← Book details Dangina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 14

Sashe 1

Dangina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read


DANGINA
*[AKA RABANI DASU]*

STORY &WRITEN

BY

ADAMA UMAR
SECRET PEN

07081940768

LOVE AND ROMANTIC STORY

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI

1️⃣

PAGE ONE

Zaune suke a falon kuna ganinsu kunsan suna tattauna abu mai mahimmanci ,yatsunra yana sarke a cikin na yar uwarta ta sake kallonta ta ce

Dan.Allah Hafsat ki amince da buƙata ta dan Allah bamuda wata mafita da yawuce haka babu abunda zamuyi mu goge lqifinmu a gareki saita wannan hanya pls ki taimaka

Kwarai Hafsat abunda zuwaira take faɗa miki gaskiya ne na roƙeki nima gani na durkushe akan guiwowina dan Allah ki amince da buƙatar mu

Fisge hannunta tayi daga yatsun yar uwartata sannan ta dauki jakarta ta kallesu kawai ta fita a gidan cikin hanzari sunanta suke kira amma ina ko juyowa batayi ba balle kuma ta sauraresu ,kallon zuwaira yayi ya ce

Mucigaba da jarrabawa insha Allah wataran zata amince kinsan sai mun mata uzuri yanzu tana cikin wani hali ,harna rasa da wacce irin fuska zan kalli hafsat wlh ,amma mucigaba da kokartawa insha Allah wataran zata amince

Hawayen dake zuba daga fuskarta ta goge ta ce

Haba hafsat kibani dama kibani dama mana mu goge babban tabon da muka miki ,ki amince mu cireki a cikin kuncin da kike ciki da bakin ciki

Tafaɗa tana kqra rushewq da kuka

Rungumota jikinsa yayi yana ban baki .

A banagaren hafsat kuwa Allah ne kawai ya kaita gida lafiya tana zuwq tayi park na motarta sannan ta fito ta nufi ciki gida ,tana shigowa ta hadu da amminta tana zaune tana karatuna alquran ta zare glass ɗin idonta ta kalleta ta ce

Wai hafsa lafiyarki kuwa ,gaba ɗaya yanayinki ya sanja wai me yake damun kine

Kwanciya tayi a kafadun wannan dattijuwa kana ganinta kasan mahaifiyartace ta ce

Wlh ammi na rasa ya zanyi dq zuwaira gaba day tasani a gaba akan wannan kudiri na ta nikuma nama rasa ta ina zan fara amincewa kai bazan ma faraba domin wlh ita da kanta zatayi nadamar faruwar wannan kudiri nata

Ajiyar zuciya Ammi tayi ta ce

Gaskiya Hafsat bazan boye miki ba ,kinsan nidai mahaifiyar kice ,bazan baki shawarar da bata gari ba ,a ganinq kuma a abunda ya dace ni kaina ina mai baki shawarar da ki amince da bukatar zuwaira da mijinta wannan itace mafita a gareki

Zubur ta tashi daga kan kafaɗarta ta kalleta Ta fara magana

Haba Ammi kema haka zaki fada,yanzu kina daya daga cikin mutanen da zasu goyi bqyan wannan lamari ,gaskiya Ammi tunda kince shawara ba umarni ba gaskiya bazan yadda da wannan kudirin ba .

Tanq gamq faɗar haka tq tashi da hanzari ta haura sama ,Ammi tq maida glass ɗinta tq ce

Yaro yarone Allah ya ganar dake kamqn yadda ya nunqmun faidar hakan .

Yau tana da lecture around 8:00 shiyasa ta tashi ta shirya da wuri ko break batayi ba haka tayiwq Ammi bankwana ta fita tana zuwa makaranta ta nufi hall taji ankira sunanta a hankali ta juyo ta kalli me siran sunan ta ,dafe goshinta tayi ganin zuwairace ta kira sunanta ,agogon hannu ta ta kalla taga batada lokqcin bqtawa aikuwa ta wuce ta shiga hall ɗin batare da ta tsaya ba,wuri ta nema ta zauna tana jiran su gama lecture ta fito suyi magana don yau babu wanda zai rabata da hafsat matikar bata amince da kudirinta ba ,To abangaren Hafsat ma haka gaba daya tinani ta tsaya yi akan maganganun da ake mata ita gaba ɗaya kanta ya kulle kuma kwakwalwarta ta toshe bata hango abunda ake faɗa ba ganin tinanin bqzai kaita ko inaba shiyasa ta kwatsar da zancen ta maida hankali akan karatunta ,gqba daya lecture ta dau zafi shiyasa gaba ɗaya a gajiye ta fito amma me tana fitowa tayi karo da zuwaira tana jiranta kallonta takeyi kafun tai magana ta kariso inda take ta ce

Dan Allah Hafsat bazan gajiya ba bazan karaya ba sannan bazan haura ba matikar baki yadda da kudirna ba ,mena miki meyasa cike tsanata kumq kike ƙyamata ,shin guduna kikeyi

Ohooo haba zuwqirq meya kawo maganar nan da zakice ina kyamqrki yaushe mukayi dake inq gudunki kawai don naki amincewa da kudurinki shiyasa zaki yanke mun danyen hukunci haka gaskiya kiyu hakuri ,karki manta yadda muka taso dake tamkar yan uwa kudubq irin shakuwa da kaunar dake tsakaninmu kisani inaso ya daure harga yayanmu ,amma ki sani matikar kudirinki ya cika zai iya zama sanadiyar tarwatsewar muamalarmu ,hakan zai dawo gaba mai tsanani a tsakaninmu kuma harga yayanmu ,inqso ki bari Allah ya zaɓamun duk abunda ya dace dani a rayuwata dan Allah karkiyiwa Alla shishigi

Shiru tayi gaba dayata rasa me zata faɗawa kawartata hakan yasa ta fashe da kuka ta ce

Da kinsan alkhairin da nake hangowa da baki faɗi wannan zantuttuka ba

Shin wani irin alkhairi kika hango wanda ni nakasa hangowa pls allow me to rest banason damuwa

Bata jira me zatace ba ta nufi parking space tashiga motarta tayi gidq ,jiki a sanyaye zuwaira tabar makarantar tana nazqrin shin taya zata fara bullowa da kawar tata ta amince da ita .

Tana zuwa gida bata tsaya bata lokaiba ta wuce daining domin wata azababbiyar yunwa da take damunta serving ɗin kanta ta fara sanna tafara cin abincinta hannu baka hannu kwarya ,tana cin qbinci sai hoton lokqcin rayuwarta ta baya ya fara dawo mata ,tana tina yadda ta kasance da walwala da nishaɗi da farin ciki amma yanzu ya zama tarihi ,ture abincij tayi domin saitaji duk abincin ya ginsheta ,tashi tayi ta nufi dakinta ta ajiye hakarta ta kalli wayarta na ƙara ,dauka ta duba tsaki tayi ganin sunan my besty ya bayyana ɓaro ɓaro ,jifa da wayar tayi akan gadon kafun ta fara rage kayan jikinta ta faɗa bandaki ,tana shiga ta tsaya kallon kanta a madubi tana duba shin ta kara ƙiba kota rage shin tumbinta ya karu koya ragu wannan ta kasance dabiarta ce saida ta gama karewa jikinta kallo sannan ta fara wankan ,tana gamawa ta fito daure da alwala ta dauko wata doguwar riga ta zura ta tada Sallah ,tana tayar da sallah saiga Ammi ta shigo da waya a hannunta ,kara wayar tayi a kunnenta ta ce

Ayyah zuwaira sallah take shiyasa bata ɗaga kiranki ba amma idan ta idar zan hadaku

Shikenan Ammin na gode

Saida ta idar da sallah sannan tai afduointa ta shafa tasawa kofarta kry ta kwanta a lafiyayyen gadonta tana kulle idonta tana sauraron bugun xuviyarta da alama bacci takeso ya dauketa ,wayarta ce ta fara ruri da alamar neman agaji tsaki tayi kibata duba ba tasan wace me kira shiyasa ta dauko wayartasata a silent ta maids kanta ta kwanta har bacci ya dauketa .

Ba ita ta farka ba sai misalin ƙarfe 3:00 na rana aikuwa a gurguje ta tashi tayi wanka Hafsat kenan sarkin tsafta haka take kaman wata agwagwa.kullum cikin wanka take ,bata fitoba saida ta dauro alwala sannan tafito ta shirya ta nufi falo ,tqna fita ta tarar da Ammi tadan mike kan sofer maakaciyarsu nanna tana mata tausa karisowa tayi ta rungume Ammin ta ce

Kai ammi yau nasha wahala gaskiya shiyasa dana dawo ban nemiki ba

Na sani kuma naje dakinki a rufe nasan bacci kike abunda nakeso dake ki tashi ki dauko mayafinki inaso ki kaini anguwa

Shikenan Ammi amma bazamu jirq mu gabatar da sallar laasar ba saimu fita

Shikenan bari inje indauro alwala saura minti 5

Tashi tayi ta nufi dakinta ,kallon.Nanna tayi.macece mai dan shekaru don a ƙalla zatakai shekara 40 gashi tanada nitsuwa ga ilimi ita kanta tashi tayi taga Ammi da Nanna domin batai aure bama me gadin gidan aka aura mata sannan ya rasu ya tafi ya barta da yaro daya tilo dagananbata sake aure ba ko zancen aure Ammin tayi tayi harta gaji ,ajiyar zuciya tayi tace

Nanna dan akwai abunda nakeso in tambayeki kinga.dai ke babbace watakil kema ki hango abunda na kasa hangowa

Jinjina kai tayi ta ce

Ina jinki hafsatu

Kaman yadda kika sani Zuwaira ƙawata tace kuma...

Kiran sallah ne ya katseta ta ce.

Kibari hjy nanna idan muka.dawo nida Ammi zanzo har dakinki inbaki labari bari inje inyi sallah

Shikenan to Allah ya dawo daku lafiya

Tafaɗa tana mikewa itama ta.nufi dakinta ,bayan sun idar da sallah kowacce ta fito da shirin fita sannan suka shiga mota suka fita a gidan ,suna ciki tafiya Hafsat ta kalli Ammi ta ce

Ammi wai ina zamuje ne sai tafiya mukeyi

Murmushi ammi tayi ta ce

Gidan zuwaira.

Fuskarta babu alamar wasa ,hakqn yasa Hafsat tadan haɗe rai ta cigaba da.drinving,dede kofar gidan taja tai parking Ammi ta kalleta ta ce

Me kike nufi kina nufin bazaki shiga ciki bane kome

Gaskiya Ammi ni bazani ba.kije ki kawa...

Bata karisaba.kawai taji saukar mari kan kuncinta ta dafe.ta juyo a mamakance tana kallon Ammi.

Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*

STORY &WRITEN

BY

ADAMA UMAR
SECRET PEN

07081940768

LOVE AND ROMANTIC STORY

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI

2️⃣

PAGE TWO

tabbas Ammi tana.wasa da yara amma tanada zafi.kuma ga zuciya macece tsayayya akan yayanta duk da ta.kasance ita ta rainesu amma hakan baisa tarbiyyarsu ta lalaceba ,batayi magana ba ta buɗe marfin motar ta fita aikuwa Hafsat ta rufa mata baya domin taga babu alamar wasa alamarin Ammi .

Zaune suke a falon dukkansu suna kan rug itq kuma Ammi tana kan kujera ta gyara glass ɗinta ta fara magana kamar haka
Chapter 1 · 0% Book details