← Book details Dangina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 14

Sashe 6

Dangina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka na fashe dashi lokacin da nagama kafanta sakon julabib aikuwq baifi satiba ka kira ka shaida mana yabar duniya ,dqga nan na shiga cikin kunci da damuwa wanda baya misaltuwa ,shikuma sanadiyar abunda ya faru ya daina shaye shayen miyagun kwayoyi,wata rana inq zqune zuwaira ta kirani ta ce idan babu damuwa tanason ganinan bankiba na tashi na shirya naje gidanta ananne take shaidamun tanaso in auri mijinta ,hqka ta dinga basa labari har izuwa kan dauri auren dake tinkarosu .

Tunda ta fara maganq yake binta da idanu wanda take kalarsu ta sanaja izuwa jaa kaman wuta na tabbata da zaka taba to saita konaka kasa magana yayi domin yama rasa taya zai bullowa wannan lamari shiru yayi kafun ya rungume yar uwarsa wacce kuka yaci karfinta yana rarrashinta saida ya tabbatar ta hakura sannan ya dauko wata daja ya fara fito da kayayyaki wasuma agogone zobbuna masu uban tsada hakan ya dinga janta da hira saida ya tabbatar ta sake sannan ya rabu da ita ya Nata tabbacin indai yana raye bazaayi auren nan a .

Bayan fitanta ya zauna shi kadai yqna nazari gaba daya abun ya kulle masa kai meyasa julabib bai fada masa wannan lamarin ba har ya rasu ,shin wani mataki zai dauka akan wannan mutum ai a cikin maye yake kuma ya dauka matarsa ce ,meyasa ammi ta dage akan auren nan kawai don basuda asali to tabbas yayi alkawarin saiya samo asalinsu kuma ya kawosu gaban Ammi koma mai zai faru ya faru bazai yiwu laifinsu ya shafesu ba ,haka ya dinga zancen zuci kafun ya yanke hukunci mai karfi wadda yake gani shine solution.

Anata ribibin biki wanda iya Ammi da zuwaira su suke kidansu suyi rawarsu ita dai ko a jikinta don batadauka ma aure zatayi ba ,rana bata karya saidai uwar diya taji kunya yau zaa daura auren Hafsat da Abdulmallik gaba daya hankalinta a tashe yake ta nufi dakinsa ,shida Nannata samu yasata a gaba yana zubq shagwaba tana kallo kaman julqbib dintane a gabanta kallon nanna yayi ya ce

Nanna na ta dan Allah kimun gwaten kuskus mana

Dato ta amsa ta tashi ta nufi Kitchen ,inda ta tashi nan hafsat ta maida mazaunanta ta kalleshi ta ce

Hab Yaya yanzu hakq mukayi dakai kamun alkawari bazqkq bari ayi auren nan ba gashi saura awannni shida a daura ,wlh aka daura auren nan mutuwa zanyi

No bazaki mutuba nayi mqgana da mama ta cemun batayafewa duk wanda yayi kokarin dakatar da auren shiyasa na yanke hukunci a daura auren amma hakan bawai yana nufin kin zama tashi bane

No yaya matiqr aka daura aure kqm ai aikin gama ya gama meyasa Ammi zatamun hakq meyasa shin wai menene asalinmu daga ina muke shin ammq batada iyaye ne bare sasu baki kodai cikin shegenmu tayi tq haifemu

Sam kunada asali kaman yadda kowa yake da nashi hasalima kunfi wasu bayin Allah asali karku sake sa zargin ko bakwada asali ko kuma bata hanya mai kyau aka samekuba ,ko daya ba haka zancen yake ba

Juyowa sukayi suna kallon Nanna da take rike da dan jaramin kwano a hannunta guri ta nemq ta zauna da sauri rai's ya iso kusa da ita ya kama hannunta ya ce

Nanna dama kinsan asalinmu kinsan suwaye mu meyasa kuka mana haka keda Ammi kuke boye mana mu suwaye sannaj kuce karmusa shakku a cikin zuciyarmu ai wannan dolene dan Allah ki fada mana mu suwaye

Girgiza masa kai tafara alamar bazasuji komai daga bankintaba ,magiya suka fara mata suna rokonta wanda hakan yadawo mata tilas ta shaida musu su waye kodan ta dakatar da auren dolen da zaayiwa Hafsat kallonsu tayi ta ce

Zan fada muku amma sai kunmun wani alkawari

Mun yadda komeyene zamu miki

Kubari ayi auren nan a watse tukunnan sannan kudau duk wani mataki da kukeso

Kqllon juna sukayi rai's ya jinjina mata kai ya ce

Mun Amince my nanna

Gyara zamqnta tayi tana ajiye flat din hannunta ta ce ..........

Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*

STORY &WRITEN

BY

ADAMA UMAR
SECRET PEN

07081940768

LOVE AND ROMANTIC STORY

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI

7️⃣

PAGE SIX

ASALIN AMMINKU

A garin bayelsa akwai wani attajiri mai kudi Alh Usama ,Alh Usama yana da ƴa guda daya tilo domin an jima ana haihuwa a gidansa amma yaran basa zuwa da rai ,cikin ikon Allah aka haifa masa ya mace duk da itama daga farko batayi kuka ba har ancire rai saidaga baya ta fara kuka nanda nan murna ta karqde dangi anata murna dake Alh usama yanada jamaa gashi yana kyautata wa yan uwa Alh Usama yana da kaninsa Abdulwahab ,shikuma Abdulwahab yanada yara maza sunkai hudu sai mace daya itace ta zama saar Aisha wato yarinyar da aka haifa itace Ammi ,sun an mahaifiyarta maimuna it a din yard asalin kasar Niger ce amma mahaifinta dang Nigeria ne shiyasa ta dauko kyawun mahaifiyarta ,Ammin ku tatashi cikin gata da kulawa ta dukkan bangare kama daga dangin mahaifi dana mahaifiya,haka akasa amminku a makaranta ajinsu daya da yar baffanta Asiya suntashi tare komai Alh Usama baya nuna warayya hakan yayiwa kqninsa Alh Abdulwahab dadi yafara shirin hada aure tsakanin amminku da yaronsa babba Inuwa ,lokacin da Amminku takai shekara goma shatakwas ta gama secondary mahaifinta ya fara mata cuku² sama mata karatun gaba da secondary nan dangi suka masa ca akan bazai yiwu yarsa tacigaba da karatu batare da aure ba Hakan ya damesa shiyasa ya samu Dan uwansa akan ya bashi shawara nan kuwa ya gabatar masa da bukatarsa na hada aure ,Alh Usama yayi farin ciki sosai ya dawo ya sanar da Mqimuna bataji dadiba domin hankalinta bai kwanta da hadin auren ba amma babu yadda ta iya haka ta hakura ,lokqcin da aka shaidawa Amminku batace komaiba ita dai damuwarta ayi auren kuma ta cigaba da karatunta na likitanci .

Wata rana kanin mahaifinta yazo shida Inuwa mahaifiyarta ta umarceta akan ta kai musu abunsha babu musu ta dauka ta nufi dakin baki tazo daf da shiga taji sunacewa

wato ina fada maka inuwa idan kasamu ka auri yarinyarnan shikenan duk kudin mahaifinta ya dawo hannunka da ita zakayi ammafani kana karban kudi a hannun mahaifinta idan shekaru sukaja ya mutu ta gajeshi shikenan kazamo attajiri

Wlh.da gaskiyarka baba nifa kasan wani abu idan mukayi aure da wasu shekaru zansa a kasheshi kawai itama bayan ta haifa mana yara saina kasheta yadda kudin nawane da yarana

Gaskiyanka ne inuwa kaga ka mallake komai kenan

Karar kofunan da sukaji a waje shiyasa sukai shiru da hirar tasu suka fita suna rokon Allah yasa baaji hirarsu ba ,cikin flower suka hangota sukai kanta da sauri suna mata sannu kallonta Inuwa yayi ya ce

Haa kanwata lafiya kuwa meya faru

Murnushi ta kago ta ce

Ina tahowa ne Ammi tace in kawo muku ruwa Shine nai tuntume na fadi

Ayya kanwata sannu kinsan kedin ba.kalar wahala bace shiyasa don haka idan mukai aure bazan barki kiyi aikin komai ba

Murmushin dole tai tana tina abunda taji yana fada tai qjiyar zuciya mai karfi suna cikin haka saiga Alh Usama suka karisa daga ciki

Dakinta ta nufa ta turo cleaner akan ta kwashe kwalaben ,tunda ta shiga dakinta take tinanin qbunda kunnenta ya jiye mata batada bakin da zata samu mahaifinta ta shaida masa wannan lamari ,to kota fadawa Amminta tane hakan ma taga ba mafita bane ,tina yadda sukai da mahaifinta tayi lokqcin da yake shaida mata maganar auren Inuwa akan tana da zabi dan batasonshi ta yanke hukunci zata samu mahaifinta ta shaida.masa batason Auren Inuwa a sokeshi ,hakan kuwa akayi da safe ta samu mahaifinta ta shaida masa batason aure amma yayi fafur yace kozata mutu sai anyi auren ,babu yadda batayi ba amma haka mahaifinta yaki ,dakinta ta shiga taita kuka ta rasa wace mafita zatayi kallon akwatinta tayi hakan ya bata idea ta gudu aikuwa babu watata ta shirya kayanta ta dauki kudin da tasan zai isheta taje ko ina a nigeria ta dauki A TM dinta bayan ta gama hada jayanta taji an turo kofa da sauri ta juya tqga Ammin tace rungumeta tayi ta fashe da kuka nan taita rarrashinta tana bata baki harta hakura ,suna cikin haka kiran Alh Usama ya shigo wayarta alamar yana nemanta tashi fitar da tayi kuwa yasa amminku ma ta fita ta juyo ta kalli gidan ta ce

Kayi hakuri Abbi bazan iya auren wanda yakeson yaga bayanka ba sannan zanyi tafiyar nan ne domin in tsiratar da rayuwarka da tawa idan da rabon zamu gana zamu sake haduwa

Haka amminku ta tafi tasha ta samu guri ta zauna kusa da wasu mata saitaji suna cewa ,

Kai ladidi yau zamusha tafiya daga bayelsa zuwa gombe nan kusa ne ai zamusha tafiya mai nisa sosai

Gaskiya kam nima na fara tinanin wannan tafiyar

Hakan da suka fada ya bata daman shiga motar gombe aikuwa babu jimawa motarsu ta tashi direct har gombe

Bayan sun gama tattauna tsakanin Ammi da Abbu sun yanke hukunci saidai ta fada musu kwakwaran dalilinta na fasa auren to zasu daina zance auren kwata kwata ,dakinta ta taho don ta kirata suji ta bakinta amma abun mamaki tqzo ta samu batanan a tinaninta ta shiga wani gurine a cikin gidan amma ina ta bincika ko ina batanan wayoyinta ma duk a kashe ,mahaifinta ta shaidawa nan suka fara bincikq gidan yan uwa da abokan arziki amma ina babu .
Chapter 6 · 0% Book details