Sashe 15
Deen House Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya kalmarta ta bashi wai tana tunani wato batama tabbatar ba, cire rigarsa yayi yace “Ai Banga ta zama ba bbyna najin yunwa" a kasalce tace “Ba komai nake iya ci ba akwai doya dana soya da safe zan iya cinta yanzu da ruwan zafi" jinjina kai yayi ya nufi kitchen ɗin ya haɗo mata kamar yanda tace ta kuwa zauna taci sosai ya tsaya yana kallonta doya da ƙwai me sanyi a haɗa da ruwan lipton babu ko arziƙin madara lallai wani kwaɗon sai lalurar ciki shidai ko da kuɗi yayi wannan haɗin a cikinsa sai yayi amai amma ita lfyr Allah taci ta zauna.
Tana gamawa ta miƙe takai kayan kitchen juyowar da zatayi ne taja baya da sauri tare da furta Innanillahi wa inna ilaihirraji'un da ƙarfi cikin ƙaraji ba komai ne ya sanyata razani ba sai ganin wata narkekiyar kunama baƙa ƙarin tafi girman rafin hannu maƙale jikin handle ɗin ƙofar ta ɗana ƙarinta tana neman wanda zata harba.
Da mugun gudu ta kuma ja baya ganin wata ta ƙara hudo tiles ɗin saime basai taga ko ina yana tsagewa sunata fitowa ba aikuwa ta rinƙa tsalle² tana ihu kunamun sunata nufota har ta rasa gurin fakewa saboda yawansu wata tayi tsalle ta maƙale mata aikuwa ta saki wani razanannen ihu tare da zubewa a gurin sumammiya.
Duk ihun da takeyi Deen baiji ba sai yanzu ya nufo kitchen ɗin da gudu yana zuwa yaganta zube a ƙasa da gudu ya ƙarasa gareta ya fara aikin jijjigata amma a banza har Saida dabarar yayyafa mata ruwa yazo masa ya yayyafa mata ta saki ajiyar zuciya can ta miƙe tana shirin tashi ta zuba da gudu ya riƙota yace “Ke meye hakan?" Idanunta a rintse tace “Wayyoh Ya Deen zasu kasheni yawa suke ƙara wa kunamu duk sun cika kitchen ɗin...." Mamaki ya cikashi ya jijjigata yace “Zainab buɗe idanunki babu komai a kitchen ɗinnan" sai lokacin ta samu ƙwarin gwiwar buɗe idsnunta ta kuwa faɗa jikinsa da sauri ta rushe da kuka tace “Deen meye yake faruwa ne wlh kunamu nagani daga ɗaya sukayita ƙaruwa Saida ya cika kitchen ɗin nan harma wata ta maƙalemin a jikina....
Rufe mata baki yayi yace “Shikenan ya isa firgici kawai kika samu amma babu komai" ɗagata yayi cak suka koma parlour ya rinƙa yi mata tausa har bacci ya fara ɗaukarta cikin baccin taganshi tsaye da wuƙa akanta ya ɗaga zai daɓa mata a ciki, tayi wata zabura ta miƙe tana kiran sunansa ya riƙe da sauri ganin shine tace “me nayi maka zaka kasheni don Allah karka kasheni wlh inawa Mamana addu'a Ni kaɗai ta mutu ta bar...."
Rufe mata baki yayi yace “Oh God Zainab ko kina da aljanu ne?" A raunane ta dubeshi tace “Nidai koma bulukiya ce a kaina na rokeka kada ƙiyayya ta daka faraji tasa ka kasheni don Allah ya Deen idan ka gaji dani ka mai dani gidan Abba basai ka kasheni ba su suna sona" tana faɗin haka ta rushe da kuka ta zamo ƙasa ta rinƙa yi masa magiya tana cewa “Don Allah Ya Deen don girman Allah karka kasheni kabarni da raina Ni sai na bar maka garin ma idan ganina ne bakason yi......
[10/13, 11:59 AM] AM OUM HAIRAN: *DEEN HOUSE*
*Bonus page*
Daga yau 16 ga watan Rabi'ul Auwal zuwa 19 ga watan farashin wannan littafi ya sauka daga 300 ya koma 200 VIP daga 600 ya koma 400 PC daga 1k ya koma 600 ku hanzarta ku biya kafin wannan damar ta wucce, ga me son biya zai tura ta wannan acct ɗin 0255526235 Fauziyya Tasiu ko3184512451 First bank ko katin MTN ta WhatsApp number na 09013718241 Ƴan Niger katin Airtel.
*33-34*
Yanda take masa magiyar tana kuka tana riƙon shi gaba-daya sai kansa ya kulle to wannan kuma wanne sabon salo ne Zainab ɗin takeson zuwa dashi ɗazu tace kunama yanzu tace zai kasheta, bashida wani zaɓi da ya wucce zaman aikin rarrashinta har Saida ya tabbatar mata mafarki ne aikuwa kin sake kwanciya tayi ta zauna tana kallonsa ya tashi ya tafi sallar magrib itama ta nufi ciki don yin alwala tana shiga ta mayar da ƙofar ta rufe ta nufi bathroom ɗin da addu'a a bakinta ta ɗauro alwalar ta fito tana fitowa taga hasken dake ɗakin ya ɗauke bata kawo komi ba domin ranta bata yayi wuta suka ɗauke sai ya shigo ya jorner musu engine ko solar.
Saime maimakon da wutar ta ɗauke taga duhun yaci gaba da wanzuwa sai kawai taga ɗakin yayi wani jan haske cikin haske ne kuma taga wata inuwa ta bayyana da takasa ganin ƙarshenta take tsoro ya kamata ta matsa baya da sauri jikinta ya ɗauki rawa bakinta ɗauke da duk addu'ar da tazo bakin nata.
Ta jikin wannan doguwar inuwar taga wani baƙin hayaƙi ya fito ya nufota ta rinƙa matsawa tana addu'a cike da tsoro da firgici amma maimakon taga abin ya ragu sai taga yana ƙaruwa yanayin wani kanannaɗe irin na maganin sauro yayi sama kafin ta ankara ya zagayeta wata masifa yana zagayeta ta rinƙa jin ana matseta tare da wani irin zut zut kamar ana zuƙar jininta haka taci gaba da kuka tanata ƙoƙarin ƙwatar kanta amma ta kasa har ƙarfinta ya gaza ta zube a gurin tana wani irin kakarin wahala daidai lokacin data gama ficewa daga hayyacinta ubangiji ya shigo da Deen ya nufi ɗakin nata yana kiran sunanta baiji alamun zata amsa ba hakanne yasa shi shiga ɗakin yaga duhu ya ɗauki wayarsa ya haska ya hangeta a zube a ƙasa.
Da sauri ya kunna glub ɗin ya isa gareta sai wani nannaɗe jiki takeyi tana mimmiƙewa cikin ɗimuwa da tashin hankali ya rinƙa girgiza ta maimakon ta buɗe idanunta hakan bata samu ba saima jini da yaga ya soma fita ta baki da hancinta tsoro ya ƙara shigarsa ya dagata cak ya fice da ita yasata a mota yayi hanyar asibitinsu da ita dakansa ya fara bata taimakon gaggawa.
DEEN ya shiga kiɗima da lamarin yarinyar ganin yanda akayi mata wani wawakeken rami a gabar gwiwar hannunta jini sai zuba yakeyi ga ramin yayi zurfi sosai, shidai haka ya rinƙa bata kulawa ranar batayi kwanan hayyaci ba shima bai rintsa ba saboda zaburar da takeyi.
Sai asuba Allah ya taimake shi ta farka tayi miƙa tare da salati ta buɗe Idanunta a ɗan tsorace wannan inuwa da wata mata data caka mata farce a gaɓar hannu sunayi mata gizo ta zabura ta mike tare da fara karanto addu'o'in neman kariyar ubangiji, Deen dake tsaye yana kallonta ya kira sunanta ta buɗe Idanunta suka kalli juna tace “Yaya kaine?" Ɗaganta kai yayi yace “nine Zainab meye yake faruwa ne?" Ajiyar zuciya tayi ta ɗago hannunta ya kama ya tashe ta zaune ya zauna a gefenta hakan ya bata damar kwantar da kanta a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya.
Iyakar sonta data bashi labari ta kasa ko tayi yunkurin magana kasawa takeyi to shima bai matsa mata ba amma ya ƙudurce a ransa zai rinƙa bibiyarta don gano matsalarta, haka suka tashi suka koma gida tunda suka shiga kwanar unguwar gabanta ke faduwa har suka isa gidan yayi parking ya fito ya bude mata itama ta fito suka nufi gidan a ƙofar shiga parlour taja da baya da ƙarfi tare da fasa ƙara ta take zata zura da gudu ya bita suka zuba tsere dakyar ya kamota ya mannata da jikinsa yanda yaji jikinta na ɓari ya sashi a mamaki ya rinƙa shafa bayanta tare da lalubar kunnenta ya sanya harshensa a ciki yana tsotsa tare da hura mata iska.
Can tsayin lokaci yaji ta sauke ajiyar zuciya ta sanya hannu ta maƙalƙaleshi yaja numfashi tare da cewa “ƙanwata" cikin sanyin murya tace “Na'am" janyewa yayi ya sake kama hannunta ta turje ya juyo ya kalleta ta noƙe kafaɗa tace “Baƙin maciji ne ya cika bakin ƙofar kuma ya fasa kai Ya Deen karmu shiga" murmushin tausayinta yayi yace “Babu komai Zainab Allah bazai bashi damar cutar damu ba zo muje"
Batason yi masa gardama shiyasa tabi bayansa jin tana shirin juyawa ya cafki hannunta ya ɗagata cak ya shigar da ita parlourn ya ajiye ta saman kujera, wani abin mamaki maimakon maciji ɗaya data gani dazun yanzu sun zama biyu kuma kowanne ya fasa kai ya zaro harshe waje gashi dai ya mayar da ƙofar parlourn yayi mata key duk da haka bata daina ganinsu ba sunma juyo da kawunansu itadai duk a tsorace take saboda ko normal maciji bata ƙauna mugun tsoransa takeji bare wannan data lura ita kadai take ganinsa don iya kwatsncenta da nunawa Deen macizan shi yace bai gansu ba ƙarshe sai haƙura tayi da nuna masa shi kuma ya shiga ɗaki ya dauko ƙur'ani yazo ya bata ɗaya ya buɗo suratul Baƙara ya fara karantawa tana binsa suna karatun tare amma fah har zuwa lokacin hankalinta yanakan waɗannan macizai maimakon da suka fara karatun su gudu kawai sai taga sun fara aman wuta suna feso musu amma wutar bata zuwa garesu take mutuwa.
An ɗauki lokaci a haka taji wata kururuwa me kashe dodon kunne wannan karon ba ita kaɗai taji ba shima yaji duk da ƙarar da yaji batakai yadda taji ba ya juyo ya kalleta ya zubawa gurin da take kallo idanu ganin ta miƙe shima ya mike yace “Ina zaki meye yayi ƙara?" Nuna masa ƙofar shigowa parlourn tayi tace “Sun kama da wuta kagani sai cin wuta sukeyi" murmushi yayi yace “To ai Alhmdllh Kinga sai su barmin ke ki sarara" ajiyar zuciya tayi ta kama hannunsa tace “Ka kaini gidan Umma in zaka tafi office" zaro idanu yayi yace “sabida gantali" idanunta ne ya kawo ruwa tace “Wlh tsoro nakeji Ni kaɗai" shafa cikinta yayi yace “Bafa abinda zai sameki sai ikon Allah kiyi hƙr ki saba da rayuwa a gidanki yafi ki rinƙa yawon bin gidaje yanzu idan na kaiki gidan Umma kin yini to kwana fah tunda kinsan bake ɗaya ke gareni ba?"