Sashe 21
Deen House Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata uwar harara ya watsa mata ya juya ya fice yana duba agogon hannunsa ɗaya da rabi na rana asibitin da Abba ya sanar dashi can ya nufa bai sha wahala wajen gano ɗakin ba da Umma sukayi karo ta kwaso kayan da aka ɓata zataje ta wanke ta watsa masa harara tare da jan tsaki ta wucceshi duk sai jikinsa yayi sanyi yaja ƙafafunsa daƙyar ya nufi ɗakin Hajiya Sadiya dake fitowa tace “Aa Shamsu ashe sun sanar dakai yanzu nake shirin kiranka" shafa kansa yayi yace “Abba ya sanar dani"
Sake gaisawa sukayi sukayiwa juna Barka ya shiga ɗakin ita kuma ta nufi pharmacy domin siyo magani Allah ya taimake shi ɗakin sai Zainab ita kaɗai tana zaune ta haɗe kai da gwiwa sai sauke ajiyar zuciya takeyi, ya jima tsaye kanta bata sani ba har Saida yakai hannu zai ɗauki yaron sannan ta ɗago Idanunta ya shiga cikin nasa gabansu ya faɗi tare ta janye idanunta daga kansa ya sanya hannu ya ɗauki yaron da keta baccinsa hankali kwance buɗe masa fuska yayi yana kallonsa yaron masha Allah kyakkyawa dashi bai ɗauko komai na kamannin Zainab ba hatta haskensa na ubansa ne.
Sake sauke idanunsa yayi kan Zainab yace “Na gde ƙanwata" daga haka bai iya sake ce mata komai ba tsayin lkc har Umma ta shigo ɗakin ta tsaya turus tace “Aa ikon Allah Shamsu baka gama ganin ɗan naka bane?" Yasan Umma sarai bata ɗaukar abubuwa da wasa hakan yasashi yin ƙasa da kansa yace “Ku fahimceni Umma...." Dakatar dashi tayi da cewa “Dakata don Allah ba sai kace komai ba in ka gama kallonsa ka ajeshi ko kaje dashi ina buƙatar kaɗaici da Zainab"
Kora da hali Umma takeyi masa ya sani don haka ya aje bbyn ya fita Matsawa tayi ga Zainab tace “Meye yace Miki?" Girgiza kai tayi alamun baice mata komai ba ta sauke numfashi tace “Ki nutsu kisan inda ke Miki ciwo Zainab Ni na haifi Deeni amma bazan iya cewa komai game da halinsa ba, Zainab duk abinda kake tunanin bazai iyaba iyawa yakeyi kija darajarki ki zama me zuciya duk mutumin daya nuna baya son kasancewa tare dakai kaima ka janye jikinka daga gareshi Zainab rabuwarki da Deen bazai zama ƙarewar nasarar ki ba indai akan wannan ne kike zubar da hawayenki to ki daina"
Kalami ta rinƙa bata masu sanyaya zuciya har Saida taga ta saki ranta sukaci gaba da karɓar Barka wajajen yamma suka koma gida basu jima da komawa ba Deen ya shigo da kayansa niƙi² duk yanda yaso ganin Zainab bai samu ba kasancewar Umma ta kasa ta tsare Deen ya shiga damuwar da bai taɓa shiga ba a haka akaci gaba da tafiya har zuwa ranar suna akayi sunan babu wani armashi duk da ba ƙaramar bajinta Deen yayi ba a haihuwar amma rashin walwalarsu yasa kowa ma walwalarsa tayi ƙaranci.
Sai ranar suna sannan ya yarda ya kawo Nafisa tun daga get ɗin gidan ta raina kanta ta dubeshi tace “Shamsu inane nan ɗin?" ”Gidansu Zainab ne" ya faɗa batare da ya ko kalli inda take ba bare ya fuskanci mamakinta ya fice daga motar itama ta fito tana kallon gidan tana jinjina mamakinta wai ashe mahaifin Zainab attajiri ne lallai dole ta sake ɗaura ɗammara ashe ita da ƴar attajirai take kishi bata sani ba.
Da wannan tunanin suka shiga parlourn da Bahijjah ta fara haɗuwa Bahijjah tayi mata kallon mamaki tace “Sai yau akazo ganin ɗan kenan mugun ya hana" murmushi tayi tace “Me zanyiwa kuma bayan wanda ya haɗa ya raba" murmushi itama Bahijjah tayi ta kuma cewa “Ai fah dama dake kinsan zaren ba kalar yadin bane dama shigar sauri ce ta baku ba cancanta ba irinki kece kika dace da....."
Shigowar Deen ɗin ce tasata haɗiye maganarta da cewa “Abban Abdullah Barka da isowa" dafa kanta yayi yace “kyautarki ta musamman ne Bahy ina Zainab ɗin" kallon ƙofar ɓangaren Dad tayi tace “Kanta ke ciwo batason hayaniya shiyasa Dad yabada umarnin ta koma can kuma kar wanda ya shiga" jinjina kai yayi ya juya ya nufi part ɗin ya murɗa ƙofar ya shiga s parlour ya ishe Zainab ɗin kwance dafe da kanta Saida ya isa ya tsaya a kanta sannan ta ɗago ta sauke idanunta kansa yayi mata kyau sosai cikin shigar tasa ta yau, ta haɗiye wani abu me ciwo ta juya masa baya ya zauna tare da dafa cikinta yace “Meye ya kawo ciwon kan?" Tsaki tayi ta miƙe zata fice daga ɗakin ya cafko hannunta yana shirin magana ta gasa masa wani masifaffen mari daya sanyashi sakin hannunta tace.
“A farko kana cikin mutane masu daraja da nakeyi dansu dole kona bari donsu tsakiya ka zama me ragaggiyar daraja ƙarshe darajarka ta dawo arziƙin aure and end kuma nakejin cewa babu wata sauran alfarma ko ƙima da kake da ita a wajena Shamsuddeen ina me umartarka fita daga rayuwata ta lumana ko kuma ka fita don dole.........
Please karki karanta in baki biya ba Nrml group 300 VIP 600 PC 1k acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin waya MTN ta WhatsApp number na 09013718241 ƴan Niger zaku turo kati Airtel
[10/23, 11:24 AM] AM OUM HAIRAN: *DH*
*_Paid page_*
*_45-46_*
Bawai ciwon marin da tayi masa ne ya hanashi motsi ba a'a ciwon kalamanta lallai da gaske Zainab ta ɗauki wannan lamari, yana kallo har ta fice daga ɗakin taja ƙofar da karfi shima gwiwa a mace ya nufo parlourn Abba ya gani tsaye da bbyn a hannunsa ya ƙarasa suka gaisa daidai lokacin da Dad ya fito Dad ya dubeshi yace Deeni inason ganinka" ransa na ayyana masa abubuwa da yawa yace “To Daddy gani" murmushi yayi ya kama hannunsa suka koma parlournsa suka zauna ya dubeshi yace.
Lamarinka da Zainab yasani a kokwanton da har yasa na fara bincike game da lamarin a matsayina na lauya na binciki abokan aikina da yawa ko sun taba samun irin wannan cest ɗin abu ɗaya suke tambayata shin kana shaye² ne ko kuma kanada shafar aljanu? Nakan rasa amsar da zan basu duk da nasan cewa a baya dai bakashan komai to amma faruwar wannan al'amari yasa yasa na fara kokwanto akanka.
Ina kan bincike Deeni kaje kayi hƙr nasan kanason matarka idan bincike ya tabbatar da kamar yanda kake da'awar bakaine kayi sakin ba, ya tabbata bakaiɗin bane to zan dawo maka da matarka idan kuma ya tabbata kaine koda a cikin maye ne to saidai kuyi hkr daga kai har ita ku cinye jarabawa domin ita ƙaddara ta riga fata watakil akwai wani abu da ubangiji ya ɓoye shiyasa hakan ta faru, kafin nan inason ka bani damar tattaunawa da matarka don sanin ta inda zamu fara aikinmu"
Shiru Deen yayi har Saida Dad ya kuma magana sannan ya ɗago yace “Ok Daddy bari a kirata" wayarsa ya ɗauka ya kira wayar Nafisa ta daga yace “kice da Bahy ta rakoki part ɗin Dad" yana faɗin haka ya kashe wayar ta dubi Zainab dake zaune a gefenta tace “To Zainab Allah ya kyauta ya kawo abokin zama na kwarai Allah ma ya taimake ki bazakiyi dogon Zama a gida ba"
Bahijjah ce ta yunƙura bata amsa Zainab ta dakatar da ita tace “Amin na gde aunty Nafisa" fita sukayi Bahijjah na hararar Zainab ta rasa wanne irin sanyin zuciya ne da Zainab da bata ɗaukar abubuwa da zafi.
Shiga sukayi part ɗin Dad Dad ya dubi Deen yace “Ɗan bamu guri" miƙewa yayi ya fice Nafisa ta bisa da wani malalacin kallo kafin ta mayar da hankalinta a kallon ƙawatuwar falon tana rayawa a ranta lallai jin daɗi yana wajen masu kuɗi, a zahiri kuma gaishe da Dad tayi da Abba dake shigowa.
Dad ne ya kira sunanta yanda ya furta sunan nata Saida gabanta ya faɗi tace “na...na'am" sake kafeta yayi da idanunsa dake cikin farin Glass yace “A daren da mijinki ya saki abokiyar zamanki kina ina ke?" Da sauri tace “Ina part ɗina" “Ok meye ya faru a daren?" Kallonsu tayi ya sake gyara zama yace “mijinki yana da'awar bai saki matarsa ba mun kasa samun shaida ke kadai zaki warware wannan abin" jin abinda ke faruwa ne yasa ta dake tace “Muna kwance naga ya tashi ya fita bayan nan bansan meye ya faru ba amma naji ya buɗe ƙofar parlour sai bayan dogon lokaci ya shigo ya isheni a parlour nake tambayarsa ina yaje yacemin can part ɗin nace me yaje yayi nan yake cemin sakinta yayi shine nace akanme zai saki mace da tsohon ciki nan ya rufeni da faɗan karna dameshi don bansan abinda yakeji ba idan ya kalleta"
Jinjina kai sukayi Dad yace “ko mene shaidarki?" Da sauri tace “Akwai CCTV a gidan indai baya gogeba ina tunanin ta ɗauki komai" ajiyar zuciya Dad yayi yace “Ok jeki" Dad ya sallameta bayan yayi mata kyauta me tsoka ta fita ya kira Shamsu yabashi umarnin dauko masa modern na CCTV na gidansa.
Da karfin gwiwa ya amsa suka fita da Dad tare sukaje suka ciro modern ɗin suka nufi gidansu Deen acan ne suka sanya videon komai tun daga fitowar Deen daga ɗaki har zuwa lokacin daya ɗauki biro ya yagi memo yayi rubutu har zuwa lokacin daya fita a parlourn kama zuwansa part ɗin Zainab buɗe parlournsa da shigarsa da fitowarta sanye da rigar bacci da lokacin da take tambayarsa lafiya meye ya hanashi bacci da tsohon daren nan har zuwa juyowarsa da miƙa mata takardar da juyowarsa ya fice da sauri, kai har komawarsa part ɗin Nafisa da tambayar da tayi masa da amsar daya bata.....