← Book details Deen House Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 25

Sashe 19

Deen House Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abinda yake bata mamaki wannan hudar bata bajewa kuma sai taga gurin duk ya ɓaci da jini wannan tasa mata mugun tsoron kasancewa da Deen indai yayi tunanin kusantarta sai yaga alamun firgici a tattare da ita gata da mugun zurfin ciki tambayar duniya ta kasa faɗa masa dalilin da yasa take shiga damuwa idan ya kusanceta.
Kuma a daidai lokacin sai Allah ya jarabceta da wata irin kasala indai zai kusanceta to bazata iya taɓukawa kanta komai ba harsai tayi bacci ta farka kai hatta yawan ibadarta Saida ya ragu batada aiki sai bacci da bin sanyin tiles.
Cikin hakan ne kuma abubuwa suka rinƙa sanja salo kulawar da yake bata gabaɗaya ya daina hankalinsa ma yabar kanta ko sauraronta bai cika yi ba duk jarabar nacinsa gareta kamar wanda aka cirewa ya daina bibiyarta ko gado ɗaya sai su kwanta su tashi bai saurareta ba ita kuma sai ta jarabtu da mugun son kasancewa dashi tun tana shareshi saboda kunya har takai a hakan batada cikakkiyar lafiya amma duk abinda tasan zai alamta masa buƙatarta gareshi shi takeyi.

Maimakon sauƙi sai tunzuri takai tun wata rana daya shigo ya tarar da ita tana amai kamar wanda aka yayyafawa ruwan masifa haka ya rufe ta da faɗa duk tsaftar Zainab Deen baiji kunya ko shayin cewa da ita ƙazama ba haka ya gama cinye mata mutunci tsaf ya tsaya tayi masa bayani ma kasawa yayi a cewarsa wai gidan wari yakeyi tana kallonsa ya juya ya fice.
Rarrafawa tayi ta shige ciki ta kwanta cikinta nayi mata ciwo amma ya saurareta ma ta kasa samun wannan arziƙin kalmar ƙazama tayi mata ciwo haka taci kukanta ta share hawayenta akaci gaba da tafiya a haka dole kesa Deen shigowa ɓangarenta ran girkinta itakam takan gwammacewa zamansa a part ɗin Nafisa wahala biyu in yana part ɗinta gata jiki gata masifarsa kyara da tsangwama, abincinta kuwa rabon da Deen yasashi a bakinsa har ta manta indai taga dariyarsa da kulawarsa to ga Nafisa ne itako ta zama banza ta zama wofi batada wata power haka ta rinƙa jiyyar rashin sanin abinda yake damunta har wajen wata bakwai tana a kunci saidai tayi kuka ta share hawayenta ta kasa faɗawa kowa to wama zata sanarwa? Ya kyautu ta rinƙa zuwa tana fadawa Umma da Abba laifin Deen ne bayan tasan duk daɗin kunun zaƙi baikai na ruwa ba, ta sani duk yanda suke sonta ba kamar Deen da suka haifa ba, gata batada uwar da zata faɗawa matar ubanta ta tsaneta da iya tsanar ce ma da sauƙi to mahaifin nata ma ta rabata dashi baya ko waiwayenta......."

Bata fahimci meye ke tare da ita ba Saida taga mararta ta ɗaga sosai ga kuma motsi tanaji a cikinta nan ta kira Umma take faɗa mata tunda shi yaƙi saurararta bare su tattauna Umma ce ta kirashi tace yakai Zainab asibiti inshi bazai samu damar dubata ba, ransa baiso ba yace ta shirya suje asibitin bayan ya gama masifarsa.
Ta shirya sukaje yasa aka dubata cikine har wata shida da sati biyu duk da rashin mutuncin da yake yi mata ranar Saida yayi murna har siyayya yayi mata duk jikinta ya ƙara sanyi a ranta tana raya wato ita batada wata daraja a gurin Deen sai idan morarta zaiyi? Hawaye ya tsiyayo mata tayi saurin gogewa suna komawa gida ya faɗawa Umma nan ta gargaɗeshi da yayi shiru da bakinsa batasan surutu har ta ƙara da cewa dama wancan cikin ance Mayu ne suka cinyeshi wannan tasa yaja bakinsa yayi shiru tunda da gaske yakeson haihuwar.

To tundaga wannan rana ta ɗan samu sauƙi babu dai wata kyakkyawar mu'amala amma kullum zai tambayeta meye takeso in tana bukatar wani abu ta sanar dashi in bata buƙata tace bata buƙata duk da haka inya fita saiya samu abinda zai shigo mata dashi da haka har cikinta ya shiga wata na tara sai a lokacin Nafisa tasan dashi sun fito zai kaita asibiti ba ƙaramin tashin hankali Nafisa ta shiga ba da ganin cikin kamar ta mutu don baƙin ciki saboda tsabar hassada itama cikin ne da ita amma ƙyashi takeyi da na wata.
Kwana biyu tsakani da dare wajen sha biyu Zainab na kwance taji an buɗe ƙofar parlourn ta tashi zaune da sauri tunda dama a wannan ƙadamin bacci ba yuwuwa yakeyi ba, shiru taji hakan yasata tashi ta buɗe ɗakin ta fito bakinta ɗauke da bismillah hadi da addu'ar neman tsari, tsayawa tayi turus ganin Deen yanata safa da marwa a parlourn cikin mamaki ta kira sunansa ya juyo ya zubanta idanunsa da sukayi jawur ta taka a hankali tana cewa “Meye ne ya hana ka bacci a wannan daren?" Sunkuyar da kansa ƙasa yayi ya sanya hannunsa a aljihunsa ya zaro wata takarda a naɗe ya miƙa mata ya juya ya fice da sauri.
Duk ta kasa buɗe takardar hannunta har rawa yake wajen karɓa gabanta na bugawa da ƙarfi haka tayi karfin halin buɗe takardar tare da waro idanunta tace “Wht? Innanillahi wa inna ilaihirraji'un! Ya Deen saki kace ka sakeni saki uku..........

Please karki karanta in baki biya ba Nrml group 300 VIP 600 PC 1k acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin waya MTN ta WhatsApp number na 09013718241 ƴan Niger zaku turo kati Airtel
[10/19, 8:33 PM] AM OUM HAIRAN: *DH*

*_Oum Hairan_*

*_Paid page_*

Jiri taji yana ɗibanta hakan yasa dole ta dafe bango cikinta na rawa tashin hankalin da bata taɓa tunanin ana shiga irinsa ba ranar shine ya kawo mata ziyara saboda masifar data riski kanta ma a ciki kuka ma ta kasa sai azabar tafasar zuciya.
Dakyar taja ƙafafunta ta koma ɗakinta ta zube a ƙasa wani ciwon mara ya ziyarceta ta wawuro wayarta a wahale tama rasa waye zata kira a wannan lokaci cikin azabar zuciya data ciwo ranta ya bata ta kira mahaifinta ai duk daɗin uban wani baikai naka ba kasa kiransa tayi saboda ta sani ko ƙalau ta kirashi sai yaga dama yake ɗagawa.
“Idan na rasa gatanka a daidai wannan lokacin tabbas zanci gaba da rayuwa matsayi mara makoma na rokeka Dad kaji tausayina ka bani matsuguni a gidanka ta yanda zanyi nesa da Shamsuddeen, Dad ina baƙin cikin sanar dakai ƙasa da minti goma Ya Deen ya sakeni saki uku"......
Tana gama rubutawa ta turawa Alh Ibrahim ta zauna zaman jiran tsammani ta rasa abinda ya dace ta tashi tayi fita zatayi a wannan tsohon daren ko kuma bari zatayi sai gobe? Azalzalarta zuciya takeyi ganin lokaci na tafiya babu reply babu kiran mahaifin nata kawai ta yanke shawarar tashi ta bar gidan tana ganin yafi mata alkhairi.
Hijjab ɗinta ta zura tana dafe mararta ta fito ta janyo ƙofar ɗakin idanunta na zubar da hawaye tace “Allah kanaji kana gani Allah bansan laifina ba da yakai mijina ya yanke shawarar rabuwa dani rabuwa ta har abada...

Wayarta taji tana ring ta duba da sauri cikin tsoro ta ɗaga muryarta na rawa tace “Dad... Daddy...." Ajiyar zuciya yayi yace “Mamana fito ina ƙofar gidanki" wani hawaye ya zubo mata me sanyi tace “To" ta kashe wayar ta nufi get ɗin ta buɗe motar data gani a ƙofar gidan ita ta nufa ya buɗe mata ta shiga ya zubanta idanu tare da sauke numfashi me nauyi yakai hannu ya dafa kanta tare da sanya ɗayan ya share mata hawayen yana girgiza mata kai yace “Ya isa haka Mamana kiyi hƙr kowanne bawa baya wuccewa ƙaddararsa da baki yace ya sakeki ko a takarda ya rubuta?" Miƙa masa takardar tayi ya buɗe.
“Ni Shamsuddeen Nuhu na saki matata Zainab saki uku in ta haihu ta sami miji tayi aure...." Wani murmushi me ciwo Dad yayi cikin tausayin ɗiyar tasa yace “Ai Shikenan muje gida Allah yasa hakan shine yafi alkhairi" jan motar yayi sukabar ƙofar gidan ta rushe da kuka me ciwo ta faɗa jikin Dad jikinta na rawa tace “shi...Shikenan Dad ya rabu dani... Wayyoh Allah na shiga uku meye yasa tun lokacin da bansoshi ba yaƙi rabuwa dani Saida ya koyamin soyayyarsa Dad waye zai mayemin gurbinsa?...."

Rufe mata baki yayi yace “Ki daina Mamana banason kukanki nasani kin tawaya a rayuwarki insha Allahu yanzu zaki samu gatan uba da kika rasa a baya Mamana ki yafemin wlh inasonki bansan dalilin da yasa na kasa janki a jikina ba" shiru yayi yana furzar da iska don ya lura bata da niyyar daina kukan shi kansa yasan kukan zai rage mata damuwa inya hanata ma baiyi mata adalci ba daga Rijiyar Zaki zuwa Sallari tafiya ce ba wata me shahararren nisa ba itakam batasan sunzo ba Saida taji ya buɗe mata kofa ya kamo hannunta suka shiga gidan duk da bata cikin nutsuwar tantance abubuwa tasan ba asalin gidan data sani bane.
Koda suka shiga wani ɓangare ya buɗe mata yace ta shiga ta tsaya tana kallon part ɗin komai akwai a cikinsa sosai ya haɗu nan ta zauna a bakin gado ya juya ya fice tare da cewa “Karkisa damuwar komai a ranki Mamana kiyi bacci kamar bakida wata matsala insha Allahu bazaki ƙara kuka ba"
Da wannan yaja mata ƙofa ita kuma ta kwanta badon tayi bacci ba saidon ta bawa zuciyarta dama tayi yawon ta yanda takeso.

Washegari da wuri ta tashi don dama ba baccin tayi ba ta fito a wanka kenan taji ana taɓa ƙofar tabada izinin shigowa wata mata ce da bazata wucce shekaru arba'in ba ta shigo da sallamarta da murmushinta tace “Jiya ina gurin aiki Daddynki ya kirani yake bani mummunan labari Zainab sai hƙr halin maza Bama ku sanya ƙafa ba nidai fatana karki sanya damuwa a ranki musamman da kike da tsohon cikin nan"
Sunkuyar da kanta tayi cikin ladabi ta gaishe da matar duk da batasanta a gidan mahaifin nata ba Hajiya Luba ta sani to ga kuma baƙuwar fuska wadda alamu yake nuna da bambanci tsakaninta da Hajiya Luba.
Kama hannunta Hajiya Sadiya tayi suka zauna tace “kina mamaki ko Ni baƙuwa ce shiyasa baki Sanni ba gabaɗaya satina biyu a gidan mahaifinki dama a satin nan nake cewa dashi ya kaini naga ƴata Zainab dayaketa bani labari tun kafin nazo to kuma Kwatsam wannan abu ya faru"
Chapter 19 · 0% Book details