← Book details Deen House Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 25

Sashe 14

Deen House Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai yamma likis sannan suka tafi gida suna shiga gida kiransa ya shigo abin ya zame mata baƙo tadai taushi zuciya ta ɗaga suka gaisa kamar babu komi har yana tambayarta jikinta da bbynsa tayi masa shiru yayi murmushi yace “Kullum inason kiranki ayyuka sunmin yawa na gaji da zaman ƙasar nan cikin satin nan nake saka ran dawowa mu raini unborn ɗinmu tare" itadai ƙala ta kasa cewa dashi har ya gama zantukansa ya kashe wayar itama ta aje tata tun daga wannan rana Saida suka sake shafe wata biyu basuyi magana ba ranar wata Litinin tana parlour tana shan guaver Bahijjah nayi mata tsifa sukaji an murɗa handle ɗin Bahijjah ke tambayar waye? Bai bata amsa ba ya shigo ya Zainab ta mike da sauri cike da mamaki shima kallonta ya rinƙayi ta rame sosai sai hanci da idanun kawai yaja fasali ya zauna ya dubi Bahijjah yace “Wannan daga jinya ta tashi ne?" Da mugun mamaki Bahijjah tace “Au dama baka sani ba?" Kallonta yayi yace “Bansan batada lfy ba" cikin mamaki Bahijjah tace “nikuwa na zaci Abba ya sanar dakai Zainab nada ciki gashi har yayi kwari ma laulayin yayi sauki" shafa sumarsa yayi yace “au hakane fa na manta wlh sannu ya jikin" ƙululun baƙin ciki ne ya hana Zainab amsawa saima barin gurin da tayi ya rinƙa kiranta tayi masa banza ta shige ɗakinta.

_Bayan Hutu da wannan littafi ya tafi sakamakon ƙaruwa dana samu ta Bby girl Aishatu (Weedat) ayau 10/10/2022 Alhmdllh mun dawo bakin aiki, Shima littafin BAWA NA insha Allahu gobe zamu ɗora da post nasa sannan inama duk wanda yakirani yayimin Barka da arziƙin dana samu na kyautar Nana Aisha da ubangiji ya bani dama masu text kai harma waɗanda basu samu damar yin ko ɗaya ba fatan alkhairi._

_Saƙo daga_
_OUM HAIRAN & AFFAN AND WEEDAD_

Paid book 300 ne VIP 600 PC 1k ki turo katin MTN ta WhatsApp number na 09013718241 ko ki biya ta wannan acct ɗin 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank
[10/12, 7:45 PM] AM OUM HAIRAN: *DEEN HOUSE*

*Bonus page*

Daga yau 16 ga watan Rabi'ul Auwal zuwa 19 ga watan farashin wannan littafi ya sauka daga 300 ya koma 200 VIP daga 600 ya koma 400 PC daga 1k ya koma 600 ku hanzarta ku biya kafin wannan damar ta wucce, ga me son biya zai tura ta wannan acct ɗin 0255526235 Fauziyya Tasiu ko 3184512451 First bank ko katin MTN ta WhatsApp number na 09013718241 Ƴan Niger katin Airtel.

Bai wani damu da shigarta ɗakin ba ya miƙe yace “ga wannan in ta fito ki bata zan ɗan fita" rusunawa tayi ta karɓa ya fice daga gidan itama ta fara shirye-shiryen barin gidan amma ta sanyawa yayan nasu ayar tambaya ace ka tafi kabar mace wata huɗu ka dawo ba wani doki ba lallashi bare shauƙin ƙauna?
Saida ta gama shirinta tsaf sannan ta shiga ɗakin cike da mamaki Bahijjah tace "Au wai dama ba bacci kikayi ba?" Lumshe idsnunta tayi tana ƙoƙarin mayar da hawayenta tace “Banyi bacci ba ina Yaya Deen ne Bahijjah?" A tausaye don tabbas ko wacece ma dole abinda yayi mata ya daki zuciyarta, Bahijjah tace “Ya fita wai zaije ya dawo yama bada kaya yace inkin fito na baki kafin ya dawo to ni na shirya tunda Allah ya nufesa da waiwayowa zan tafi inda aka aroni"
Tashi zaune Zainab tayi tace “tafiya kuma Bahijjah don Allah kiyi zamanki ina ganinki kina ɗauke min kewa" zaro idanu Bahijjah tayi tace “Wannsn boss ɗin mijin naki bazan iya rayuwa s inuwarsa ba kedai da Allah ya ɗorawa Ni Kinga tafiyata" juyawa tayi ta nufi ƙofa Zainab na kiranta amma tayi mata banza saboda tasani indai ta kulata saita kashe mata jiki ta hanata tafiya.

Bataji daɗin tafiyar Bahijjah ba saidai babu mafita hakanan ta tashi ta gyara gidan ta sanya masa turare ko ina ya ɗauki ƙamshi sannan ta koma kitchen ta ɗora abinci batabar kitchen ɗin ba Saida ta gama komai ta jera a dinning ta sake wanka ta zauna a parlour tana jiran shigowarsa amma shiru har ta fara jin yunwa ta miƙe ta zuba abincinta tana turawa taji shigowarsa ta kuwa sauke ajiyar zuciya ta zubawa ƙofa idanu ya buɗe ya shigo tare da sallama ta amsa masa ya nufeta zuciyarsa na bugawa da ƙarfi ya zauna a dinning ɗin tayi ƙasa da murya cikin girmamawa tace “Barka da shigowa" ajiyar zuciya yayi ya ɗora kansa saman dinning ɗin ya rage injin idanunsa zuwa ƙanana yace.
Ina Bahijjah?" “Ta tafi" ta faɗa batare data ɗago ta dubeshi ba, Sake mayar da hankalinsa yayi ga kallonta taja flat ta haɗa masa abinci ta tura masa gabansa tace “Bismillah" murmushi yayi sarai yasan bata jure kallo shiyasa ya kafeta da ido yasan dole zata magantu da haka ya samu damar cewa “Zainab kiyi hƙr na daɗe ban dawo ba ko?" Sai yanzu ta samu damar kallonsa yanayin kallon da take masa ne ya tabbatar masa tana riƙe dashi a zuciyarta dole ya gyara zama yace.

Banyi niyyar daɗewa haka ba abubuwa ne suka ɗan yi yawa har suka janyo hakan" sai yanzu ta saki fuskarta ta motsa ɗan ƙaramin bakinta tace “ai ka faɗamin kasan dake kullum muna waya" da sauri ya kalleta iyakar saninsa baisan rana biyu da sukayi waya da Zainab ba ko ya ɗauki wayar zai kirata baya iyawa ya rasa dalili saidai kewarta da tunaninta ya dameshi ko lkcn da Abba ya sanar dashi tanada ciki ƙarfin hali yayi kawai ya kirata amma tsabar ta duba masa kala har faɗa masa take suna waya kullum.
Sake ɗagowa yayi zaiyi mata magana ya hangeta har ta buɗe ƙofar dakinta ta shige baiyi nufin dakatar da ita ba saima flat ɗin da yaja ya fara cin abincin yana yabawa da baiwar yarinyar wajen iya girki har taso tafi malamar tata wato Umma tabbas kowa yabar gida gida ya barshi dandanon abincin Nigeria dabanne dana kowacce ƙasa ƴan Nigeria sun san darajar maggi a girki kanaci yana ratsa kwanyarka ba kamar sauran ƙasashe ba da saidai kaci kawai kamar abincin masu lalura.

Ya jima yana santin abincin har ƙarawa yayi sannan ya tashi ya shiga ɗakinsa ya watsa ruwa ya canza kaya ya dawo parlour yanayi yana kallon ƙofar fitowa daga dakunan wai ko zata fito amma shiru shidai haƙurinsa karewa yayi ya tashi ya nufi ɗakin ya ishe ta kwance ƙasan tiles da waya a hannunta tana dannawa da alamun abinda takeyi ya ɗauki hankalinta sosai tunda ya fahimci batama san ya shigo ba.
Damar kare mata kallo ya samu yana mamakin yanda ta rame sai fuskarta tayi wani kyau da haske fatarta har wani glowing takeyi ƙirjinta ya ƙara cika sosai abinka da wanda yake a hannu nandanan yanayinsa ya fara sauyawa ya mayar da ƙofar ya murɗa mata key ta miƙe da sauri zaune suka kalli juna tace “Ya haka?

Ƙarasowa yayi ya zauna kusa da ita ta kawar da kanta tare da mayar da hankalinta ga wayarta ya karɓe wayar tare da kasheta ya dafe kuncinsa biyu da hannunsa biyu yace “Kinyi saving damuwa a ranki kinason ki rama abinda ya faru karki zargeni ki cireta a zuciyarki mu zauna lfy nine dai na tafi kuma gani na dawo" banza tabawa ajiyarsa yayi murmushi yace “Ko kiyimin dariya ko kiyimin kuka ko kiyi fushi dani nidai haƙƙina nake nema" ɗagowa tayi tace “Haƙƙi?" Jinjina mata kai yayi da ƙwarin gwiwa tace “Aa wlh Ni bakada wani haƙƙi a jikina..." Murmushi yayi yace “ok bari mu gani" yana faɗin haka yayi kanta ta miƙe da sauri mikewar da zatayi mararta ta riƙe tayi ƙasa da sauri tare da ƙwalla ƙara ya nufeta ya riƙota ta tureshi tana dafe mararta yayi murmushi yace “zaki rainamin wayo idan komai ya kammala sai muje asibiti" da wannan ya kinkimeta ya ɗorata a gado tana tureshi tana kuka amma yayi mata banza Saida yayi abinda yasa kansa sannan ya ƙyaleta zuwa lkcn ta galaɓaita ɗagatan da yayi yaga.

Numfashinta yana sarƙewa shine ya firgitashi ya tallafo wuyanta yana kiran sunanta ta buɗe Idanunta a wahale ta dubeshi hawaye ya zubo mata a galaɓaice tace “Mam....marata...." Da sauri yakai hannunsa mararta ya shafa yaji cikinta ya cure a kasan mararta miƙewa yayi ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya dawo ya ɗauketa itama ya wanketa yasa mata kaya suka fice daga gidan.
Asibitinsu ya nufa tun kafin yaje ya kira ya sanar yanada mara lfy suna zuwa aka dubata sukayi mata hoto komai Normal suka bata magunguna suka koma gida tun a hanya ta rinƙa kwara amai har sukaje gida gabaɗaya ya cika da tausayinta itan ce wani lokacin ta cika gardama data tsaya tayi masa gamsasshen bayani ai da bazai taɓata ba amma ta miƙe zatayi masa tsageranci.
Da wannan suka shiga gidan ranar basuyi baccin kirki ba saboda ciwon marar ya tafi ya dawo haka yake yi mata washegari kuma da taji da dama suka fita tare ya sauke ta a makaranta shikuma ya wucce office shine ya dawo ya mayar da ita gida tun daga shiga gidan ta fahimci canji ta dubeshi tace “Ya Deen ka dawo gida ne?" Da mamaki ya dubeta yace “aa ban dawo ba kamar an shigo gidannan ko?" Jinjina kai tayi tace “nima haka na gani" duba gidan ya shiga yi ganin babu wata ɓarna yasashi sauke ajiyar zuciya yace “baa ɗauki komai ba to waye ya shigo?" Ita dai tama rasa bakin magana saboda kanta da yake juyawa ta lumshe Idanunta tare da zubewa a kan kujera ya Matso yace “yadai?" Iska ta furzar tace “wani irin duhu nake gani a idanuna ina tunanin yunwa nakeji"
Chapter 14 · 0% Book details