← Book details Dangina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 14

Sashe 10

Dangina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Da farko zan fara da gode miki akan irin halaccin da kikemun a rayuwa ,na sani ke macece kuma babu abunda mace takeso kuma take kishi sama da mijinta amma kika amuncemun na auri mijinki ,ki daina daurawa kanki laifin abunda ya faru tsakanina da shi Allah ne ya kaddara hakan ,sannan nima da laifina akan wani dalili zanje na kwanta na kwanta a dakin matar aure wacce takeda miji kuma kinga abunda ya faru kowa yanada laifi nagode sannan ina mai.baki hakuri akan kin auren mijinki danayi domin wannan shine kawai mafita kuma shine alkhairi da kuma daurewar zumuncin mu ,inaso kafun ki tafi zansa a loda miki kayan lefensa a mota akaiki har gida a ajiyesu.domin ni bana bukata na gode sosai ,yanzu zamusa Hankali akan nemo dangin mahaifinmu da mahaifiyata"

Kafun ka karisa fada ta rungumeta ta fashe da kuka ,saida tasha kuka sannan ta saketa ta kira maaikata suka fidda kaya aka mata rakiya .

Abangaren abdulmalik kuwa yana fita ya dagi bango ya ce

"Wlh karyane ,karyen kace bazan auri hafsat .ba tunda na kusanceta ban kara cin wani gindi mai ruwa irin nata ba don haka ko duk abunda na mallaka zai kare saina mallaki Hafsa"t ..........

Tofa wannan shine ana wata ga wata

Ya kune ganin raayinku akan fasa auren

Shin iyayen Ammi suna raye ko baban inuwa ya kashesu

Shin iyayen Abba suna raye ko kuma

Shin meya faru da iyayen su Rais suna raye ko dagaske sun mutu

Tofa maganar nanna da rais fa tana kankama

Ina jiran raayoyinku ,gaskiya banji dadin yacce kuka ƙi yin comment ba jiya

Share pls

*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*

STORY &WRITEN

BY

ADAMA UMAR
SECRET PEN

07081940768

LOVE AND ROMANTIC STORY

*Tsarabarmu ta yau*
*SIRRIKA UKU NA ZOGALE*

Kowacce mace tana da damar aiki da zogele ta hanyoyi uku wanda kowanne daga ciki yanada amfani wajen sauƙarda ni'ima nan take saidai abu ɗaya da zogale yake dashi shine ɓata ciki, yakan sanya gudawa a kowanne lokaci shiyasa yakeda muhimmaci kisan abu buyu, kafin ki fara na farko shine kada kisha da yawa na biyu kuma idan kinada ƙaramin ciki wanda be wuce watanni biyar ba kadama kisha, amma dai wani abu kuma daya kamata kisani shine bayan ni'ima dazai baki zai ƙara miki lafya,

hanya ta farko kiyi garin zogale wanda ya bushe a inuwa saiki zuba cokali ɗaya a ruwan zafi ki bari ya jiƙa saiki tace ruwan ki saka masa madara saiki sha,

hanya ta biyu ganyen zaki tafasa da kananfari sai bayan ya tafasa saiki tace ruwan sannan ki saka lefton kisha kamar yanda kike shan shayi,

hanya ta ƙarshe wato ta uku shine ki dafa ganyen saiya dafu saiki yanka masa farar albasa da tumatir kina iya saka masa mai da magi amma banda abu me yaji,

kamar yanda na faɗa asama kowanne daga ciki zakiyi kada kiyi da yawa sannan sai kina tare da miji zakiyi haka kuma ba'a yinsa asaka a firji don yayi saniyi, saidai kina iya sakawa shayin sikari ko zuma ko mazarƙwaila don yayyi zaƙi amma dai ba'aso yayi sanyi

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI

1️⃣1️⃣

Washe gari gidan ya tashi shiru babu kowa a falo kowa yana dakinsa sai nanna dataketa zirga akan daining ,da alama karyawa take hadawa ,tsayawa tayi kaman mai tinanin wani abu sai kuma ta juya ta nufi dakin danaga an rubuta rais a jiki ta kwankwasa ,qmsawa yayi da "shigo" babu fargaba ta fada ciki ta sameshi dagashi sai boxer ta lura wannan dabiar suce shida Julabib ,wani murmushi tayi wanda ya karawa fuskarta kyau ta shigo ya juyo ya kalleta ya ce

*Our Nanna kece da safiyar nan "

"Nice mana yaron Nanna nazo na sanar maka karyawanka yana jiranka karyayi sanyi "

"To shikenan Nanna amma dai ke zakiban a bakiko "

Murmushi tayi ta ce

"Duk yacce kakeso yarona "

Harta kama hanaya zata fita saita juyo ta ce

"Yauwa jiya kace na tina maka zamuyi magana "

"Eh tabbas zamuyi magana amma inajin nauyin maganar ne "

Dawowa tayi ta zauna tana tinanin meyake tinanin fada mata haka da yakejin nauyi ,kusa da bakin gadon ta zquna ta ce

"Rais ka daukeni kaman mahaifiya ka fadamun wani abune yake damunka "

"Tabbas nanna inada damuwa a cikin raina amma na rasa wazan fadawa ,shine na yanke hukunci bara na fada miki ko zanaji sanyi a raina ""

Murmushi tayi ta ce

"Tabbas nasan damuwar da yarona yakeyi akan wata ce ,fadamun wacece ta sace zuciyarka"

Murmushi yayi ya ce

"Nanna idan na fada miki bazaki damuba kuma bazaki dauken marar hankaliba "

"Ko kusa bazan maka wannan kallonba saboda ita soyayya babu abunda bata jawowa ,takansa mutum makanta idan idonsa ya rufe akan abu baya taba ganin muninnsa sannan talansa kurumta kome mutum zaiji bazai taba dauka ba so kenan "

"Nanna wata nakeso amma ta girmeni sosai watalil ma ta haifen "

Murmushi tayi ta ce

"Tome a ciki don ta haifeka kota girmeka ,ka manta manzon Allah S A W matarsa khadija irin auren da sukayi ai wannan ba aibu bane "

"Nanna kuma abun shine matar ta daukeni tamkar danta kuma tanamun kallon da ina mata kallon mama ,sai daga baya Allah ya jarabceni da sonta ,bangane so nake mata na.aureba sai yanzu "

Shiru tayi ta ce

"Yoni agun aikin nakune ka hadu da ita har kake gudun kartaki amincewa "

"Ah ah Nanna.,tun lokaci. Da na bude ido nake ganinta ,ta nunamun so irin wanda takewa danta ,ni ndauka da sonta nake da kallon mahaifiya sai yanzu na gane sonki nake Nanna dan Allah bansan da wace manufa zaki fassaraniba amma nidai gaskiyata na fada miki kawai ,ki amunce ki auren "

Wani gigitaccen mari ta daukeshi dashi wanda ita kanta batasan tayi hakanba taya Rais zaice yanasonta wannan wani irin mafarki takeyi ,shin kodai Rais ya fara shaye shayene ,yanzu dai tasan yana da shekara 25 ,ita kuma 45 amma yace ita yakeso ya aura ,innalillahi wa inna illaihirrajiun ,

Shi taketa maimaitawa harta bar dakin ta barshi sake da baki yana kallonta ,dakinta ta wuce ta fashe da kuka ,tana tino Julabib dinta ,tabbas tasan da Julabin yana raye da kofa wasa rais bazai furta mata soba ,kalmar da abakin mutum daya ta sanshi wato Julabib ,ko mijinga mahaifin julabin haka sukai aure bai taba shaida mata yanason ta saidai inyaga ranta ya baci yace mata masoyiya shikenan amma shine yau dan cikinta yake fada mata haka ,ta rushe da kuka.ta kifa kanta akan filo .

Tunda ta fita yaji ciwom fitarta fiye da marin da tayi masa ya gwammace da duka ta mishi ta fada masa abunda yake ranta da yafi masa ,to wai.meye laifinsa don yace yana sonta kuma har yanzu yana sonta kotaki.kotaso

A falo kuma Ammice ta fita ta kalli falon da alama dai Nanna ta fito amma bataji motsinta ba ,kallon dakin Hafsat tayi ta mataa kusa da kofar ta kwankwasa babu jimawa aka bude ta kalleta da rigar wanka da alama daga wanka ta fito ,kallonta tayi ta ce

"Hafsa"

"shiiiiiiii Kice my inlow "

"Dallah nikam ki.saurareni meyasa naga gidan shiru yau kaman ba kowa a ciki "

"Eh Ammi ,wlh yau nayi baccin da najima banyi irinsa ba shiyasa amma ai ganinan kije jiyiwa Brox magana ya fito muyi break ,wannan break din na musamman ne domin an jima baayi irinsa ba a gidanan "

Juyawa tayi da alama dai Hafsat murnar fasa aurenta takeyi ta nufi dakin Rais ta.sameshi yana zaune kaman me tinanin wani abu shigowanta ne ya dawo dashi hayyacinsa ya ce

I"na kwana Ammina kadde harkin fito "

"Eh nafito yanzu fa almost 10 naga baka fito ka karya ba "

"Oh nima ban jima da tashiba amma bari na shirya yanzu ina fitowa "

"Ok" ta fada tana jawo masa kofar ,kama ta juya sai kuma ta kalli dakin Nanna ta nufesa ta murda ,tun daga bakin kofa take jiyo sheshekar kukanta da sauri ta bude dakin ta ahiga tana shiga ta ganta kwance akan filo taje ta zauna kusa da ita tana tambayarta lafiya

Dagowa tayi taga hawaye sun wanke mata fuska abunda ta jima bata ganiba tun bayar rasuwar danta julabib ,a razane ta kalleta ta ce

"Meke damunki Nanna kodai bakida lafiya ne.? "

Kai kawai ta daga mata domib ji take kaman idonta zasu fado taabar sarawar da kanta yakeyi

Da sauri ta fita ta kira driver tace ya dauko mota sannan ta koma dakin Rais take shaida masa babu jimawa sai gasu tare shine da kansa ya rikota aka sata a mota sai asibiti .

"Gaskiya zan fada muku shine matar nan rashin hutu yana damunta sannan jininta yahau amma bada yawaba ,don haka tana bukatar kulawa ka kula da mahaifiyarka da kyau ya fada yana kallon Rais da yayi shiru yana kallon dr "

Fitowa sukai da Nanna da ammi suka shiga mota soja yana driving juyowa yayi ya ce

"Nanna ta ya jikin naki ?"

"Da sauki kawai ta amsa domin yanzu ko hada ido bataso suyi "

Murmuahi yayi ya ce

"Ammi kodai zamuyi Nanna ta aurene ko zaa samu wanda zaina sata farin ciki "

Dakuwa ta masa ta ce

"Idan zaayi saika hada da uwarka "

Juyawa yayi yana dariya.,ita kuma Nanna.kwafa kawai tayi batace dashi komai ba .

Suna dawowa suka sameta a falo da alama waya takeyi ganinsu yasa ta kashe wayar ta nufo gunsu tace

"Lafiya kuwa ammi meke faruwa ?"

Ganin yanayin Nanna yasa ta gane itace bata da lafiya zasu wuce da ita daki Rais yace sam saidai su dawo falo taci wani abu haka suka dawo yaje ya hado tea ya kawo mata ,kin karba tayi ganin zai bata a baki yasa ta karba a kafa kai taanasha a hankali kaman bataso ,sannan aka bata magungunanta tasha.
Chapter 10 · 0% Book details