← Book details Dacewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 24

Sashe 2

Dacewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waya take da amirah tana fada mata idan tahir yakawota ta tsayar mata dashi zatai magana dashi.

Jitayi anbude motar anriqo hannunta ba musu ta fito dan ta 'dauka tahir ne,

Tana fitowa saitaga Habib ta fizge hannunta da qarfi tareda tamke fuska sosai tana masa kallon qarin bayani.

Manyan lovely eyes 'dinta suka rikitasa yaji wata muguwar sha'awarta na neman haukatasa sai kawai ya fiddo handkerchief ya shaqa mata wani Abu a fiska nan ta sulale ya tarota jikinsa ya cicci6eta ya saka motarsa yabar gurin da sauri.

Mamuh💋

_*DACEWA*_
( _when east meets west..._ )

_By_
_Mamuh geee_

*4-5*
Taheer na zuwa motar yaga bata ciki
Yayi saurin danna kiran numbarta sbd tunanin ko gajiya tai da jiransa tabi wata motar ta wuce.

Ringin 'din wayarta yaji daga bayansa ya juya saiya hango wayar a qasa.

Dauka wayar yayi ya fara dubbuba harabar gurin cikin mamaki.

Amirah yakira tana 'dauka yace,
Pls amirah bby ta iso gida kuwa?

Nope, akwai wani abu ne?

No kawai dai nazo mota bata ciki and I called her phone but abin mamaki wayar a qasa na tsinta.

Gaban amirah yafadi ta tashi daga kwancen datake tai qasa da murya sbd kada wani yaji ayi making big issue out of it.

Kadaka fadawa kowa bari ganinan tafe gurin yanxu.

A sulale ta fice ta hau napep
Tana isa ta tarar dashi duk hnklinsa ya tashi idanuwansa sun qada jajir sbd tashin hnkli.

Sake dudduna ko ina agurin sukai basu gantaba harsun juyo sai amirah ta hango head 'din neesah cikin flowers ta ruga da gudu ta 'dauko gabanta na faduwa

Tahir kuwa jikinsa ne yaqara 'daukar rawa ya damqi head 'din yana jin tsoron abinda yake shirin faruwa dashi ace amaryarsa ta 6ata a daren 'daurin aurensu.

Amirah wayarsu asmy tahau kira tana tambayarsu ko suna tareda neesah amma kowaccensu tace aa.

Wayar mamy takira ta tambayeta ko neesah ta iso gida.

Mamy tace,
Aa, amma yakamata ace tadawo sbd fa dare yayi kuma dai Ai anriga angama dinner metake jira ne haryanzu.

Datse kiran amirah tai sbd batamasan me zata cewa mamyn ba.

Sake kiranta mamy tayi takasa 'dagawa sai abin yaba mamy mamaki sosai nan take ta zargi ba lafiya ba ta qara kiran amirar.

Murya na rawa amirah ta dauka.

Amirah lapiya kuwa?
Ina aneesah bata wayar zanyi magana da ita.

Hawayen datake dannewa suka gangaro mata ta bude baki murya na rawa tace,

Mamy wlh an nemi neesah an Ras.....

What? Mamy ta fada da qarfi kafin tace,
Kamarya amirah?
Ba mumbarku a gurin ba?
Ki kira tahir may be suna tare.

Mamy gani nan tareda tahir gaba 'daya ma baya cikin nutsuwa mun duba ko ina,mun kira mutane da dama amma duk ba'a gantaba.

Sulalewa mamy tayi ta zauna da6as a kujesa cikin tsantsar tashin hankali.

Saurin riqeta Anty Mamee tayi ummi kuwa wayar ta kar6a da sauri tana cigaba da sauraren bayanin amirah.

Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun,,,,
Shine abinda ummi ke maimaitawa cikin tashin hankali.

Wayar abban neesah takira yana 'dauka tace,
Yaya kadawo kuwa?

Alh sanda dake zaune a babban palonsa yana kallon news yace,

Eh tun 'dazu nadawo ina Palo na.

Fita tai da sauri ta nufi palonsa tana shiga ta fara fada masa halinda ake ciki.

Sakato yayi yana kallonta cikin rashin fahimta yace,

Aysha ki nutsu ba abinda zai faru bari nakira tahir 'din naji.

Yanda yaji yanayin muryar tahir yasashi tashi tsaye yace,

Tahir menake ji yanxu?

Abba wlh kaina a 'daure yake da wannan alamari sbd acikin mota nabarta dan na sallami wasu baqina sai kawai na tarar da batanan.

Kwantar da hnklinka tahir insha Allah za'a ganta.

Fitowa sukai dukkansu suka ha'dudasu tahir 'din sukai station.

Acikin daren 6atan Amarya neesah ya ya'du har gidansu tahir
Wanda wasunsu ke cewa tadai gudu ne bawani 6ata.

Kasa zama umman tahir tayi tafara kai kawo a 'dakinta cikin dogon tunani da wasi wasi,

Gskia bazata iya bari tahir 'dinta datake masifar so ya auri neesah ba sbd ga abubuwa nan marasa kyau na qara faruwa.,

Duk iya yanda ake tsammanin tashin hankalin to abin ya wuce nan dan tuni gidan bikin yakoma kamar gidan makoki gashi dare ya tsala sosai amma ba Wanda yasamu damar ko kwantawa bare rintsawa.

Duk iya yanda mamy taso daurewa kasawa tayi saidata zubarda hawaye sbd fargabar menene zai faru da aneesar dan bakowa zai yarda da duk abinda zai biyo bayan ganin nataba.

Ummi kam kuka take reras dan sosai Allah yasamata so da qaunar 'yar 'dan uwantaba.

Su Abba da dadynsu Jamaal tareda tahir 'din da babban amininsa jafar kuwa har gabanin asuba suna can tareda jamian tsaro cikin tashin hankali gurin nemanta.

Amirah kuwa tasha kuka har idanuwanta sun kumbura hakama su siyams acikin Daren duk suka iso gidan aka zauna jigun jigun jiran tsammani.

Koda akai sallar asuba da qyar kowa yatashi jiki a sanyaye sukai sallah
Har lokacin duk Wanda ka kalla idanuwansa a kumbure gashi har lokacin su Abba basu dawoba.

Qarfe shida na safe su Abba suka dawo zuciyoyinsu a dugun zume da tashin hankali.

Mamuh💋

_*DACEWA*_
( _when east meets west..._ )

_By_
_Mamuh geee_

*6-7*
Zama sukai a babban palon Abba suna sauraren bayanin da dady ke musu akan iya binciken dasukai.

Tahir kuwa yana isa gidan ya tarar da wani sabon tashin hankali dan kuwa ummarsa ta yanke hukuncin ko anga neesah bazai aureta ba sbd itadai hankalinta yakasa kwanciya da abubuwan dake faruwa.

Zubewa yayi gabanta ya riqo hannayenta cikin tashin hankali yace,

Umma dan Allah kadaki yankewa neesah wannan hukuncin sbd zai lalata rayuwarta data iyayenta

Umma yakike tsammanin mutane zasu dau zancen ace neesah ta 6ata kuma anfasa aurenta
Mutane 'dauka zasuyi wani abin banzar ta aikata har aka fasa aurenta kinga daganan samun miji zaiyi mata wahala kuma ma ba duk wannan ba Umma wlh ina son neesah kamar numfashina dan Allah kadaki rabani da farin cikina.

'Dauke kai tayi cikin tunanin abinda yafada to amma idan ta yarda ya auri neesah za'ariqa gulmar 'danta akan ya auri wadda ta gudu yawon banxa daren aurenta

Nasa mai sauqi ne duk yanda yakesonta bayan kwana biyu zai hakura ya nemi wata.

Girgiza kai tayi da sauri ta miqe tsaye cikin tamke fuska tace,

Tahir idan har ni ce na haifeka to tabbas bazaka auri neesah ba kuma wlh nagama magana yanxu kawunka zaije yasanar musu cewar mun fasa.

Quryar 'dakinta tashige tana gama fadar hakan tabarsa zaune yana rintse idanuwansa dasukai mugun ja.

_11:00am_

Ahankali ta bude idanuwanta dasukai mata nauyi ga kanta datakejin yayi mata wani nauyi.

Da qyar ta tashi zaune zaune tana kallon 'dakin tana lumshe ido sbd har lokacin basu gama bude mataba.

Gabanta ya fadi da qarfi sbd tuno abinda faru hartazo nan.

Jikinta takalla taga komai nata na jikinta head ne kawai babu
Ta tashi a hankali ta sauko gadon amma jiri ya hanata tsayuwa sbd jinta take kamar abuge ko tsayuwa bata iyayi ga idanuwanta suma sun kasa gani sosai.

Bango tafara bi tana tanga'di hartakai qofa takama handle da qyar ta bude tafito palo.

Zaune yake a palon yana kur6a wine a hankali yana waya da Umma tana sanar masa yazo maza dashi da Kawu zasu gidansu neesah su fada musu anfasa auren.

Wani shu'umin murmushi yasaki zaiyi magana sai ganinta yayi tafito tana bin bango.

Kashe wayar yayi tareda aje cup 'din hannunsa yataso yana murmushi yace,

There she comes my beautiful charming baby..

Hannu yakai zai rungumota ta 'daga hannu zata maresa amma takasa sbd ko gani batayi sosai hakama jikinta a mugun mace yake.

Sheqewa yayi da wata muguwar daria yana cewa,

Baby kadama ki wahalar da kanki bazaki iya komai ba you can't even stand dan haka kidaina qoqarin yin wani Abu.

Qara 'daga hannu tai amma sai hannun yakasa kaiwa.

Da qarfi ya fixgota jikinsa ya matse yana shinshinata yana lumshe idanu wani 'dadi na shigarsa.

Rigarta ya fara qoqarin zamewa ta tattaro wani 'dan qarfi ta turesa tana qoqarin zubewa sbd layi ta

Damqarta yayi sbd ransa daya fara 6aci gashi zata 6ata masa time harsai Umma tasake kiransa.

Matseta yayi ajikinsa yana qoqarin kai bakinsa anata.,

Zubewa tayi qasa cikin baqin ciki hawaye nafitowa idanuwanta sbd ko kadan batada qarfin qwatar kanta.

Binta yayi qasa ya cicci6eta ya yanufi bedroom da ita cikin zaquwa dan jin yake idan baiyi gaggawar kusantarta ba yanxu zai iya rasa ransa.

Zip 'din rigarta ya bu'de yafara shafar lallausau fatarta yana lumshe ido harya gangaro kan qirjinta yana 'dora hannu akan qirjinta yaji nutsuwarsa ta qara kwancewa jikinsa yadau rawa yafara qoqarin rabata da rigar ta tattaro qarfi daqyar ta turesa amma ko motsi baiyiba sbd qarfinsa da nata ba 'daya ba.

Lasarta yafarayi tako ina
Jin yana qoqarin rabata da pant 'dinta ta 'daga hannunta daqyar ta lalubo bedside lamp ta 'dagota da qyar ta kwada masa akai.

Wata raza nanniyar qara yasaki tareda zubewa gefenta a sume.

Fadowa tai qasan gadon ta rarrafa ta fito Palo da qyar takai kanta bakin fridge 'din data hango palon ta budesa da qyar ta lalubo robar ruwa
Bata tsaya la'akari da sanyin ruwanba ta bude robar ta juyewa kanta har fuskarta sbd tunanin ko zata rage jin mayen kota samu qarfin gudu.

Sanyin ruwa ya shigeta sosai ta girgiza kanta taji wani 'dan qarfi yashigeta hakama mayen ya rage.

Miqewa tayi da sauri ta nufi qofa ta fice daga gidan tafara sauri tana waiwaye gashi ko 'dankwali babu akanta ga rigarta saija da qasa take sbd yanayin 'dinkin bridal gown.

A firgice ya tashi ya dudduba yaga tabbas ta gudu

'Daki yakoma da sauri yashirya dan gwara yaje gida su sanarwa iyayen neesah sun fasa data rigasa ta tona masa asiri gwara yarigata.

Da mugun gudu ya isa gidan ko zama baiyiba suka 'dunguma zuwa gidansu neesah.

Tahir kuwa tunda garin ya waye bai fitoba yana 'dakinsa ya rufe kansa banda zubar hawaye ba abinda yake.

Mamuh💋

_*DACEWA*_
( _when east meets west..._ )

_By_
_Mamuh geee_

*8-9*
Saida tayi tafiya sosai cikin qarfin hali sbd har lokacin qarfin jikinta bai gama dawowa ba ga rigarta datai mata wani irin nauyi sai ja da qasa take.
Chapter 2 · 0% Book details