← Book details Deen House Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 25

Sashe 22

Deen House Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙit Dad ya kashe System ɗin saboda faɗuwar da yaji abu yayi dubawar da zasuyi dukkansu suka ga ashe Deen ne ya zube a wajen nan suka tattageshi sai asibiti kwanaki sukayita tafiya Deen ko ya farko idan yaji ta tabbata shi da kansa ya saki Zainab saiya kama surutai yana tambayar mutane yaushe ne ya saketa me tayi masa ya saketa ko kuma ya rinƙa tambayar mutane wai shin ya haukace ne?
Tun abin baya damun Umma har ta fara shiga damuwa zuciyar ɗa da mahaifi ita da kanta taje garko tasa aka rinƙa roƙa masa Allah sauƙi da tawakkali gami da dangana ita kanta Zainab ba ƙaramin ƙoƙari akayi a kanta kafin ta cire damuwa a ranta ba ta kama karatunta da rainon Abdullah ka'in da na'in saiya kasance ko haɗuwa bata cika bari suyi dashi ba duk da cewar har yanzu daya ɗan samu sauƙi bai hƙr da kiranta da bibiyarta ba shine baya makarantar su baya gidansu idan kuwa yaji taje gidansu Umma jikinsa har rawa yake don yaje duk da idan yaje ɗin ma ba wata fuska yake samu ba, sau da yawan lokuta yana shiga take miƙewa ta fice tasha bar masa Abdallah don tasan bayan shi bashida wani issue da ita.

Bikin Bahijjah ne ya tashi lokacin Zainab ta gyagije ta zama babbar mace sosai Dad da Mama Sadiya suke jiƙata da Naira tunda ita kaɗai ce take kara kaina a tsakaninsu itama Mama Sadiya Allah bai bata haihuwa ba abin nasu kamar gado ita a fam ɗinsu haihuwa ce matsalarsu basu da yawa kuma basa haihuwa sosai basa wucce ɗaya ko biyu wasu ma da yawa basuyi ba kamar dai ita Mama Sadiyan.
Wannan biki anci masa buri a wannan lokacin ne kuma Allah ya haɗata da Dr Bature ƙanine gurin Hajiya Sadiya kyakkyawan mutum me cikar kamala da kyawun nasaba ga hatimin nasara ya zauna Asalin sunansa Aliyu Pilot ne ba mazaunin Nigeria bane a Canada yake da matarsa Hadiyyah shima kamar wasu daga cikin fam ɗin nasu haihuwa ɗaya akayi masa tun shekara goma baya yarinyar batazo da rai ba har yanzu Hadiyyah bata ƙara ba.

Ziyara yazo Nigeria bayan ya ɗauki shekaru a ƙalla sha biyar baizo ba, shine ya kawowa yayarsa ziyara ta bazata lokacin Zainab tana kitchen tana girki Abdallah dake da shekara guda yana parlour yana ƙiriniya ya shigo da sallamarsa Mama dake zaune tanata biyewa Abdallah ta miƙe zumbur tare da sakin wata ƙarar murna tace “Bature dama kaine Ni naji tsayuwar mota nayi tunanin masu gidan ne ko kuma Deeni ne?" Murmushi yayi har dimple ɗinsa ya lotsa yace “My Aunty kin manta dani ina kika samu Handsome Boy haka?" Daidai lokacin Zainab ta fito sanye da wando three quarter da riga airmless iya ƙugu caraf idanun Bature akanta tayi sauri cewa “Wayyoh ya Allah" da sauri ta juya kitchen ɗin ta ɗauko hijjab dinta ta fito cike da kunya.

Lokacin ya zauna yana ɗauke da Abdallah ta gaisheshi a kunyace ta wucce ɗakinta tana kiran Yanah me aikinsu nan ya dubi yayarsa yace “Wannan fah Yaya Sadiya?" Harararsa tayi tace “Ƴata ce" da rashin fahimta yace “Ban gane ba" bayanin Zainab ta shiga yi masa bayan ta gama ya sosa kai yace “Ina so in zaku bani" harara Mama tayi masa tace “Ɗan boko ka kiyayeni banason iskancinka" haɗe rai yayi yace “Wlh da gaske nakeyi inason ƴar nan taki kiyimin jagora gurin babanta Ni har Abdallah ma zaku bamu inason yara Yaya Sadiya"
Murmushi tayi tace “Wannan da kake ganinta bata sauraron kowa taƙi kula kowa abinda na fahimta mijinta takewa gashi babu aure tsakaninsu igiyoyin sun tsinke sannan na biyu naji Daddynta yana cewa ƙanin mijinta zai aurawa ita tunda dama shine asalin saurayinta...."

Please karki karanta in baki biya ba Nrml group 300 VIP 600 PC 1k acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin waya MTN ta WhatsApp number na 09013718241 ƴan Niger zaku turo kati Airtel.
[10/25, 8:40 PM] AM OUM HAIRAN: *DH*

Jinjina kai Bature yayi yace “kawai dai bazaki bani ba saboda ina daɗewa banzo Niger ba kuma Kinga ni seriously da gaske nakeyi yarinyar tayimin nayi tunanin ma budurwa ce, Please kiyi bakin ƙoƙari ina komawa gida zanyiwa Alh Babba magana kafin na tafi ayi komai a gama bazan wucce 2 months ba"
Kada kai tayi tace to ai Shikenan ka jarraba sa'arka kowanne bawa baya wuccewa rabonsa amma yanda naga Zainab na wulaƙanta duk wanda yazo gurinta shine yasa banji maka sha'awar zuwa ba, koda yake zan gwada yi mata magana zanso kuma zanji daɗi ka auri Zainab kaga idan da rabo sai mu ƙara samun kusanci tunda ni shekaru sun tafi na haƙura ma da haihuwar"
Cikin tausayin lamarin nasu yace “Ni kaina tsoro ya fara shiga jikina yaya tun haihuwar da Hadiyyah tayi har yanzu ko ɓari bata kuma ba idan lalura ce kanaji a ranka lalura ce bari ka nemi magani amma mu kusan mun zagaye Canada da ƙasashe da yawa kowanne Dr sai yace mana babu wata lalura kawai daga Allah ne

Fitowar Zainab cikin shirinta na tafiya makaranta yasashi miƙewa yace “Yaya ina iya tafiya da sauri Zainab ta kalleshi suka haɗa idanu yayi mata murmushin daya sanya gabanta faɗuwa tayi ƙarfin halin cewa “Haba dai tun yanzu, Mama tana yawan bani labarinka nakance mata Mama kin damu da ƙanin nan naki shikuwa bai damu dake ba Allah yasa ma kada jinsa yafi ganinsa...."
Murmushi yayi daya sanya gabanta faɗuwa yace “Nafi Mama damuwa kawai kinsan yanayin aiki amma yanzu zatake yawan jina da ganina tunda zan karɓa daga gareta"
Jinjina kai Zainab tayi tana tafiya tace “Allah ya taimaka yabada saa" har taje bakin ƙofar taji yace “zan iya rakiya Hajiya" juyowa tayi tayi dariyar data sanya wushiryarta bayyana tace “Haba dai wanda yayi tafiya me tsayi yana buƙatar hutu ka zauna ka huta Ni zanje sheka gidan Abbanmu zankai Abdul daganan zan dawo baya na shiga B.U.K kaga kuwa wannan gantalin na wanda bai gaji bane"

Shafa sumarsa yayi dake kwance luf ta buzaye yace “Ina iyawa Aunty Zainab Ni bana gajiya" yanda yayi maganar ne ya basu dariya dukkansu shima ya dara tace “Shikenan tunda ka dage amma banason kace Zainabu ta tara maka gajiya" murmushi yayi yace “Wata rana sai in rama" bata gane me yake nufi ba suka nufi waje dole sai motarsa suka shiga yaja suka fice daga gidan suka nufi Sheka a mota ta barshi ta jima sannan ta tuna tace “Lahh Nikam anyi sakarya Umma da bako fa nake ƙanin Mama ne yazo daga Canada shine yace zaizo ya gaisheku" Abba ne yace “Lallai kin cika sakarya" yana maganar yana miƙewa ya fice bai jima ba suka dawo da Bature idanunsa akanta yace “Abba Zeey ta manta ma dani a waje" dariya Umma tayi tace “Lamba ɗaya kenan ta ƴan shiririta kuma tunda ta shigo Banga uwar da tayi ba sai tsara yanda biki zai kasance"

Gaisawa sukayi da Umma Zainab ta tashi ita da Umma suka shiga ciki daidai lokacin Bahijjah amarya ta shigo sukaci gaba da tsare tsarensu can kuwa a parlour Bature ne yake zayyanawa Abba abinda ke ransa game da Zainab daidai lokacin Deen ya shigo ya bisa da wani mugun kallo yace “Anyi mata miji" da sauri Bature ya dubeshi shima Abba shi yake kallo ya mayar da dubansa ga Bature
Yace “Babu shakka kazo da babban al'amari kuma naji daɗi daka yaba da ɗiyata Zainab har kayi sha'awar sanyata cikin halwarka saidai kasan cewa duk da Zainab yarinya ce amma Shari'a ta bata damar zaɓen abokin rayuwarta a matsayinta Na Bazawara saboda haka na baka dama kaje ku daidaita kanku mu bamu yiwa Zainab miji ba"

Ajiyar zuciya Bature ya sauke yayi godiya sosai ga Abba a lokacin ne kuma Zainab ta fito tana cewa inada c.a ne fah a makaranta shiyasa na fito amma Kinga ina neman cinye lkcn a gida ga Abdallah nan Umma ya isheni da tsotso yaye shi nayi yau..." Salati Umma ta saki tace “Zainab wannan jaririn ɗan kika yaye..." Ficewa tayi tana dariya tana ganin Deen ta ɗauke fara'ar fuskarta tayi Wuf ta fice shima ya fice dake dama tun shigowarsa bai zauna ba, shima Bature mikewa yayi sukayi sallama da Abba ya fice.
A jikin motar Bature ya tarar da Zainab yana zuwa ya rufe ta da bala'i ta kuwa saki baki tana kallonsa yanata zuba masifarsa har Saida yaji bazata kaisa ba sannan yayi ƙasa da murya yace “Akanme zaki fara yiwa mutane jaye²n mutane wai har sun fara zuwa da maganar aure Zainab ki bari banaso idan ba so kike zuciyata ta buga ba...."

Dariya abin ya bata ta taɓe baki tace “Au dama wai akan wannan kake magana Shamsu? Toma banda dai abi irin naka meye ruwan biri da gada ko kuwa so kake na lalace a haka? To bari kaji Ni ban kawo kowa ba amma tunda ranka na faɗa maka zanyi maka biyayya na rayu babun baɗalahu bawan ba ƙanin, insha Allahu nikuma zan fidda miji nayi aure wala Allah na samowa Abdallah ƙani...."
Yakai hannu zai damƙota ta goce ta shige mota tana dariya takaici kamar ya kashe Deen ganin wannan mutumin da ta ɗebo yazo ya miƙa masa hannu ya janye hannunsa ya bar gurin Bature yabisa da kallo da tunanin to shi wannan ɗin waye kuma meye yasa daga haɗuwar farko basuyiwa juna ba?" Dake mutum ne wanda bai fiye shigar da kansa abinda babu ruwansa ba wannan tasa yaja bakinsa ya tsuke.
Chapter 22 · 0% Book details