← Book details Dacewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 24

Sashe 8

Dacewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon takaici ayeesha tasakar masa tana cewa,

Can you pls stop that right now before I change my mind nasa ayimin raping 'dinta once and for all nayi maganin matsalata na huta.

Wani 'dan iskan kallo ya watsa mata yana cewa,

Wlh nafiki zama 'dan iska muddin kikai ganganci ta6ata zakiga tsantsar tantirancina so gwara ki tabbatar kin tsaya a yanda muka tsara plan,
Neesah is mine alone and captain is urs.

Bude motar yayi yafito ya nufi motar neesah cikin farin ciki yana gyara agogon hannunsa.

Harara ayeesha tabisa da ita sbd Sam takasa samun yanda takeso akan neesah sbd wata stupid soyayyarsa.

Murmushi zeey tayi tace,

Kibarsa eshaa,idan munsamu buqatarmu tabiya akan neesah ni nasan yanda zamuyi dashi yanda ko sunanmu yaji saiya suma wlh.

Qaramin tsaki ayeesha tasaki batareda tace komaiba tsabar takaici ita yanxu duk ba wannanba tasamu ta zamo matar Jamaal 'din tukuna.

Shigarsa motar yayi daidai da isowar Jamaal gurin tsaf ya hango shigarsa motar
abinda yafi 6ata ransa kenan ta 'daukar masa maza a mota infact ace wai motarsa a hotel.

A fusace ya fito mota ya nufi motar
Idan ba Wanda yasansa ba Sam bazakace ransa a tsananin 6ace yakeba.

A zabure ta kalli Wanda yashigo motar..

Rantane yayi mummunan 6aci baqin ciki da takaici suka taso mata
Batasan sanda ta 'daga hannu ta wanka masa lafiyayyen mari ba
Amma ga mamakinta saitaga ya shafa wajen data maresa yana wani shu'umin murmushi.

Rantane yakuma 6aci ta kallesa a fusace tace,

Ka fitarmin a mota before I decide to do sumtin crazy.

Hannuwanta biyu ya kamo da sauri daidai Jamaal ya bude motar.

Saurin sakin hannuwanta yayi cikin sigar tsoro yana qoqarin fita daga motar.

Duk da bata tsoron Jamaal sosai ta firgita da yanayin daya samesu saidai batajin zata nuna masa hakan yaji 'dadi saita 'daure fuska tamau zatai magana ya fixgota waje tareda jefa mata key 'din motar ummi da handbag 'dinta yashiga motarsa harya fara tafiya saiya tsaya tareda qarewa Habib kallo tacikin glass yaja motar da mugun speed yabar gurin.

Mamuh💋

🌲 *R H F W F*🐄

_Don't forget to vote, follow and comments_
[6:02pm, 3/22/2018] Mamu Gee: _*DACEWA*_
_(when east meets west)_

_By_
_Mamuh geee_

*Viawattpad@mamuhgee*

*24-25*
Tunda take arayuwarta ba'a ta6a wulaqantata kamar yauba.,

Yau ita neesar da kowa ke rububice qaninta Jamaal ya wulaqnta cikin dubban mutane,

'Dagowa tayi zuciyarta kamar zata qone takalli Habib dake tsaye gefe yana sakar mata murmushin mugunta sbd buqatars data biya na yanda Jamaal yagansu.

Zeey ce ta qaraso da sauri takamata a kidime tana cewa,

Lpia neesah?
Ina motar?

Har lokacin kallon Habib take sbd wata sabuwar tsanarsa da qiyayyarsa datakeji.

Kuka takeson yi sbd zuciyarta dake mata zafi sosai amma tsabar taurin rai taqiyi sbd gani take taci baya idan tayiwa Jamaal kuka.

Tsabar baqin cikin ko motar ummi daya bar mata bata kallaba ta hau drop ta nufi gida tanajin tsanarsa shima nashiga ranta.

Harta isa gida tsanar Habib da Jamaal na kai kawo cikin ranta

A harabar gidan ta tarar dashi yana waya har lokacin fuskar nasa a ha'de take.

Kai tsaye shi ta nufa itama fuska a murtuqe.

Sarai ya lura da gurinsa ta nufo ya qara ha'de fuskarsa sosai.

Zata fara mgna ya 'dora mata oily eyes 'dinsa cikin tsuke fuska yace,

What?

Rantane yakuma 6aci tama rasa abinda zatai masa sai kawai ta juya a fusace tai cikin Palo.

Siririn tsaki yaja yanajin tsantsar takaicinta tareda qyanqyaminta na shigarsa cox yanxu yafara tunanin abinda yasa aka fasa aurenta shine shi aka maqala masa,.
Motarsa yafada yafice daga gidan.

Khadija dake tsaye qofar parlor tana kallonsu jitayi qirjinta yayi mata nauyi tayi 'dakinta da gudu tana danne hawayenta.

Neesah ta ganta taja tsaki tareda fadawa 'daki itama sbd kukan dake qoqarin zuwar mata itama tana dannewa.

Baki ummi dake zaune Palo tasaki tana bin qofofin 'dakunan nasu da kallo cikin mamakin abinda ke damun kowaccensu.

Tana shiga 'dakin ta sulale qasa tareda sakin kukan baqin ciki,
Tabbas yau taqara tabbatarda bazata iya Rayuwa da Jamaal ba sbd bazata iya 'daukar wulaqancinsa ba.

Da safe ummi hankalinta tashi yayi matuqa sbd da wani mugun zazza6i su duka suka tashi bama kamar neesah da har lokacin bata daina tsiyayar hawaye ba.

Khadija kuwa duk zazza6in dake cinta hakanan ta shirya ta gudu school sbd ganin neesah zai iya 'Dora mata hawan jini.

Zama ummi tayi tana kallon neesah jiki asanyaye tace,

Baby kidaina kukan nan ki sanar dani matsalarki nayi alqawarin magance miki ita muddin batafi qarfina ba.

Lumshe rinanun idanuwanta tayi hawayen dake ciki suka gangaro batareda ta bu'desu ba murya a karye tace,

Ummi in gaf da rasa numfashina,
Ummi rayuwata bazan ta6a samun farin cikiba muddin ina zaune da auren Jamaal akaina,

Ummi bazan iya Rayuwa da Jamaal ba sbd halayenmu sun nesa da juna,

Bu'de idanuwanta tayi ta 'dorawa ummi murya na rawa tace,

Ummi kisa araba aurena da Jamaal wlh bazan iya rayuwar aure dashiba.

Sosai jikin ummi yayi sanyi takalli neesah jikinta na tsananta sanyi tana karanto iya gskia neesah ke fadar zancen.

Baby tabbas yau da inada dama dana rabaki da Jamaal amma kasancewata mace na rasa wannan damar saidai ina miki alqawarin samun farin ciki matuqar kikayi hkr kikai biyayya.

Rintse idanuwanta tayi tareda zamewa takoma kwance.
Ummi ma jiki amace ta miqe ta fice.

Jamaal kuwa a ranar ya tunkari dady da zancen auren ayeesha kai tsaye dadyn yace ba yanxu ba.

Bai tsaya 6ata time 'dinsaba ya kira abban neesah yafada masa kai tsaye,

Abban neesah kuwa babu wani shamaki ya amince tareda alqawarin zuwa wani sati sbd ganawa da iyayen ayeesha.

Mamy dataji sosai tashiga damuwa sbd sanin halin neesah na girman kai bazai ta6a bari taji 'dadin rayuwar aureba gashi har za'ayi mata kishiya da wuri haka batareda tasan wani da'din aurenba.

Abba bayan yakira dady sunyi mgn shima dadyn ya amince ummice ta tsaya tsayin daka akan bata aminceba.

Sam Jamaal yanxu baicika zama gidanba sosai sbd Fushun da ummin keyi dashi akan mgnar.

Yau zaune suke Palo ummi na lalla6a neesah akan tasha magani inna rabi kuwa sai dariyarsu take.

Khadija Ce tafito 'dakinta tazo ta zauna kusada ummi duk ta hargitse ga wata uwar rama datai.

Kallo ummi tabita dashi cikin damuwa da tausayinta zatai magana inna Rabi tarigata da fadin,

Ummi 'yayanki dai lpia tayi musu qaranci musamman ma khadija duk tabi ta rame.

Hmmmn inna Rabi wlh ita khadija nama kasa sanin damuwarta har gwara baby ita nasan matsalar aurentane da jamaal....

Wata mummunar qwarewa khadija tayi wadda ta haddasa mata wani yunqurin amai ta sbd jin maganar ummi ta qarshe wai Jamaal mijin neesah.

Ummi dake zancen Sam bata luraba sbd hankalinta nakan neesah sake shan magani taci gaba da fadin,

Sannan yanxu dan tsabar rigima yace wani auren zaiyi kafin yakom......

Kusan atare neesah da khadija suka aware gaba 'daya ruwan dake hannunta suka xube had glass cup 'din nafashewa itakuwa khadija miqewa tayi ta nufi janyar bedroom ko gani batayi sai kawai su ummi ganin sukai ta yanke jiki ta fadi asume.

Mamuh💋

🌲 *R H F W F*🐄

_Don't forget to vote, follow and comments_

🌲 *R H F W F*🐄

_Don't forget to vote, follow and comments_
[6:28pm, 3/26/2018] ‪+234 802 437 1121‬: _*DACEWA*_
_(when east meets west)_

_By_
_Mamuh geee_

*Viawattpad@mamuhgee*

*26-27*

A rikice sukayo kanta ummi na kiran sunanta da qarfi amma Sam ko numfashi babu alamar yana tareda ita.

Shigowar Ahmed yasa ummi kallonsa a kidime tana nuna masa khadijar sunkutarta kawai yayi yafito su ummin suka biyosa zuwa asibiti.

Har suka fice neesah na zaune bata motsaba sbd baqin ciki da takaicin datake ciki na zancen auren na ummi tace zaiyi,
Imagine ace ita qaninta zaiwa kishiya dan ya rainata,
Baqin cikinta 'daya da auren nasa shine friends da sauran mutanen dasuka santa amatsayinta na babbar yarinya yanxu zasu riqa ganin itadin ma ba kowa bace a gun Jamaal 'din data raina,,,wato yafita zama 'dan rainin wayo,
To wlh bari ummi tadawo bazaiyi auren nan ba saiya saketa.

A zafafe ta miqe ta nufi hanyar bedroom taji an fixgota harsaidata fa'do masa cikeda tsoro ta 'dago idanuwanta suka shiga cikin nasa daya kafeta dasu,

'Daure fuska tayi tareda fixgewa da qarfi itama tana watsa masa irin kallon rainin dayake watso mata tace,

Karka kuma ta6ani dan ni ba sa'ar ta6awankace ba so better stay within your limits and karkayi tunanin 'dan na hakura nadawo nan yana nufin na amince da zama da wannan auren sunan....

Fixgota yakumayi ta fado jikinsa ya matseta tareda kallon tsakiyar idanuwanta cikin ra'da yace,

Banajin kinada jikinda yakai matsayin ta6awa a guna cox na girmi tunaninki sbd ni mutum ne mai qyanqyami and I don't like wat is common to people especially downgrade pple and you see this body of urs is like a common market tomatoes,
And maganan zuwanki nan I think its your problem not mine.

Tureta yayi daga jikinsa ta fa'di qasa kan hannunta ya bugu,
Magan ganunsa sun qona ranta matuqa kamar ita ya kalleta yace kamar tomatoes take a kasuwa.

Cikin qunan rai ta 'dago da idanuwanta dasuka ka'da zatai mgn ya tamke fuska tareda watsa mata kallon zallar qyama ya fice daga palon batareda tasamu ta fadi 6acin rantaba.

Hawayen baqin ciki da tsanarsa suka gangaro mata ta miqe ta fa'da bedroom tana jin kamar zuciyarta zata qone.

A asibiti saida khadija ta share 5hours kafin ta farfado kuma tunda ta farfado take hawaye ummi tayi lallashi da tambayar harta gaji amma ko magana khadijar taqiyi.

Sallamarsu Dr yayi bayan ya tabbatar musu da damuwa ce tayi mata yawa kuma tana gab da illatata matuqar ba 'a dau matakin rabata da itaba dan haka suje gida su rarrasheta ta fa'di damuwarta.

Har suka iso gida hawayen khadija sun kasa tsayawa gashi xuwa lokacin idanuwanta da duskarta tayi mugun kumbura sbd kuka amma takasa daina hawayen.

Hankalin ummi sosai ya tashi gashi suna dawowa sun tarar da itama neesah ta rufe kanta a 'daki tana kuka.

Zama ummi tayi bakin gadon bedroom 'din khadija tana kallon khadijar dake kwance ta rufe idanuwanta ga hawaye na gangarowa cikinsu jiki a sanyaye tace,
Chapter 8 · 0% Book details