← Book details Dacewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 24

Sashe 22

Dacewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani takaicine yataso mata na yanda duk wannan yaqin da bala'in datake akansa amma Sam bata gabansa qarin haushima Sam ko kallo wasu lokutan bata ishesaba hardai da cikinta ya zube shikenan komai ya qara tsananta.

Danne takaicinsa tayi murya a sanyaye tace,

My captain Umma ce batada lpia shine nakeson naje for today's night kafin zuwa gobe idan Anty hadeeza tazo daga jalingo saita zauna da ita.

Daka tawa yayi kafin ya 'dago ya kalleta for about 10 minutes kafin ahankali yace,

Eshaaa,,,,eshaa bazaki ita dubota harsaikin kwana acan.

Qyafta idanu tayi hawaye suka gangaro ta marairaice zatayi mgn yayi saurin rufe ido yace,

You can go je ki shirya I will drop you....

No no captain zanje da motana after all yau banason ka fita sbd karka manta 'dazu kace kanka yana ciwo.

Light kiss tabashi a lips kafin ta fice tana ta6e baki.

Direct gidansu zeey tanufa ta tararda matar baban zeey 'din a palo tana fira da baquwa
A 'dage ta gaidasu tareda shigewa bedroom 'din zeey.

A kwance take daga ita sai gajeran wando da vest.

Zama ayeesha tayi tana aje handbag 'dinta tace,

Yau kuma naga waccen mutuniyarki a palo da baquwa ko me suke qullawa.

Tsaki zeey tasaki tana 6ata fuska tace,
Oho musu nidai abinda nasani nazamar mata qadangaren bakin tulu sbd bata haifeniba dan haka bazata mulkeniba
Haka nima ban ajiyetaba ba ruwana da ita matuqar bata shiga gonataba.

Qarfe takwas kiran Yusuf yashigo wayarsa lokacin yana zaune palon ummi yana cin abinci ahankali sbd hankalinsa na kan qofar bedroom 'din neesah dayake ayyana yau a 'dakin zai kwana.

Ahankali ya 'daga wayar tareda cewa,

What now?

Easy man,,,inason na tambayeka wani Abu akan sabuwar budurwata zeey?

Ka kirani ne kawai kamin wannan tambayar ko kuwa sbd ni inada abinyi yanxu dan naga alamar kai bakada.

Dariya yayi sosai har jamaal 'din zai kashe wayarsa yayi saurin cewa,

Sorry captain,,,
Tattaro nutsuwarsa yayi tareda zama serious yace,

Captain there's something very important danakeson fa'da maka but dole in person nakeson fa'da maka ita.

Gyara zama Jamaal yayi yana cewa,

OK gobe zanzo nasameka.

No no dole sai yau sbd am afraid wani Abu zai iya giftawa kafin gobe.

Lumshe idanuwa yayi cikin yanayi na mamaki yace,

Akan menene haka harka damu akan dole saina fito yanxu.

Kai tsaye yace,

Akan Wanda yayi injecting khadija ne...

Cikeda mamaki yace,

Meka sani akan hakan?

Saikazo kawai"""Yusuf yace tareda katse wayarsa.

Miqewa yayi tareda zuwa 'dakin ummi yayi mata saida safe ya fice.

Mama dake tsaye tuni tagamajin wayarsa da Yusuf ta shiga 'dakin neesah ta tararda ita kwance tana waya da amirah.

Saurin 6oye wayar tayi jin anbu'de qofa amma ganin mama ce saita saki ajiyar zuciya tareda tasowa ta nufi qofa tasa key tana cewa,

Badai jikin khadijar neba?

Juyowa tayi ta fuskanceta tace,

Yusuf yakira Jamaal yanxu yanason fada masa wani Abu akan mgnar khadija.

Nazari tayi kafin tace,

Let's pray kobai samu wani babban bayani akan yanda abin yakeba yasamu koda clue ne kinga munsamu damar bayyana komai koda babu evidence akwai yiyuwar ya yarda.

Wanka yayo yashiryo cikin qananan kaya dark blue ya shiga motar yafito gidan ya nufi hotel 'din.

Baqaramin mamaki yayiba ganin Yusuf 'din cikin nisha'di hankali akwance alhalin shi ya 'daga masa hankali.

Zama yayi tareda aje wayarsa da key 'din motarsa tareda tsuke fuska zaiyi magana Yusuf ya taresa da cewa,

Do you need anything,coffee, water, drink or...

Are kidding me,,,kakirani ne kabani coffee ne ko...

Calm down man.

Ransane yaqara 6aci yace,

Kagafa malam zan tafiyata.

Sorry dama inason sanarda Kaine I was the one investigating khadijas issue kuma nafara aikina tun 'dazu danaje gidan and masha Allah komai yazomin da sauqi but bazan fa'da maka komai yanxuba saida safe insha Allah.

Manyan oily eyes 'dinsa ya watsa masa yace,

Meyasa bazaka fa'damin yanxuba saiwani gobe.

Murmushi yasaki tareda miqewa ya nufi qofar toilet yana cewa,

Zaka fahimci dalilina nayin hakan zuwa goben.

Qaramin tsaki yaja tareda jingina bayansa da kujera tunaninsa na nauyi sbd baisan wa bincikensu zai nuna musuba.

Kasa komawa gida yayi sbd hankalinsa ya kasa kwanciya matse yakeda gari ya waye Yusuf yayi masa bayanin komai.

Kwanciya yayi a doguwar kujerar room 'din yaji sanyin ac yayi masa yawa sbd shi mutum ne mai yawan jin sanyi.

Tashi yayi Yakoma lafiyayyen gadon 'dakin ya kwanta tareda qudundunewa.

Shidai Yusuf yana zaune kan kujera yana aiki cikin laptop 'dinsa.

Qarfe goma sha biyu da mintuna ashirin da biyu suka shigo hotel 'din da farko securities sunso hanasu shiga amma yanayin shigarsu dakuma yanda ayeeshar taringa taunar chewing gum tana karkashe ido yasa sukabarsu sukashiga sbd tunanin kar****ai ne wani yakirasu gurinsa.

Su uku sukazo dukkaninsu a matse sai leloh dayake sanye cikin three quarter da armless shirt 'din maza.

Room 'din suka nufa kai tsaye bayan sun baro yaron leloh 'daya a mota batareda ya kashe motarba.

Rufe laptop Yusuf yayi bayan yagama tareda sakata cikin jaka yasaka cikin wardrobe ya rage hasken wutar 'dakin yashiga toilet.

Ahankali leloh ya bu'de qofar 'dakin suka shigo cikin duk da sunyi mamakin ganin qofar 'dakin a bude.

Rufe qofar 'dakin sukayi ayeesha ta zauna tareda crossing legs tana karka'dawa tace,

Leloh tayar mana da 'dan iska.

Matsowa zeey tayi gaban gadon tareda cewa,

No my Swt friend kin manta mutuwa cikin bacci ma tanada azaba after all a dazu damukai haduwar farko ya sace zuciyata dan haka bana buqatar ganin fuskarsa dan zan iya canxa ra'ayin kashesa.,,

Dariya leloh yasaki tareda zama kusada ayeesha yana kunna sigari yayi masa mummunan ja a furzo hayaqin yace,

Zeey Ashe akwai gayen dazai iya shiga wannan zuciyartaki?

Murmushi tasaki tareda kallon inda yake kwance tace,

Poor Yusuf,yashiga zuciyata sosai akaro na farko saidai gangancinsa na bincike akan matsalar khadija yaja masa sbd yanda yayi saurin Ganowar nan cikin lokaci qanqani zai gano mune muka kashe Ahmed,
Muka zubar da cikin dayakeso,
Mukaita ha'dasa da neesah,
Mukazo saceta qarshema dai zaigano komai kuma kaga qarshenmu yazo batareda muncimma buriba shiyasa gwara tun yanxu daba komai yasaniba mu aikasa kafin mu aiko neesah sauran masu rabon zuwa.

Tsaki ayeesha tasaku tareda miqewa ta fizge bindigar hannun zeey 'din ta saita gadon zata harba Yusuf ya bu'de qofar toilet tsoro yasata harba bindigar ba shiri cikin rashin sa'a sai a qafar zeey leloh yasa hannu ya fixgo ayeeshar da qarfi suka bar 'dakin da mugun gudu ko qofafi basu rufeba direban yaja suka bar gurin a guje.

Tun lokacinda warin hayaqin sigarin leloh ya bugi hancinsa ya farka amma jin abinda suke fada yasa yakasa koda motsi.

Da sauri Yusuf ya qaraso gadon tareda ta6asa yana kiran sunansa.

Ras yaga idanuwansa a bude saidai wani mugun ja dasukai Wanda shima saida faduwar gaba tashigesa dan yasan zuciyar Jamaal ba kyau idan ransa ya 6aci.

Saukowa gadon yayi jikinsa har wani mazari yake ya kalli inda zeey ke kwance tana qoqarin Jan qafa ta miqe cikin tsoro da tashin hankalin Jamaal,,
Tuni jikinta ya 'dau rawa tafara ja da baya.

Kallon fuskarta yayi tareda tariyo maganganunta ya 'daga hannu ya yanka mata wani gigitaccen marin daya sata zubewa qasa hancinta da kunnunta na kawo jini
Ya 'daga qafa da qarfi ya taka qafarda bullet 'din yashigeta tasaki wata masifaffiyar qara tareda sumewa a gurin.

Dafasa Yusuf yayi cikin jimami tareda cewa,

Karka fitarda fushinka da 6acin ranka gaba 'daya yanxu kabari harsai kasan suwaye take taredasu,

Nasanda zasuzo shiyasa nakiraka kaji kagani da kanka sbd ba lallaine ka yardaba da fa'da maka akayi,,

Neesah da khadija sunsan komai gamedasu shiyasa suke qoqarin ganin sun kawar dasu Wanda hakan ya hana neesah nuna warkewarta.

Ya mutsa kansa yayi da qarfi yanajin xuciyarsa na Neman bindigewa babu abinda yakeso yanxu daya wuce ya daddatse zeey amma dole ya barta ta fa'da masa partners 'dinta.

Juyowa yayi tareda janyo zanin gado ya 'daurota aciki yafito batareda tsoron wani ya gansaba ya bude Boot yajefata ya rufe yabar gurin da mugun gudu kamar zai tashi sama.

🤔🤔🤔gskia inaga zanje break 'din sati biyu sbd voters da comments sunyi qasa🤔🤔🤔

Mamuh💋

🌲 *R H F W F*🐄

_Don't forget to vote, follow and comments_

*_DACEWA_*
_(when east meets west)_

_By_
_Mamuh geee_

*_Viawattpad@mamuhgee_*

*60-61*

Direct gidansa dake qarshen street 'dinsu ya nufa

A gigice mai gadi ya bu'de masa gate sbd jin horn 'din dayake a masife.

Ko kashe motar beyiba ya fito ya bu'de boot ya jawota kamar kayan wanki ya nufi bq ya bu'de ya jefata batareda ya warware mata zanin gadonba ya rufe qofar ya juya yabar gidan da mugun speed.

Koda ya isa gida qin fitowa yayi daga motar ya kwantarda kansa jikin seat tareda rintse idanuwansa yanajin zuciyarsa na quna har lokacin.

Ya 'dau tsowon minti goma sha biyar kafin ya bu'de idanuwansa da har time 'din basu dawo daidaiba ya bu'de motar yafito.

Part 'dinsu ummi yakalla jikinsa na saki sbd ba abinda yake qaunar gani yanxu sama da neesah.

Kai tsaye can ya nufa batareda la'akari da menene time ba.

A rufe yaji qofar palon ya lumshe ido cikin damuwar kasancewar qofar a rufe.
Part 'dinsa ya nufa yashiga bedroom tareda tu6ewa yayo wanka ya zube a gado zuciyarsa na qara azalzala da tsananin buqatar ganin neesah duk da yasan Abu ne mai wahala ta manta komai dan ya lura da tanada kafiya akan abu.

Da qyar yaga gari ya fara haske bayan sallar asuba ya fito yashiga motarsa ya fice.

Koda ya isa a kwance ya tarar da ita tana nishi hawaye nabin fuskarta data kumbura,,

Qafar ya kalla ta kumbura sosai sbd har lokacin bullet na cikin qafar,,

Cikin tsananin tsoro take kallonsa sbd ganin sa6on 6acin rai a tattared dashi.

Saiti da gurinda bullet 'din ke ciki ya taka da qarfi ta saki wata razananniyar qara tareda qara sumewa daga zaunen.

Ruwan qanqara ya kwara mata a gigice ta farfa'do yakuma taka qafar da qarfi nanma saidata kuma sumewa ya kuma zuba mata ruwan qanqara.

Tana farfadowa ko motsi bata iyayi sbd azaba...

'Daga qafa yayi zai kuma takawa cikin kakkausar murya yace,

Tell me su waye partners 'dinki?
Chapter 22 · 0% Book details