← Book details Deen House Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 25

Sashe 6

Deen House Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wai meye ya hadaki da Yayan naki ne?" Numfashi ta sauke ta basar da zancen da cewa “Nayi tunanin da wuri zaki dawo sai naga har mun fita baki dawo ba" hira suka fara ƙarshe suka tashi suka shiga kitchen suka ɗora abinci sukaci suka sake shantakewa da hira Nafisa akwai Magana.
Surutun ta har damun Zainab yakeyi data gaji ta shige ɗaki bata jima da shiga ba taji an buɗe ƙofar an shigo ta ɗago sukayi ido huɗu ya miƙa mata kwalin waya ya juya ya fita tabi kwalin da kallo cike da farin ciki Allah yayita da son waya a rayuwarta shiyasa tayi murna da wannan kyauta ta bazata ta zauna ta ɓareta waya ce babba da gaske ta daɗe tana juya wayar kafin ta kunna ta murna ta cikata ganin harda layi a ciki nan ta rinƙa shige² tanajin farin ciki na mamaye ta batasan ya shigo ba Saida taji ya fizge wayar ta ɗago fuskarta a sake tace.

“Wlh naji daɗi sosai na wayar nan Ya Deen inason waya ko don chat" kallon da yake yi mata ne yasata shiga hankalinta ya tako ya zauna kusa da ita yace “Meye tsakaninki da Zaharaddeen?" Da sauri ta ɗago tace “Wai Ya Zain?" Jinjina mata kai yayi tayi murmushi tace “Babu komai sai zumunci da aminci...." “Da kuma soyayya ko?" Ya faɗa yana miƙewa yaci gaba da cewa “Ba damuwata kiyi soyayya dashi ba kawai dai zan faɗa Miki koda bazaki yarda ba Zainab bakida mijin da ya fini jinki nakeyi matsayin matata shiyasa nake mu'amala ta mata da miji dake ba kuma zan fasa ba naje nayiwa Abba magana kamar yanda nayi Miki jiya yaƙi amincewa to dalilin dole zaisa ya amince tunda bazasu yarje min ta maslaha ba"
Ficewa yayi ta taɓe baki tace “tunda kai ka haifeshi ai saikayi masa dolen" tashi tayi ta fara bincika kayanta ta dauko number Zain tasa a wayar ta kirashi bugu biyu ya daga muryarsa a kasalce tace “Allah shi taimaki Yayana...." Ya cafe da cewa “kuma mijinki” dariya tayi tace “ashe zaka ɗauki murya ta" yace “ko cikin dubu ko cikin ciwon ajali Muryar matata bazata taɓa ɓacemin ba" nan take labarta masa tayi waya yayi murna yace “Dama inason Inna dawo na roƙi alfarmar Abba ya barki ki riƙe waya ashe kafin nazo ma Deen zai samamin mafita.

Murmushi tayi na yaƙe tace “Na daɗe inason na sanar dakai amincewata da kuma zaɓarka da nayi Ya Zain amma dai Abba bazaisa aurenmu da nisa ba ko?" Cikin matsanancin farin ciki yace “Wayyoh daɗi ƙanwata insha Allahu jibi zanzo zanyiwa Abba magana na kusa gama komai yanzu ma abinda ya tsaida ma'aikatar da nake ne sukeson riƙeni so zan dai nemi alfarma nazo serious ina buƙatar aure" sunsha hirarsu ta ƙauna Zainab ta manta da wata damuwa ta rasa meye yasa indai tana tare da Ya Zain bata tuna wata damuwar duniya.
Kamar yanda ya alƙawarta mata kuwa hakance ta faru ranar Alhamis ya shigo Kano baije gida ba Saida yazo gidan yayan nasa suka sha hira da abar ƙaunarsa Nafisa na tsokanarsa yanata dariya sai yammaci ya nufi gida, da dare kuwa sunga bala'i da Deen ya dawo ya samu labarin zuwan Zain gidan abin har tsoro ya bawa Nafisa tace “To wai kai ina ruwanka da lamarin Soyayyarsu tana sonsa shima yana sonta saboda haka wannan aure ikon Allah ne kawai zai hana yinsa" bai bata amsa ba ya shige ɗakinsa yana fatali da komai cikin tashin hankali yake cewa “Akanme Abba zaimin haka meyesa zai bawa Zain Zainab bayan yasani Ni nafi cancantar mallakarta?

Da dare ta fito kitchen don ɗaukar abinci ya ritsata acan ta juyo da sauri tsoron shaiɗancinsa takeyi yanda taga idanunsa ya kaɗa ya sake firgitata ta ɗauki abincin ta juya zata fice ya cafko hannunta ya mannata da ƙirjinsa yace “zuwa yanzu ya kamata ace kinyi sabon da bazaki yarda a rabamu ba amma na fahimci ke ba wannan ne a gabanki ba Zainab meye da Zain wanda banidashi uwa ɗaya uba ɗaya fa ta kawomu duniya dashi me kike tunanin samu a gurinsa wanda bazaki samu a gurina ba?"
Shiru tayi masa kanta a ƙasa ya sanya hannu ya ɗagota ya ɗora bakinsa a kuncinta ya lashe hawayen firgicin daya zubo mata yace “Wlh bazan bari na rasaki ba zan iya yima Zain kyautar komai amma banda ke don nafisa buƙatarki...." Da wannan ya fara lalubeta zuciyarta takai maƙura zuwa yanzu dole ta rinƙa ƙoƙarin ƙwatar kanta hakanne yasata tureshi ya sake cafkota ta kuwa wawuri cup na glass idanunta na tsiyayar da hawaye tace “Na rantse da Allah ka kuma taɓani saina illataka...." Damƙar damtsenta yayi batare da yayi tsammani ba yaji danshi a goshinsa ya sake ta da sauri dafawar da zai yi yaji kwalba cake a goshinsa jini yana tsartuwa aikuwa tana ganin hakan ta ɗiba da gudu bai iya tareta ba.

Saboda tsabar tsananin mamaki da takaici ita kuwa tana fita ɗakinta ta faɗa tayi masa key ya fito bugun duniya taƙi buɗewa takaici yasashi komawa ɗakinsa zuciyarsa na bijiro masa da irin matakin da zai ɗauka, shigarta ɗakin babu daɗewa wayarta tayi ƙara ganin Number Umma Tsoro ya kamata ta kara wayar muryarta na rawa tace.
“Don Allah Umma ki yafemin wlh babu yanda zanyi ne inajin tsoron kar na....." Katseta Umma tayi da cewa “karkije me? Meye ya faru Zainab yayi Miki wani abu ne?" Ajiyar zuciya tayi tace “Aa Umma babu komai" numfashi Umma ta daidaita tace “ok to gobe da safe kizo gida tunda shi bashi da hankali bare mutunci zaman gidan nasa ma kin daina" wata ajiyar zuciya me ƙarfi Zainab ta saki cike da farin ciki tace “da wuri ma kuwa Umma" tana aje wayar ta fara haɗa kayanta ranta da zuciyarta wasai tace “Allah zai rabani da ƙaya"
Shi kuwa ya gama yanke hukunci da kansa yayi dressing gurin da taji masa ciwon ya kwanta da sassafe kuwa ya ɗauki hanyar Garko cikin Sa'a ya tarar da Mal Tsalha ƙanin kakansu a zaurensa da Almajirai yana ganinsa yace.

“Ikon Allah mutumin birni kaine a tafe haka babu zato" murmushi yayi ya zauna suka gaisa Mal Tsalha ya dubesa da kyau yace “Mutumin birni ina marainiyar Allah Zainabu Allah sarki rayuwa jiya na gama kukan rashin mahaifiyarta Ubaidah mutuniyar kirki shikuwa Ibrahim saidai fatan Allah ya ƙwatoshi hannun wannan azzalumar mata daya aura sun cutar da Ubaidah matuƙa" shafa sumarsa yayi yace “Wlh Mal abin sai addu'a wannan mata ina ganin tsafi takeyi yanzu fa baba Ibrahim ko gidanmu baya zuwa yama ce ya yafe ƴar tasa bayaso. am dama Mal akan maganar Zainab ɗin ne ta kawoni......" Nan ya zage ya rinƙa shiryashi da ƙarairayi abinka da mutumin ƙauye take ya hau ya zauna yanata salati yace “Yanzu yarinyar nan haka ta zama ashe kaico Ni Ɗalhatu ina ganin rayuwa aikuwa indai da gaske kanasonta bazaka bar garin nan ba Saida igiyar auren Zainabu a hannunka yaron nan kaidai Allah yayi maka albarka ka taimaki maraici kayi zumunci"......
[9/13, 6:23 PM] AM OUM HAIRAN: *DEEN HOUSE*

*OUM HAIRAN*

_Free Page_

_Sakamakon bina PC da aketayi ana roƙona nayi sauƙi to nayi maimakon 300 na nrml group yanzu 200 ne VIP 600 yanzu 500 ne PC 1k yanzu 700 ne acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank or 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank ko katin waya MTN ta WhatsApp number 09013718241 ƴan Niger zaku turo kati Airtel ne._

Itako Zainab garin Allah na wayewa ta shirya barin gidan daƙyar Nafisa tabarta ta fita akan cewa zuwa zatayi ta dawo, tana samu ta fita ta ɗauki ɗan sahu sai gida da murnarta suka rungume juna bayan sun gama murnarsu suka zauna ta fara karyawa da dumamen tuwan shinkafa miyar zogale tanata zubawa Umma santi sunayi mata dariya.
A haka Abba ya fito ya ishesu yace “Aa Kakale dama gurin mahaifinki nake shirin zuwa akan maganar aurenki da ɗan uwanki Zaharaddeen"

Rufe idanunta tayi tana Murmushi sukayi dariya Umma tace “Ja'irai gara dai da kuka haɗa kanku Allah yasa yin na Allah ne" Bahijjah ce ta amsa suka tashi suka kama aiyukan gida Bahijjah na bawa Zainab labarin sabon saurayinta Zainab na dariya itama tana bata labarin yanda takejin Ya Zain a ranta, yini sukayi basu da zance saina samari su, ƙarfe uku saura Abba ya shigo suna baje a falo harda Ya Zain suna hira, yanayin shigowar Abban ne yasasu miƙewa dukkansu don alama ta zahiri ta bayyana ba lafiya ba hakanan Zainab ta tsinci kanta da faduwar gaba.
Umma ce ta katse shirun da cewa “Abbsnsu ya akayi ne munga yanayinka na bayyana tashin hankali" zama yayi a kujera yana furta “Innanillahi wa inna ilaihirraji'un" abinda ya ƙara ɗaga hankalin kowa dake gurin can ya ɗago yace “Anya Umma ba'a canza mana Shamsuddeen a asibiti ba?" Da sauri dukka suka kalleshi ya sharce gumi yace “Da yazo min da shirmensa naƙi aminta yanzu haka yaje garko ya shiryawa Baffa Tsalha ƙarya da gaskiya harma me afkuwa ta afku" da sauri duka suka sake dubansa tare da cewa meye ya afku Abba?" Cikin tsananin jimami yace “Baffa Tsalha baiyi bincike akan gskyr lamari ba ya yanke hukuncin ɗaura auren Shansu da Zainab yanzu Alh Aminu ya kirani yakemin Allah ya sanya alkhairi bansan ta mece ba na tambayesa yake cemin ɗana Shamsu mana da aka ɗaurawa aure a masallacin juma'a yanzu....."
Chapter 6 · 0% Book details