← Book details Dacewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 24

Sashe 10

Dacewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Falon ya nufa da hanxarinsa danshi a tunaninsa ummin ce wani Abu ya sama sbd dady baya gari.

Tun a Palo yake jiyo kukan ummi tana kiran sunan neesah.,

Gabansa yayi mummunar fa'duwa sbd jin sunan wadda ake kira cikin kuka, qarasawa ciki yayi, yana arba da fasashin kwalabe da jini a tsakar 'dakin yaji qirjinsa yayi wani mugun nauyi da qyar ya isa qofar toilet 'din ya hangota kwance cikin ruwa bata numfashi
Idanu ya rintse da qarfi nauyin zuciyarsa na tsananta,

Patoranking half shirt 'dinsa ya cire tareda zura hannu ya fiddota ruwan jikinsa har wani rawa yake
Ummi da inna Rabi suka fito jiran ya kimtsota.

Rigar ya zura mata takai har gwiwarta ya sunkuceta bai tsaya bita kansu ummiba yasakata motarsa kafin sufito harya fita da wani mahaukacin speed da saura ka'dan ya tafi da qafafun mai gadi saida yayi wani mugun tsalle haryana fadawa cikin bokitin wankin dayake.

Fitowar Jamaal ba Riga 'daukeda neesah yasa khadija tabar bakin qofar tanaji qirjinta na cixo hawaye suka gangaro mata tai 'daki da sauri tareda rufo qofa ta sulale bakin qofar ta cusa kai cikin qafafu tana sakin kuka ahankali.

Ummi kuwa motar Ahmed suka nufa yajasu sukabi bayan Jamaal dake gudun tashin hankali.

Ahmed ma gudun yake cikin tashin hankali dan sai yanxu dayaga zai rasa neesah ya tabbatarda feelings 'din dayake ji akanta kuma a shirye yake daya fuskanci kowa yanxu akanta tunda batason Jamaal yazama dole arabata dashi.

_Kuyi Manage ba enough time_

Mamuh💋

🌲 *R H F W F*🐄

_Don't forget to vote, follow and comments_

_*DACEWA*_
_(when east meets west)_

_By_
_Mamuh geee_

*Viawattpad@mamuhgee*

*_I sincerely heart you too my Raheenat (heenat)_*

*30-31*

Emergency ward suka nufa kai tsaye Ahmed idanuwansa har wani yaji suke sbd Jan dasukayi ji yake zai iya rasa ransa idan wani Abu yasamu neesah.

Zaune suka tarar dashi yayi crossing legs yana duba wayarsa,

Sarai yasanda qarasowarsu amma ko motsi baiyiba bare ya 'dago ya kallesu.

Jigum jigum sukai suna jiran tsammani
Ahmed kuwa kasa zama yayi sai kai kawo yake.

Almost 2 hours suna jiran kafin wata Dr yafita room 'din yana zare coat 'dinsa,

Ahmed ne ya nufesa da 'dan hanxari ummi ma baza idanu da kunnuwa tayi tana jiran jin abinda zai fada,

Shidai yana nan still ko alamar kulasu baiyiba
Dr ya kallesa kafin ya maido da hankalinsa gurin Ahmed 'din yace,

Well numfashinta ya dawo saidai raunikan data jiwa kanta suma anyi dressing nasu all she really needs right now shine abari tasamu isashen Hutu,
Dan haka zaku iya komawa gida gobe da safe Ku dawo.

Ajiyar zuciya ummi da Ahmed suka saki atare kafin Ahmed yakalli ummi cikin marairaice fuska yace,

Ummi kije gida I will spend the night hia.

'Daure fuska ummin tayi tareda kallonsa tace,

Bakada tunani ne zaka ce zaka kwana anan kana namiji tana mace kuma matar 'dan uwanka.

Ha'de rai shima yayi kai tsaye yace,

Na za6i kwana anan ne sbd nine na cancanta,
Nine nake tsananin so da qaunarta Wanda bazan ta6a 6arin cuta kusantotaba sa6anin mijin nata da kike fada na tabbatarda shine sanadin koma meyene yasa takeson kashe kanta.

Idanuwa ummi ta zaro cikin tsananin tsoro tace,

Ahmed me kakeson fahimtar dani?
Idanma namiji ne dole zai kwana aikafi kowa sanin Jamaal ne ya cancanta.

Juyowa tayi gurinda Jamaal 'din me zaune zatai magana taga wayam basa.

Ta maido da kallonta ga Ahmed da alamarinsa yafara bata tsoro tace,

Muje gidan ka 'dauko inna Rabi ita zata kwana anan 'din.

Kai tsaye ya yarda sbd dama Jamaal 'din ne bayaso ya kwana tareda ita.

1:00am

Kasa kwanciya yayi ya zauna bakin gadonsa yana lumshe idanuwansa da har lokacin sunke qunshe da 6acin rai mai tsanani daya kasa tantance kona meyene.

Rintse ido yakumayi da qarfi maganganun Ahmed na qara yawo cikin kansa.

Me Ahmed ke nufi?
Raini ne wannan dazai bu'di baki yace yana son matar dayasan aurensa na kanta ko kuwa dama can soyayya suke in secret?

Saurin rintse ido yayi yanajin 6acin rai da fushi.

Zamewa yayi ya kwanta idanuwansa a lumshe yana fatar wannan tunanin na Ahmed da kowama yafita ransa.

Da safe da wani mugun ciwon kai khadija ta tashi amma haka ta daure ta girka breakfast sbd ummi datace tayi.

Komai ta gama ta ha'da nasu neesah a basket ta aje tashiga 'dakinta tayo wanka ta shiryo dan itace zatakai abincin duk da zuciyarta ba qaramin dauriya takeba gurin ganin ta danne baqin cikinta da damuwarta.

Doguwar Riga baqa tasaka tareda siririn yellow Vail ta fito ta 'dauki basket 'din ta nufi 'dakin ummi.

Zaune ta tarar da ita a gado ta gaidata tareda cewa,

Ummi zan kai musu breakfast 'din daga can inason naje gurin saloon.

'Daga kai ummi tayi sbd yanda kan ke mata ciwo itama na rashin bacci da damuwar data kwana da ita jiya akan bala'in dataga na shirin afkowa tsakanin 'yayanta dan Abinda tagani jiyan a idanuwan Ahmed ya tsoratata sosai hakama tasan tsaf Jamaal ya dame Ahmed ya shanye fagen taurin rai da zuciya mai tsanani.

A hankali ummi ta bu'de baki tace,

Ki gaidaminsu kafin na qaraso anjima Insha Allah.

To,,tace tareda ficewa jiki a sanyaye.

Tana Sanyo kan motarta wajen gate din gidan daidai zeey zata shigo amma mai gadin ya dakatar da ita akan neesah batanan.

Tsayawa khadija tayi tareda sauke glass takalli zeey ba 'daurewa ba sakewa tace,

Neesah na asibiti tun jiya idan xaki ne muje can zani.

Shiga motar zeey tayi tana mamakin yanayin khadijar sbd yanda take ba wata walwala atareda ita.

Har suka isa ba Wanda yayi mgn
Tanayin parking suka fito atare suka nufi 'dakin gaban khadija sai tsananta nauyi yake duk taqara taku guda na zuwa 'dakin.

Har lokacin barci take Inna kuma na zaune tana gyangyan'di.

neesah zeey ta nufa kamar zatayi kuka tana cewa,

Neesah Allah ya sassauta miki wannan jarabawa.

Ameen inna race tana karbar kayan hannun khadija.

Ido khadija ta kafawa rigar Jamaal dake jikin neesah tanajin karyewar zuciya da hawaye na yunquro mata.

Abincin inna ta 'diba ta fita waje dan taci
itama khadija juyawa tayi ta fice jiki ba kwari.

Miqewa tsaye zeey tayi tana shu'umin murmushi ta bu'de handbag 'dinta taciro wata kwalba tana dariya ta nufi abincin ta bude flask 'din ruwan tea tazube gaba 'daya abinda ke cikin kwalbar ta rufe flask 'din
Tana juyowa gabanta yayi mummunar yankewa nan take jikinta ya'dau rawa sbd khadija data gani tsaye bakin qofa tana kallonta.

Zufane ya yanko mata cikin rawar murya tace,

Um um um maganin.....

Wuceta khadija tayi ta zura hannu cikin basket 'din data kawo musu abinci ta 'dauki mukullin motar ta tafice cikin wani irin yanayi bawai dan bata ga abinda zeey 'din tayiba
Bata buqatar sanin koma meyene manufar zeey akan neesah dan tun kallon farko dataiwa zeey ta fahimci babu alkhairi a tattare da ita amma koma meyene ba abinda ya shafeta koma kashe neesah zatayi.

Yawu zeey ta ha'de tareda sakin ajiyar zuciya dataga khadijar ta fita batace komaiba alhalin ta ganta sarai.

Komawa kujera tayi ta zauna tana share xufa cikeda mamakin khadija.

Ahankali neesah ta bude idanuwanta daidai shigowar Ahmed tareda Dr da nurses guda biyu.

Kallonta Dr yayi yana murmushi yace,

Finally sleeping beauty ta tashi.

Ahmed dake kallonta cikin murmushi yace,

Dr inajin kunyanka fa sbd wannan sunan yayi maka nauyi.

Dariya sukai dukkaninsu ita kuwa lumshe idanuwa tayi tanajin wata irin matuwar jiki.

Fita Dr da nurse 'din sukai bayan ya duba file 'dinta yayi rubutu aciki.

Matsowa kusa yayi tareda kafeta da fararen idanuwansa hannuwansa a har'de cikin wata sabuwar lallausar murya yace,

Antynahhh..

Har cikin ranta taji yanda yaja sunan ta bu'de lumsasun idanuwanta ta 'dora akansa.

Kashe masa jiki idanuwanta sukayi ya tako ahankali ya zauna bakin gadon kafin yayi wata magana ummi da Jamaal tareda khadija data dawo suka shigo 'dakin
Kyakkyawar fuskarnan ta Jamaal a ha'de.

Kujeja inna Rabi ta jawo masa tana murnar ganinsa

Zama yayi tareda amsa wayarsa dake ringin kallo 'daya yayiwa gurin dasuke ya 'dauke kai bai kuma 'dagowaba yacigaba da wayarsa.

Ahmed ma 'dan tamke fuska yayi yana gaida ummi dake binsa da kallon tsoro da firgici.

Zee ma a ladafce tagaida ummin.

Amsawa tayi tana shafo kan neesah cikin kulawa tace

Baby Yaya jikin naki?

Kai ta 'daga alamar amsawa sbd batadaqarfin jiki ko ka'dan.

Inna Rabi kawo guri ta wanke bakinta ko tea ne tasha.

Da sauri inna tashiga toilet ta 'dauko bucket zeey ta 'dauko robar faro 'daya a fridge ta kama neesah ta tashi zaune ta wanke baki Ahmed sai sannu yake mata cikin kulawa.

Ummi da kanta ta hada mata thick tea ta matso tafara bata ahankali tanasha.

Zeey ji take kamar ta kar6i cup 'din tajuyewa neesah gaba 'daya tashanye.

Sosai tasha tea 'din hartaji tasamu qarfi sosai ajikinta.

Kallon ummi tayi ahankali tace,

Ummi zanshiga toilet fitsari xanyi.

To tace tana qoqarin kamata tace,

No ummi kibarshi zan iya.

Ahankali take takawa saita tsaya cak tana hadiye yawu
Dafe cikinta tayi tana qoqarin kiran sunan ummi amma kumfan jinin daya fara fita bakinta ya hana sai kawai ta zube sai ajikin Jamaal jini na fita bakinta tareda kumfa.

Ummi,Ahmed da inna atare sukayo kanta cikin tashin hankali saidai wani matsiyacin kallo da Jamaal ya watsawa Ahmed ya hanasa qarasowa sbd wata kyakkyawar runguma yayi mata data fa'do jikinsa.

Dr Ahmed ya fita da gudu yana qwalawa wani mahaukacin kira.
Ummi kuka tasaki tana kiran sunan neesah duk a rude.

A sace zeey takalli gefen khadija suka ha'da ido tai saurin 'dauke kai tana gyara tsayuwarta cikin hawayen tausayin neesah na kissa.

Khadija kuwa sinne kai tayi cikin hawayen dasuka 6alle mata na ganin neesah kwance jikin Jamaal tasamu kyakkyawar runguma daga garesa ga wani tashin hankali datake hangowa cikin idanuwansa duk da ba kowa ke iya gane fushinsa da 6acin ransaba bare tashin hankalinsa kasancewarsa miskili amma yau ita tana iya hango tashin hankalinsa..

Ficewa tayi da Sauri tana sakin wani wahalallen kuka
A kuma lokacin doctors kusan Biyar da nurses hudu sukayo 'dakin a gaggauce.

_Ayshart bellow naga saqonki na tabayar wayafi wani mugun hali,hassada,baqin ciki da zama maqiyin gaske a tsakain Ayeesha,,,zeey da khadija_
Chapter 10 · 0% Book details