← Book details Dangina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 14

Sashe 4

Dangina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaman yadda aka shirya Ammi ta kira aminan mijinta guda biyu ta sanar musu idan babu abunda zasuyi gobe zaazo neman auren hafsat dukkansu sunji dadi sunsawa abun albarka .

Washe gari

Da musalin karfe 6:09 na yamma Ta dawo daga makaranta cikin gajiya.ga shegen yunwa dake ibarta har wani jiri takeji ,gaba daya tayi nadamsr zuwa makaranta don babu abunda ta gane tsabar damuwa ,shigowa falon tayi ta ajiye hakarta tana kallon Ammita ce

ammi sannu da gida

Yauwa sannu yadai karatunne ya dawo daie haka

Eh wlh ammi gaba daya karatun ya bamu wahala

Ok kije gacab abincinki maza ki dauka

Tashi tayi taje ta dauki abincin ta dawo falo har yawunta tsinkewa yake tsabar yunwa ,kusa da ammi ta zauna ta fara cin abincin kallonta qmmi tayi ta ce

Yauwa Hafsat dazu DA hantsi magabatan yaron nan sunzo neman aurenki kuma anbasu.har ansa muku lokaci nan da 2 weeks ga sadakinki ma ankawo

Abincin da takecineya shiga kofofin hancintq aikuwa nan take tari ya sarketa ta fara ba gaggautawa ruwa ammi tabata sannan tarin ya tsagaita gaba daya idonta sun fito waje tsabar wahala kallon Ammi tayi ta kalli kudin ta ce

Ammi wani karya naji kunnuwa na sunamun kaman an kawo kudin aurena naji kince kuma da Abdulmallik

Kwarai ka kuwa kuma auren babu jimawa domin kuba yara bane kuma kunsan juna tunba yauba

Haba.Ammi wannan wani irin tozarcine ,saikace wata kaza zaku daukeni kubada aurena kuma nanda sati biyu saikace auren tattabaru gashi yayana baya gari zanyi aure gaskiya ammi bazan yarda ba

No na kira yayanki shima yana hanya nan da sati daya

Why Ammi meyasa zqki yanke hukunci batare da neman izinina ba kinsan yanzu ni nake da daman nemaw kaina miji fa

Eh kwarai na sani kuma na zaba miki ,wlh Hafsat idan baki maida hankalinki ki nitsu waje dayaba zakiga yadda zamuyi nida ke

Tunda Ammi tai mata maganar aure taji abincin ya fita a akanta cikinta ya toshe ko yunwarma bataji,tashi tayi ta nufi dakinta tai kuka son ronta tana cikin kukw kaman wacce aka mintsina ta firgita ta tashi dauko daya daga cikin akwatunan ta ta fara zuba kaya a ciki saida ta shirya tsaf sannan ta ajiye a cikin drower ta dauko babbar jakarta ta zuba wayoyinta da system da charger saida ta gama hada komai nata ta nufi bandaki tai wanka ta dauro alwala ta fito ta tayar da sallah ,bata tashi akan dardumanba saida ta gabatar da isha sannan ta koma kan gado tana saka tana warwara wata zuciyqrta tana shaida mata abunda take shirinyi ba abu me kyqu bane amma batada mafitar da yawuce haka da tayarda a mata auren dole ya lalata rayuwarta har abada domin matikar aka mata auren nan shi zaikaita har cikin wutan jahannama domin bazata bawa mijin hakkinsa ba kuma bazata masa biyayya ba gwanda kawai tayi iya kokarinta kar ayi auren don matikan akayi auren nan to an lalata mata rayuwa tana cikin wannan tinani taji anyi knowking izinin shigowa ta bayar tana share hawayenta ,Nannace ta shigo tai murmushi irin nasu na manya domin taga hawayen da take gogewa kusa da ita ta zauna tana dafa kafadarta ta ce

Hafsat shin amminki ta sanardake maganar aurenki da akasa nanda kwanaki jalilan

Wani murmushi ta kakalo tayi ta ce

Eh nanna ta fadamun

To wani hukunci kika yanke

Tinanin da nake kenan har yanzu ban yake hukunci ba shawara nakeyi da zuciyata

Kisani ba koda yaushe zuciya take baka shawara mai kyauba ,a wasu lokutan takan baka marasa kyau don haka inaso kiyi shawara da kwakwalwarki bada zuciyarki ba

Hakane Nanna nagode

Shikenan yanzu qbunda nakeso ki tashi kiyi istihara saiki kwanta Dafatan Allah ya nuna miki aurenki dashi alkhairine ko kuma akasin haka

Shikenan Nanna in sha Allah zanyu kokarin yin hakan

Mikewa tayi ta nufi bandakin dake cikin dakin Nanna kuwa harta mike tana kallon jakar da take shakare da kaya bude jakar tayi taga wayoyi d sauran abubuwan bukata da sauri ta.bude drower taga akwati ,yawancin kayanta babu ,jinjina kai tayi ta fita tana zancen zuci ,bayan fitan Nanna hafsat ta fito babu alamar ruwa a fuskarta ta ja jakarta ta dauki wayarta ta fara dannawa .

Gidan yayi shiru babu qlamar mutane da dukkan alamu kowa na gidan yayi bqcci tafiya take cikin sqnɗa da akwatinta akanta sannan ta bude kofar falon a hankali ,motarta ta nufa ta bude boot tq saka kayanta ta jinginq tana karewa gidan kallo wasu hawaye masu zafi suka wanke mata fuska ji take kaman ta fasa abunda tayi niyya amma ina zuciyarta ta kekashe bude marfin motar tayi zata rufe taji an rike marfin kofan da sauri ta fito don ganin waye ,zaro ido tayi ganin .........

Share pls

*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*

STORY &WRITEN

BY

ADAMA UMAR
SECRET PEN

07081940768

LOVE AND ROMANTIC STORY

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI

5️⃣

PAGE FOUR

Nanna a tsaye tana rike da marfin kofan fitowa tayi jiki a sanyaye Nanna tasa hannu ta zare key din motan ta kama hannunta suka koma cikin gida bangarenta suka nufa sannan ta zaunar da ita ta ce

Haba hafsat wani kuskure kikeson aikatawa ne ,shin kinaso tarihi ya sake maimaita kansa ne ,kinaso kiyi nadamar da haryau Amminki tana cikinsa meyasa haka meyasa

Wlh Nanna bazan zauna a auramun wannan mutumin ba karki manta da abunda yamunfa kuma yazo yace yana sona na fada masa banasonsa amma duk da haka ya dage saiya auren don haka gwanda in barmusu garin kowamq ya huta Gwanda tarihi ya maimaita kansa

Ba haka sakiyi ba yanzu idan kikw tafi idqn yayanki ya dawo me zamuce masa wani hali kike tinanin zai shiga ,yanzu kiyi hakuri har Allah ya dawo da yayanki lafiya saiki masa bayani yana da hakkin dakatar da auren ba shikenan ba

Shiru tayi tana tinanin maganganun Nanna tabbas a amaganarta akwai kamshin gaskiya don tasan matikar ta fadawa yayanta batason auren nan anfasa shima angama nan take wani kayataccen murmushi ya kamata ta ce

Shikenan Nanna bari zqn jira ba ammi tace yana hanya nanda one week ba
Kwarai yana hanya saiki masa bayani nasan shi zai fahimceki,nasan me Ammi take tsoro shiyasa ta amince da auren nan

Haba Nanna kenan kinq nufin kinsa asalinmu kumq kinsan tarihin su Ammi da Abba

Kwarai nasan komai amma nayiwa mahaifiyarku alkwari bazan taba fadawa wani wannan zance ba matikar ba bukatar hakan ta taso babu yadda aka iya ba ko kuma ita ta amince

Dan Allah Nanna kiban labarin asalinmu daga ina muke mu yan wani garine suwaye yan uwanmu ki taimaka

Bazaki taba jin wannan zance a bakinaba matikar ba wannan dalilai biyu dana fada miki ba

Shiru tayi don tasan tunda tace bazata fadaba to bazata fadaba .

Shirye shiryen biki ya kankama Ammi ta dage tanqtq hidima taje gurin gyaran jiki tayi booking amma tabita akan ta shiryq ta fara zuwa sam taki haka ammi tarabu da ita don tasan ita da kanta zata nema a mata kaman kullum suna zaune a falo jewelry's ne da yawa a gaban Ammi ta rasa wanne zata zabawa a marya itako gogar taku kaman bata falon ,zuwaira ce tai sallama ta shgo Ammi ta amsa cikin faraa da murmushi kusa da Hafsat ta nemu giri ta zquna ko kallona batayi ba dayake batada zuciya ta ce

Amarya bakya laifi ,kinsan gidan nan yadda ya dauku haramar kamshi kuwa tundaga bakin gate nake jin kamshi kowa yasan tabbas gidan nan akwai amarya

Banza tai da ita kaman batasan tanayi ba ta juya ta kalli Ammi dake murmushi ta ce

Yauwa Ammi dama Abdulmallik ne ya turoni ya ce wai ku shiryq gobe abokansa zasu kawo kayan aure da abubuwan da bazaa rasaba

ah masha Allah to shikenan Allah ya kaimu lokacin

Yauwa Ammi amarya bata fitar mana da anko bane don kinsan nice babbar kawafa

Ah gaki gata bi narasa wani irin aure Hafsat zatayi babu abunda take shiryawa ko gyaran jiki nida kaina naje na biya kudi amma nayi nayi taje sam taki ,nq tamayeta idan batason sintirin zuwa ne in kira wakiliyarsu tazo qmma ta ce itada ba auren soyayya zatayiba wani gyara zatayi Gatanan da ki mata fada idan zata gyara ta gyara ehen

Kallon Hafsat zuwaira tayi ta ce

Haba besty me kike nufi kenan don bakyason Abdulmallik shikenan bazaki gyara jikinki bw kumw bazayi shirin bikiba to idaj bazakiyiba mu zamuyi don haka zan samu sauran kawayenmu na school na fada musu kuma nida kaina zan tafi kwari in fitar da anko inke bazakiyiba ni zanyi

Dallah malama banason shishigi kawai kiyi sabgar gabanki ,tsabar rashin zuciya zaayi miki kishiya shine kik wannan rawar kafar kije can kiji da bikin mijinki babu ruwanki dani kowa yayi sabgarsa na jima da fada miki hakan

Ke Hafsat anya kinsan waye a gabanki kuwa zuwaira ce fa your pen friend me Inna ke nufi karkiga anbarki da hankalinki ki nemi rainqwq mutqne wayo sai yanzu na tashi na faffalla miki mari kinsan zan iya.koran kaiki gidan mijine zan.miki shegen duka ba damuwata bane

Haba Ammi ai abun yayi yawa ga mari ga tsinka jaka nasani ko kaffara bazanyi ba.zuwaira ita ta fadawa mijinta.akan ya nemi aurena nikuma basonshi nakesba aisaiya hakura amma kun nace ina rokon Allah.ya.dauki rayuwata kafun auren kowa mq ya huta

Ko kin mutu sai ankai gawarki gidansa kuma shine zaisaki a kabari

Ah ah Ammi Hafsat tana bukatar lallabine a ayanzu saikuma anusheta muhimmancin aurensu bawai a zageta ko.duka ba

Kirabu da yarinyarnan dani take zancen ba taga na barta bane ahiyasa take duk rashin kutumcin da takeyi

Mikewa tayi ta bar.musu falon don tasan da zata kara magana Ammi zata iya kai mata duka ita kuma bason abunda zai taba lafiyarta take.yanzu ba

Haka sukaci gaba da hirar biki Ammi tana fada mata shirye shiryen da sukeyi Nanna kam na gefe kaman ruwa ya cinyeta don tasan halin da ake ciki da badan ta dakatar da Hafsat ba ai da basuma san inda takeba balle su mata wannan maganar ko kumq sudinga shirye shiryen biki .
Chapter 4 · 0% Book details