “Wannan matar da baƙin kishi take ita an faɗa mata son mijin nata akeyi?" Murmushi tayi tace “Haka take tunani har alwashi takeci bonono wlh Bahijjah bantaɓa son Ya Deen ba hassali ma ya dasamin ƙinsa da ganin baƙinsa a raina" rausayar dakai Bahijjah tayi tace “Zaku daidaita akwai dacewa fah a lamarin" tsaki tayi ta juya tayi kwanciyarta tana ganin kiran nasa da saƙonninsa taƙi ɗagawa.
Kwanaki wajen goma Zain yayi a asibiti suka dawo gidan badon ransa ya daina ƙunci ba duk yanda Zainab taso ya bata dama yaƙi bata haushinta yakeji da ganin duhunta gani yake yi kamar itace ta bawa Deen damar zuwa a ɗaura masu aure shine takeson raina masa hankali bayan ta yaudareshi.
Tayi kukan zucci tayi na fili akan wannan wofintarwa da masoyinta kuma amininta yakeyi mata a daidai lokacin ne kuma suka koma makaranta wannan komawa ba ƙaramin daɗi tayiwa Deen ba tunda ya rasa damar ganin Zainab kwata² ko jinta ko gidan yaje baya samun ganinta tana ɗaki kuma umma ta kasa ta tsare, matuƙa yakeson kasancewa da matarsa amma ya rasa damar hakan daga Umma har Abba babu wani wanda yake sauraronsa shikam Zain gaba ce me ƙarfi ta shiga tsakaninsu ko kallo baya samu daga gareshi ana haka Abba ya gama shiryawa Zain barin kasar domin ƙaro karatu duk don dai ya samu ya wanke masa zuciya shirye-shiryen tafiyarsa sun kankama Zainab duk ta damu babban burinta koda bazai sake sauraronta ba ya bata dama ɗaya ta wanke kanta a gurinsa amma abin ya faskara a wannan yanayin ya ɗaga zuwa Birnin London don ƙaro karatunsa ran Zainab a jagule washegari da taji labarin tafiyarsa ta tafi makaranta.
Tunda taje bata iya tsinana uwar komai ba sun samu Interval kowa ya fice amma banda ita data zuba uban tagumi taketa tsiyayar hawaye bataji shigowarsa ba saiji tayi an sanya handkerchief ana share mata hawayen ta sauke numfashi tare da aje idanunta akansa shima idanunsa cikin nata yaja ajiyar zuciya ya kama hannunta ya miƙar da ita ta turje tare da rushewa da kuka ya jata da ƙarfi ya cilla ta a motar ya rufe ya zagaya ya shiga zuciyarsa a zafafe ya fizgi motar da ƙarfi ya fice.
Tariga ta fara tsikewa da tsoronsa ta shiryawa duk abinda zaizo mata dashi taci alwashin hana masa jin daɗi indai da itane amma me? A yau ta kasa hassala masa komai har sukaje wata unguwa me kyau da tsari yayi Horn jikin wani gida aka buɗe masa get ya shiga yayi parking ya fita ya zaga ya buɗe mata ya kamota ta fito yajata babu musu har cikin parlourn ya mayar da ƙofar ya rufe tare da tsayawa jikin ƙofar ya zubanta idanu itanma shi take kallo da idanunta daketa zubar hawaye.
Paid book 300 ne VIP 600 PC 1k ki turo katin MTN ta WhatsApp number na 09013718241 ko ki biya ta wannan acct ɗin 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank
[9/21, 9:07 PM] AM OUM HAIRAN: *DH*
_Paid page_
_19-20_