← Book details Dangina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 14

Sashe 13

Dangina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aisha kun isone"
"Juyo bayanka Abba"
Juyawa yayi ya kalleta tana tsaye wayar dake hannunta ta fadi sai hawaye ,nan ta zube akan guiwarta ta fashe da kuka da sauri ya karisa kusa da ita ya kamota ya rungumeta ,a jikinsa yana ba kuka zakiyi ba Aisha ki godewa Allah daya sake sada fuskokinmu .

Manyan taburmai naga an baza a wannan tsakar gidan da aka malalashi da simiti ammi kan tana mamanta ,wayarsa yake dannawa babu jimawa aka dauka bai jira yayi magana ba ya ce "kayi sauri kazo yayarka ta dawo " dagowa ammi tayi ta ce
"Baba kana nufin mama ta sake aihuwa bayata" ,"kwarai ma kuwa ta sake haihuwa har guda biyu ma ,abubakar da rakiya ,uta rakiya tana gidan yar uwarki asiya tace mu tana tsoron taimaka mana saboda babanta amma bazata bar rakiya a wahala ba "
"Waini Babba mai yafarune kuka sayar da gidanku kuka dawo nan da rayuwa "
"Labarine mai tsawo ,tun bayar tafiyanki Abdulwahabu yake bani baki akan in kawo kudi akai gun malamai ayita addua ,haka na dinga bashi kudi nima kuma inatayi idan nayi istihara saina ganki kina cikin rayuwar jin dadi shiyasa hankalina ya kwanta ,kasancewar na yadda dashi shiyasa na sake masa komai nawa haka yace ya kamata mu gina masallaci saboda mahaifiyarmu ,bankawo komai a rainaba na yarda na sa hannu a takardan da bakomai ,ashe haintata yayi domin yaga mahaifiyarki tana da juna biyu bashi da gadona idan ya kashe ni shiyasa ya hada baki da lauyana sukamun haka ,watarana.kawai akazo mun wuta wuta in tattare komai nawa gida.ba nawa bane da kadarorina babu yadda na iya haka muka hada dan kayanmu lokacin ana goyon abbakar saida muka fito zamu dauki mota aka shaida mana bayan suturar jikinmu babu komai namu a gidan ,hakan yasa muka fito saiga Abdulwahabu a nafe ya.fito mukasa kayanmu da komai yanata.bani hakuri akan zaiyi bincike mu zauna anan zai shigar da kara ,manyan abokanaina suna ta kirana kowa yayi wani yunkuri sai a nuna masa wannan sa hanu dole suyi shiru daga haka muka hakura muka mika lamuranmu ga Allah,"

Gyara zamanta tayi ta fadawa su baba dalilin barinta gidan da yacce tayi rayuwa hatta halin da mijinta yake ciki bata boye musu ba ,kuka Baba ya dingayi yana sawa ammi albarka ya ce

"Wato gidan nawa ma an rushehi an dawo dashi company"

Eh baba domin.munga tabbacin hakam baro baro a bakin company din

Rais ne yayi gyaran murya yace ina neman wata alfarman abani dama inyi bincike akan wannan lamarin ,babu musu aka bashi ,ya tattari maaikata suka nufi wannan company din suna zuwa suka shiga inuwa ne wanda ya gina company din dan haka suka nemi da akaisu office din C E O babu mata lokaci suka kwamusheshi suka nufi deppot din dake bayelsa suka mikawa mazashi saida yasha jibaga sannan ya kura mahaifinsa yayi masa bayani ,gaba daya hankalinsa ya tashi ya kira yan sanda jin inda dansa yake yasa sukace aikin yafi karfinsu ,karshe dai saida ya kawo wannan takardun shima yasa hannu ya mallakawa Alh Usama aka fiddashi a duk gidan da yake da komai su Alh usama suka koma anata sawa Rais albarka ammi tanajin alfahari da aikin danta koba komai ya share musu hawaye.

A bangaren maaikata kuma sun tsananta bincike sun gane cewa kiran da Aka yiwa Alh muhammad na karyane babu wasu baki da yayi sannan kotarsu ta fada cikin kogin bakin gada inda akasa manyan maaikata suka shiga cikin ruwa suka fito da ita ,basuga ko alamar kashi ba hakan ya tabbatar musu da cewa sacesu akayi akajefa motar cikin ruwa ,manager din da ya kirasa ya shaida masa bakin sunzo aka kwamushe da yasha jibga yake shaida musu shima wasu ne suka sace matansa akan saiya kirashi ,bashi da zabi shiyasa ya kirasa daga nan suka kama hanya suka fita ,tambayarsa sukai baiji wata magana da ya danganci inda suke ba ya ashaida Musu babu abunda yaji duk da tsufa ta kamashi amma dayaji bugu saiya tina address din da aka bayar akaisu Alh muhammad ,bibiyar adress din akayi aka tabbatar bana nigeria bane nan suka mika aikin wa sojojin south africa , shaaninku da zafin nama suke aikin bilhakki da gaskiya shiyasa baasha wahala ba aka turo musu da rahoton cewa wani babban mai arzikine yasa aka saceshi domin akwai wani aikin nuclear da zaizana masa ,taurin kan da yayine kuma ya shaida musu ya fita a kaidansu shiyasa sukasa a kamo musu shi suka hada harda bello ya dawo kaman mai taimaka masa ,yanzu haka zanen nuclear ta kammala har yabayar a kera masa ita inda yace bazai sakeshi ba har sai ankawo yaga babu wata matsala ,inda suke masa bara zana da idan bai musu aikiba zasu kashe iyalansa ,domin yana ganin iyalansa sannan yana sanin halin da suke ciki ,haka suka maida shi kaman bawansu yana yiwa manyan ƙasashe aiki su kuma suna karban kudi yanzu haka a yadda rahoto ta nuna daga bakin daya daga cikinsu gobe nuclear zata iso kuma ana tinanin nuclear na isowa yaga zanenta yayi daidai zai kashe Alh muhammad domin karya sake zana irinta , jin wannan rahoto ya gigita shi hakan yasa ya tara kowa da kowa yayi musu bayani nan aka fara adduoi da sallah ,shikuma ya tattara runduna mai yawa harda sojojin south africa suka nufi wannan tsobirin ,sun hadu da haradi masu yawa wanda dole saisun shareau kafun su isa haka suka dinga haduwa da manyan yan caskale da masu suburbuda duk suka kara dasu inda suma sunyi rashin jamaarsu sosai ,a gida nigeria kuma gaba daya tashohin television duk sun dauka anata sanar da abunda ke. Faruwa sai adduoi ake musu na fatan nasara ,masallatai tsangayoyi ,islamiyyoyi duk anatayi ,cikin ikon Allah da taimakon adduoi da suka samu suka kubuto da su daha hannun mugaye inda basu hakura ba suka dinga binsu da ruwan bindigogi amma suka tsallake ,su kuma aka tattara su nuclear kuma aka dan kata a hannun sojojim nigeria domin nigerian ne ya kerata hakan yasa aka karawa Rais matsayin bigeanty a soja inda kasa nigeria ta karade da farincikin ,gaba dayansu suka nufi bayelsa inda kowa da kowa na family ake tare ,Alh muhammad dai sai kallon wannan saurayi mai kama dashi yake wanda ake kira da Muhammad muhammad suna zuwa dama anyiwa gida waya ga tarin yan jarida nan da gidan rediyo suka fito a mota,ammi kam tun dazu sai murza ido take ko tana. Tinanin mafarkin da tasaba shine taleyi amma ina kaman ba mafarki bane wannan da gaskene bata tabbatar ba saida rais ya kama hannunta ya dankashi cikin na Alh muhammad ,hakan yasata wani suman tsaye wanda jamaa suka.yiyo kansu suna salati ,kici kici ta farayi da numfashinta tana salati .........

Share pls
[9/12, 7:58 PM] ADAMA UMAR (SECRET PEN): 👨‍👩‍👧‍👧👨‍👩‍👧‍👧👨‍👩‍👧‍👧👨‍👩‍👧‍👧👨‍👩‍👧‍👧👨‍👩‍👧‍👧👨‍👩‍👦‍👦
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*
👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👦‍👦

STORY &WRITEN

BY

ADAMA UMAR
SECRET PEN

07081940768

LOVE AND ROMANTIC STORY

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI

1️⃣5️⃣

Bsnda farin ciki babun da yakeyi gaba daya sai hasken camera yake tashi a wajen ya juya ya fito da Alh bello mijin nanna shima ya danka mata hannunsa a nata ,kukan dadi kawai yake tashi ganin abun bazai kareba yasa aka nufi cikin gidan Alh Usama , dama an gama shirye shirye da komai komai suka zube a baban.falo anata jajantawa juna ,karshe dai farincikin da ya watse sama da shekara 25 ya dawo cikin wannan iyali da salo na daban bayan an gama hajiya ta kalli Alh muhammad ta ce

Yana da kyau akaikuma masauki kuyi wanka kuzo kuci abinci

Sunkuyar da kai yayi yana tinanin ta ina zai fara bawa nahaifiyarsa hakuri domin tun dazu zulumin da yake kenan ,rarrafowa gabanta yayi ya kama kafanta ya ce

Hajiya ,kiyi hakuri da kuncin da nasaki ,kiyi hakuri da abunda na miki na rashin daidai ,hajiya naga tashin hankali kala kala asanafiyar bijire miki da mukayi ,munga rayuwa kala kala ,Hajiya ki yafemun ko zansamu farin cikina ya tabbata

Dagoshi tayi tana rike da hannunsa ta ce

Haba muhammad akan me zakace ka bijiremun da baka gudu da ita ba da zaku haifamun wadannan tsala tsalan jikokin ,koda kun taimaki wannan baiwar Allah da mijinta wanda suka dawo tamkar yan uwa a gareku ,karka damu karkaji komai najima da yafe maka ku tashi akwai wani part mai 2 bed room kuje akaiku can ,tashi yayi jiki ba kwari ,Maman ammice ta kira daya daga masu aikinta ta musu iso saida suka tafi ammi da nanna sai kallon juna suke ,ji suke kaman su ruga a guje su bisu amma saboda kunyar iyayensu sukai shiru domin ji suke kaman in suka tafi bazasu dawo ba ,hajiya da ta lura da hakan ta kira sunan ammi ta ce

Me kuke mana anan bazaku tashi kuje wajen mazajenku ba ,me zaku mana anan to maza ku tashi ku tafi

Dama jira suke nan suka tashi cikin jin kunya ,Abbakar yayi gyaran murya ya ce

To nidai hajiys diyar kinnan nakeso kibani zan aura ,zanyi na biyu da ita

Kulle fuskanta Nihal tayi domin dama ta jima da harbo jirkinsa tun daga kallon da yake mata ,Hajiya kam fatan alkhairi kawai tayi musu da sauran jamaan dake falon .

A bangaren su ammi kuwa saida suka shigo part din sannan kowacce ta shiga part din da aka ajiye mijinta a tare suka tura kofan ,Alh muhammad yana zaune bakin gado ya hada kansa da guiwa ,yana ganinta ya taso da sauri ,inda ita kuma ta tsaya daga bakin kofa ta kasa karisowa ,tasowa yayi ya ce

Meyake faruwa ne Aisha ,akwai matsace ,hankalina ya fara tashi da naga baki biyonba kodai kin sake wani aurene

Kuka ta fashe dashi tana mai rungumeshi ta ce
Chapter 13 · 0% Book details