Sashe 7
Deen House Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tashin hankali wanda baasa masa rana, jiri ne ya ɗebi Zain duhu ya mamaye gurbin hasken da yake gani a idanunsa yayi ƙasa luuuu cikin yanayi na ficewar hayyaci abinda ya janyo dukkansu sukayo kansa da mugun gudu Abba na jijjigashi Umma na sallallami Zainab kuwa da Bahijjah banda kuka da kiran sunansa babu wani abu da sukeyi.
Ganin babu alamar tashi a tare dashi yasa Abba fita waje ya gyara parking motarsa yazo suka cicciɓeshi suka sanyashi a mota sai asibiti, da azama likitan ya fara dubashi ya daɗe yana dubashi kafin ya ɗago ya dubi Abba yace “Meye yaja masa wannan bugawar zuciya na lokaci ɗaya?" Shidai Abba ya kasa magana sai girgiza kai kawai da yakeyi, haka sukaci gaba da kulawa dashi can babban likitan ya ɗago yace “Akwai yuwuwar ya samu sauƙi amma dole ya kasance idan wani abu yakeso kodai abashi abin ko kuma a nesanta shi da abin"
Da yanayin damuwa Abba ya girgiza kai lamarin ya cakar masa da kai baisan wani abu daya dace yayi ba a yanzu dole sai ya samu nutsuwa.
A ɓangaren Zainabu kuwa tunda wannan baƙin labarin a cewar ta yazo mata take aikin kuka wannan wacce irin kama karya ce a duniya bata taɓajin mutum mara hangen gaba da adalci kamar Ya Deen ba ta faɗa masa bata sonsa ba shine zaɓinta ba maimakon ya ƙyaleta shine yaje ya bi hanyoyin munafurci shima Mal Tsalha saboda lissafinsa bai dire ba ya yarda ya ɗaura masa aure da ita to waima shi meye nacinsa da ƙulafucinsa akanta ne? A hankali takejin ninkin tsanarsa na ƙaruwa a zuciyarta tunda take bata taɓaji da ganin mutum me son kansa kamar Ya Deen ba Shikenan yanzu ya rusa musu tsarinsu ita da masoyinta? Shikenan yanzu Ya Zain yafi ƙarfinta.......
Sake rushewa tayi da kuka tana nadamar zuwanta duniya a mara saa mara rabon farin ciki, da gaske ta sarewa farin ciki cikin rayuwarta domin Ya Zain shine takejin zatayi farin ciki tare dashi itakam da Abba zai taimaketa da ya tursasa Ya Deen ya sawwaƙe mata auren nan na masifa.
Wannan sune kalolin tunane²n Zainab wadda ta gama sarewa da tsammanin farin ciki a rayuwarta ba itaba hatta umma wannan al'amari ya tsumata tama kasa furta ko kalma ɗaya me sunan samun sauƙi ranta yakai ƙololuwar ɓaci da wannan tantirancin rashin albarka da DEEN ya aikatawa marainiyar Allah tabbas zata nuna masa kuskurensa domin baitaɓa fusata zuciyatta irin hakan ba.
To shima Abba matuƙa ya ɗauki zafi da DEEN tunanin irin matakin da zai ɗauka akansa kawai yakeyi da wannan damuwar duk suka yini babu me wata walwala ga Zain a kwance a asibiti cikin halin jinya, wannan yini babu wani wanda zai ɗorar da daɗinsa jiran zuwan Deen gidan kawai sukeyi, har dare bai leƙosu ba harma daga ƙarshe suka rufe gidansu.
Ko a daren da sukaje suka kwanta Zainab banda aikin kuka babu abinda take yi kukan daya sanya mata wani ciwon kai me masifar zafi daya haifar mata da saukar zazzaɓi, Bahijjah banda aikin rarrashinta babu abinda take yi amma kamar tana zugata sabuwar tsanar Deen na ratsa sassan jikinta ranta na ayya mata abubuwa da yawa.
Wajajen ƙarfe goma wayarta ta fara neman agaji Bahijjah ta dauko ganin number Ya Deen yasata kallon Zainab daketa jan ajiyar zuciya tace “Yaya Deen ne ke kiranki Zeey" wani uban dogon tsaki taja batare da tace komai ba, kiran nasa yana katsewa wani na shigowa Bahijjah tace “Ki ɗauka kiji meye zai faɗa miki" banza tayi mata dama wayar ta ishe ta ta karɓa ta dannata a airplane mode tayi jifa da ita Bahijjah dake zaune ta dubeta da sauri a fili tace “Lallai kin ɗauka da zafi Zainab Ni a haukana sai nake ganin kamar ki zubar da makaman yaƙinki ki karɓi ƙaddararki a yanda tazo miki Ni banga abin ƙi a Ya Deen ba inma kyau ne ai yafi Ya Zain kuma kin riga kinsan halin Ya Deen babu wani abu da zai rushe wannan aure sai ikon Allah.
Har Bahijjah ta gama surutunta babu kalma ɗaya da Zainab ta tofa saima bargo da taja ta lumshe Idanunta irin abubuwan da suke faruwa tsakaninta da Deen suna mata yawo tana matse hawaye haka baccin wahala ya ɗauketa zuciyarta cike da tunanin halin da abin ƙaunarta Zain yake ciki.
Washegari ma bai zo gidan ba sai yamma daya taso daga aiki yana tunanin irin masifar da zaije ya tarar agidan gashi fir Zeey taki ɗaga wayarsa da ita ya fara haɗuwa a tsakar gidan tana amai ya tsaya a kanta cike da faɗuwar gaba ganin ramar dake tattare da ita a iya jiya da yau kaɗai dabai ganta ba, taji shigowarsa kuma taji ƙamshin turarensa amma ko ɗagowa batayi ba ta miƙe jikinta a mace ta juya da niyyar tafiya tabar masa gurin taji hannunta cikin nasa ta tsaya cak idanunta a ƙasa wani malolon baƙin ciki ya turnuƙe mata zuciya daya haddasa ma idanunta cikowa da ruwa lkcn da ya Matso jikinta yace “meye ya saki rama da amai?" Ɗagowa tayi tayi masa kallon daya sanyashi sakinta daidai lokacin da Umma ke fitowa a falo ganinsa yasata ɗaure fuska ya rusuna a ladabce yace “Barka da yini Umma ya gidan?"
Harara ta watsa masa ta nufi kitchen ta zubo shinkafarta da miyar ƙwai da haɗin salat ɗinta ta koma parlourn, murmushi yayi dama yasan za'ayi haka ransa na raya masa yabi Zainab daki yaga halin da take ciki wata zuciyar ta haneshi ya nufi parlourn ganin Abba a zaune yasashi sallama tare da shafa kai Abba ya amsa tare da cewa “Aa Shamsuddeen dama kana gari" sake sosa kansa yayi yasan magana Abba ya fada masa yace “Wlh Abba na shiga busy ne jiya yau kuma na tashi da wani aikin gaggawa" murmushi Abba yayi yace “Hakane to ya aikin ince dai wanda aka fyeɗe ɗin ya tashi" yanda Abba keyi masa magana kamar ba komai ya bashi damar sakin jikinsa suka fara tattaunawa can ya shafa kai yace “Dama Abba inason idan zai yiwu a sanya ranar da za'ayi biki da abubuwan da ya kamata ayi mata game da lefe da sauran abubuwa in yaso sai abani list"
Zubansa idanu Abba yayi kamar bai fahimci komai ba yace “Wacce Zainab ɗin fah?" Sunkuyar dakai yayi yace “Kakale" murmushi Abba yayi yace “Au toto hakanne ai dake kasan Zaharaddeen ɗin bai samu aiki ba so nake na buɗe masa shago a kasuwa inyaso sai ayi maganar auren koda yake kaima kace wani abu za'ayi yanda kace...." A sanyaye Deen ya ɗago yace “Abba nayi tunanin Mal Tsalha ya kiraka jiya yayi maka bayanin yanda abubuwa suka juya wlh Abba nafi Zain buƙatar Zainab nafisa cancantar mallakarta shiyasa da naga kun kasa fahimtata naje na sameshi shi ya fahimci abinda naso ku fahimta harma yabani damar bada sadaki aka ɗaura aure na da ita"
_Alhmdllh ina gdy masoya da addu'a ido yayi sauƙi sosai sai gdyr Allah kuma na gode da uzurin da kukayimin musamman ƴan paid group._
[9/18, 8:08 PM] AM OUM HAIRAN: *DH*
_Paid page_
_15-16_
Murmushi Abba yayi yace “Toh aishe haka akayi ai bamu da masaniyar komai tirƙashi yanzu kuma gashi bakaine zaɓinmu kuma raayinmu sannan gwaninmu akan Zainab ba itama kuma ba kaine zaɓinta ba, ya kenan za'ayi?" Tunda Deen yaga yanayin da Abba yake magana dashi gumi ya soma karyo masa tabbas ya shiga uku har tara ma domin babu wata alama dake nuna Abba zai fahimceshi ɗagowa yayi yakai dubansa ga Umma dake zaune tana juya remote a hannunta yace.
“Umma...." Ɗaga masa hannu tayi Idanunta akan TV tace “Karka sani a lamarin da ban isa ba kayi yanda kakeso Shamsuddeen kaima Allah zai maka yadda ya dace gadai Zainab can kwance a ɗaki dalilinka ga kuma Zaharaddeen can a asibiti shima duk saboda kai"
Cikin kaɗuwa yace “What Umma wanne asibitin?" Kallonsa tayi ta kawar dakai tare da miƙewa tabar gurin ya jima zaune zuciyarsa na kai kawo sannan ya miƙe a saluɓe yace “Shikenan Abba bari naje na duba Zainab sainaje na gano Zaharaddeen ɗin" har yakai bakin ƙofa ya tsinkayo Muryar Abba yana cewa karka shiga ɗakin yaran nan sannan shima Zaharaddeen ɗin ka share ba sai kaje ba zaiji sauƙi" cak ya tsaya gabansa na faɗuwa da gaske su Abba sukeyi rausayar dakai yayi ya fice jikinsa a mace.
Yaji kamar zai fita yaji bazai iyaba ya koma ya buɗe ɗakin har yasa ƙafarsa ya jiyo Muryar Umma na cewa “karka shiga dakin nan ka ficemin a gidannan kafin ka fusata zuciyata"
Baiyi mata musu ba bare gardama ya fice a gidan ya jima zaune a mota daƙyar yaja motar ya nufi gidansa, yayi parking ya fito ya nufi cikin gidan baitar da kowa a parlourn ba hakan ya bashi damar nufar ɗakinsa yakai step ɗin ƙarshe Muryar Nafisa ta katseshi da cewa.
“Dama kai nake jira Deen ashe haka ne abin yake kaima duk sunanku ɗaya da sauran maza Deen Ni ka munafurta ashe dama daka kawomin Zainab ka kawota ne a matsayin kishiyata? Ka cutar dani kuma zaka tabbatar da ka cutar dani bashi kaci wlh, bazan hanaka Zainab ba amma fah ka jira zuwan da zowar" murmushi yayi ya juyo ya dubeta yace “Karki ɗaga hankalinki kisawa kanki wani ciwo Nafisa banyi Miki alƙawarin zan zauna dake ke ɗaya ba"
Bata bashi amsa ba ya banko ɗakinsa ta cije leɓe tare da yarfa hannu tace “Mu zuba mugani wlh kowa yayimin sai nayi masa"