← Book details Dangina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 14

Sashe 12

Dangina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salati sukai dikkansu suka nufeta ,Nihal ta daga masa hannu ta karbi mahaifiyarsa tana jijjigata ,saade kam da gudu taje ta dauko ruwa ta kawo aka fara shafawa hajiya ,Alh ne ya dago yana kallon Rais tabbas wannan daga ganinsa jinin Muhammad ne ,da badan yaga wanan da fuskan yarinta bama da yace muhammad ne ,zuciyarsace ta buga lokacin da qata tambaya ta ziyarce ,"shin ina muhammad din yake".hajiyace ta fara sambatu "Haba muhammad ka tafi kabar mahaifiyarka ashe zan sake gainika ,ashe Allah zai nunamun wannan ranar ,kai hakuri muhammad ka kawo ta zan aura maka ita basai kamun horo da tafiya ka barni ba na rokeka ",gaba daya jikinsu yayi sanyi da maganganunta ita dai Nuhal taji Hajiya tana maimaita sunan da tajima tana yawan fada wai yayanta to ai yanda aka bata labarin yayanta ai yaci ace shekarunsa yafi haka ,hajiya ce ta tashi ta kishingida a kujera idonta kur akan Rais hannu ta mika masa alamar yazo da sauri ya sake hannun Hafsat wacce take matikar kama da Ammi tazo gareshi ,kallo ta ksre mishi ta ce ," saurayi ina mahaifinka yake na sani ko astagfirullah bazanyiba saboda nasan ku jinin muhammad da matar sace ,ina suke ita suka shiga karkucemun sun mutu ban sake ganinsu ba ,waya fada muku inda kuke "ganin bazata daina tambayarsu banr ya ce "kiyi hakuri hajiya iyayena suna raye sune suka fada mana inda kuke yanzu haka ina tare da mahaifiyarmu ,mahaifina kuma yaje wani wajr aiki amma shima yana nan tafe zuwa gareki kiyi hakuri hajiya" ya fada yana jara rungumeta a jikinsa ,yana kuka kaman ransa zai fita ,Da sauri Nihal taje ta rungume Hafsat jin itace yar yayanta da ta jima tanajin.hajiya tana begensu ,kuka kawai.ya.karade falon harda ammi da take cikin mota wanda uta kukanta tana tinanin wani hali ke ciki ,hajiyace ta fara kokarin tashi ta ce " bari inje in tarbo surkuwata da irin wannan gagarumin ziyara da takawomun "dukkansu suka rufa mata baya suka fito daga main falo bude marfin motan da Ammi take ciki akayi ta daga kai wa zata gani Hajiyace take rike da marfin kofan hawaye ya wankr mata fuska ta bude dikkan hanayenta ,da sauri Ammi ta fito kaman wata yarinya ta fada jikinta suka sakr barkewa da sabon.kuka ,kowa yana sambatun abunda ke cikin ransa .

To bayan gari yadan sha kowa ya gama jimami nan Alh ya kalli Rais ya ce "wato kai abokina shine kaje ka dawo soja wacce bazan iya takara dakai ba kenan" dariya dukkansu sukai Ammi ta kalli hajiya batasan lokacin da ta zame akan kujeran ta durkusa ta ce "hajiya ki yafemun ,ki yafeni,nice sanadiyar rabaki da danki ,sanadiyar bijirewa iyaye mun ahiga kalubalen rayuwa kala kala ,har Allah ya kawomu wannan lokacin ',murmushi hajiya tayi ta ce " nagode miki ai kekam bakida laifi domin kome kikayi ai ke macece shidai muhammad din zai dawo daga aikin zaizo ya samen saiya fadamun dalilinshi na barina kuma bai waiwayenba ,baya tinanin halin da zanshiga na kadaici dan Allah ya tausayamun ya bani Nihal a lokacin da nacire rai da haihuwa"maganganun Hajiya sun daurewa ammi kai kenan tana nufin batasan muhammad ya rasuba ,kuka ta fashe dashi tana jinjina alamarin da wani ido zasu kalli Hajiya suce mata muhammad ya rasu me zai faru ,ganin zasu sake rikicewa ne yasa Alh ya ce "yanzu kam komai yazo karshe munq godewa Allah don haka yanzu zaa baku masauki ku shiga ku huta zuwa gobe da safe zaayi hirar rayuwa ,domin muna da tari Tambayoyi a cikinmu "Nihal ce ta tashi ta ce "nikam zan wuce da yar yaya dakina ,zan shiga dakina da ita nan zan mata masauki"ok kaikuma soja ka.dauki rundunarka ku je sashen mahaifinka dasu ,murmushi yayi ya ce to shikenan ,Ammi kuwa hajiya ta ce babu inda zataje tare zasu zauna ita da Nanna ,Nanna kam sai addua take Allah yasa ammi taga iyayenta kaman yadda akaga na Abbansu , bayan kowa yaje.ya huta a bangarensa ,washe gari da safe aka shirya lafiyayyen karyawa aka gayyaci kowa ya halarta anaci ana farinciki da kaunar juna saida aka kammala sannan aka koma falo ana bada labarin bayan rabuwa ammi kam labari ta fara basu tu daga kan wacece ita da asalinta da komai inda suka dinga mamaki ana samun yaya irinsu a duniya ,shiryawa sukai dukkansu suka tafi wajen Baba mai masa suka kaimata ziyara tayi mamako kuma tayi murnar saboda itama har perison an kaita wai an hada baki da ita aka sace dan masu gida daga baya kuma akan sakota ,ammi ta mata kyauta mai tsoka sannan suka sallameta .bayan sun dawo kowa ya nufi dakinsa ,Rais kam dakin ammi ya nufa yana zama ya ji sako ta shigo wayarsa ya bude ganin an bashi izinin bincike ne yasa ya fara murmushi .....

Share pls

*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]

STORY &WRITEN

BY

ADAMA UMAR
SECRET PEN

07081940768

LOVE AND ROMANTIC STORY

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI

1️⃣4️⃣

Juya wayarsa yake yanajin tsantsar farin cikin samun dama binciken da aka bashi ,sai juya wayar yake Ammi ta shigo ta sameshi ta ce " lafiya shiru baka fito ba?" "Eh ammi ina nan ina duba sakon daya sameni na bani daman binciko abba"murmushi ammi tayi tana gani kaman mafarki take wai dan da suka haifa shi zaiyi bincike akan abunda ya faru da mahaifinsu ,kallonshi tayi ta ce "nidai addua ta shine Allah yasa mahaifinku yana raye bai mutuba ,nidai har yau na kasa yadda mahaifinku ya rasu ,duk da cewa naga gawan da akacemun masune amma na kasa yadda" "ammi ki kwantar da hankalinki.in sha Allahu na miki alkawarin zai binciko gaskiya kuma in sha Allah Abbanmu bai mutuba yana nan da ransa" " innalillahi wa inna lillahi wa inna illaihirrajiun me kunnuwa na suke jiyemun mahaifinku ya mutu Muhammad dina ya mutu kuke boye mana gaskuya ". " Haba kakata yanzu dagajin ya mutu sai kice Abbanmu ne wani mai laifine fa muka kama ya mutu " " haba dan nan ai tunda jatumarka ta fara magana nake jinku dama nasan tunda kukazo akwai abunda kuke boye mana ku fadamun gaskiya me yake faruwa da Muhammad dina". Ganin zata rikice musu yasa ya kamata ya zaunar da ita a bakin gadon ammi ya ce " kinaso na miki bayani dalla dallah to saikin cika wannan sharadin na farko bazaki tayar da hankalinki ba ,na biyu kuma zaki tayamu da addua domin ke mahaifiyarsa ce ," kai kawai ta jinjina masa alamar zata cika sharafinsu yasa ya koma ya zauna ya bata labarin duk abinda yake faruwa ,hawayen idonta ta dinga sharcewa ,kallon ammi yayi ya ce ammi ku shirya dukkanku zamu wuce bayelsa Allah yasa muji alkhairi game da kakanninmu ,bqi jira wata wata ba ya fita ,wani file ya mikawa daya daga cikin soldier dinsa ya ce ka tatttara dukkan bayanan dake cikin wannan file din ka turasu headuarter ina bukatan cikekkan labarin meyq faru bayan fitansu Alh muhammad ,sara masa yayi ya karba ya shige masaukinsu .

Washe gari duk sun shirya harda Baba mai masa suka wuce bayalsa sunsha tafiya kam kafun nanms sukaje suka kama hotel sukayi salla sukaci abinci ,daga nan suka wuce anguwar ,suna shiga titin anguwar gaban ammi ya fara faduwa tana karanto adduoi a bakinta ,dayake da gps suke amfani har motansu ta faka a bakin wani nakeken gate fitowa sukai dukkansu suna kallon gate din daga gani baiyi kama da gida ba ,kallon daya daga cikin excot nashi yayi yamai alama da ya bincika ,hannu ya dauka ya kwankwasa aka bude ,wani sojane nan take ya sara masa ,nan sukai yan maganganu sannan ya juyo ya ce "this is note a house, is a big modern bakery company " kallon ammi yayi da hankalinta ya fara tashi kafun yayi magana ta isa gaban gate din ta ce "yallaboi nan gidan Alh usama ne mana hamshakin mai kudi "

"Sorry hajiya banjima da fara aiki ananba dan haka idan babu damuwa zan muku iso ku samu manager na company din ku masa tambayoyin kaman zakufi samun bayani daga gareshi" ,dakatar dashi Rais yayi ya kama hannun ammi suka koma mota kallonta yayi ya ce "ammi ki kwantar da hankalinki in sha Allah babu abunda ya faru yanzu ki bamu koda numbern mahaifinki ne mana "shiru tayi kaman mai tina wani abu ta dauki wayarta ta fara bincikawa kaman mai duba wani abu ta nuna masa wata lamba ,bai jira mai zaiceba ya kira numbern akayi Sallama ya amsa da sauri ammi ta kwace wayar ta ce
"Abba Abba Abbana ina kake ina kuka shiga"
Muryar da bazai taɓa mantawa a rayuwarsa ba ta shigo kunnuwansa tashi yayi tsaye yana" Aisha ,Aisha koba Aisha bace " "nice Abba nice wlh nice gashi nazo gidanmu bakanan Abba ina kuka koma ". "Eh Aisha mun tashi a wannan gidan amma kizo anguwar ogbia deden wajen babban madallacin jumaa idan kunzo zaku ganni ," ya fada yana tashi ya sharce hawayen dake zubowa daga idanunsa ya nufi cikin gida dama a kofar gida yake yana shiga ya fara maimuna ,maimuna fito kafun na baki labarin maza kiyi adduar shukur yau Allah ya amsa adduarki yanzu Aisha ta kirani tana neman inda nake na kwatanta mata da badan bani da mita ba da dakaina zanje bazan iya jiraba ,kafun ta gama jiran mai zaice zaice har takai goshinta kasa na godiya ga Allah ,ta bude dukkan kofofin hancinta ta rangaɗa guɗa , ta matsa kusa da randa ta kamfato ruwa ta zubeshi a kasa ta kurbr tsabar jin dadi ,gidan madaidaicine amma yana dauke da dakuna guda biyar gaba daya an mishi siminti a cikinsa hatta suturar jikinsu ta gani kasan ta masu karamin karfine ,yana ganin ta rikice yasa ya fita yaje deden masallaci ya tsaya ya kurwa wayarsa ido yana jiran kiransu ,yana tsaye ya shafe sama da minti 30 yaga wasu tarin motoci suna nufoshi dan matsawa gefe yayi yana cigaba da kallon wayarsa ,kiranshi akayi ya daga da sauri ganin wannan numbern yasa yace
Chapter 12 · 0% Book details