← Book details Dacewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 24

Sashe 19

Dacewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune take tsakiyar gadon ta kwantarda kanta kan qafafunta idonuwanta qure kan qofa ko qiftawa batayi saidai sun ka'da jajir duk ta qara zabgewa duk Wanda ya ganta saiya tausaya mata sbd ta canxa kamar ba neesah ba.

Mamy zaune riqeda remote tana ragewa Ac 'dakin sanyi sbd jin jikin neesar kamar da zazza6i.

Ummi ce a gaba kafin mama sai khadija.

Gurin neesah ummi ta nufa ta zauna jikinta na 'qara sanyi hawaye na taruwa a idonta sbd fuskar Ahmed take gani data kalli neesah.

Mamy gaisawa tayi da mama kafin ta amsa gaisuwar khadija dake raku6e kusada qofa tana kallon yanda yau neesah 'yar gayu da class takoma banbancinta da mahaukata ka'dan ne duk sbd aikin maqiya.

Rintse idanuwanta tayi wasu hawaye masu 'dumi suka gangaro mata ta lumshe ido tanajin damuwar rayuwar data tsinci kanta aciki Wanda sai yanxu take tabbatarda Allah ya hanata Jamaal ne sbd wannan azabar da neesah ke ciki ba qaddararta bace dan qila da ita'dince to da tuni su zeey 'din sun kasheta.

Shiru ya ratsa 'dakin na 'dan wani lokaci saiga Jamaal yashigo tareda ayeesha data biyosa damin ganin 'dakin da neesah take.

Kallon tuhuma mama ta watsawa ayeesah kafin ta saci kallon gefen Jamaal dake duba magungunan daya Dr kudi 'dazu da safe asiya tai fuskar mamaki tana fadin,

Meyasa ayeesah 'dazu kikayi mamakin da'akace neesah na raye harkina cewa bazai yiyu ace wani ya rayu a wutar nan ba?
A maganarki sai inaga kenan kina tsaye abin yafaru ko?

Dukkaninsu a bazata zancen yashigesu suka 'dora idanuwansu akan ayeesha don jiran mezatace ita.

Jikintane ya'dau rawa wani mugun zufa ya karyo mata ta kalli Jamaal taga ya kafeta da idanuwansa qasa qasa ai nan dabara ta fara kwance mata tana rawar murya tace,

Um..um...am..nazo wucewa ne dana dawo daga asibiti naga.....

Katseta mama tayi da cewa,

Wow wat miracle harkin iya fita keda kikai 6ari kuma idan ban mantaba a ranar aka dawo dake daga asibiti ina fatan dai ba wata matsalar ce tadawo miki ba harkika fita zuwa asibitin.

Wani yawun ta ha'de tana Neman abin cewa saikuma taji maman tasake cewa,

Kuma Kinga qanwarki nan khadija kwanakin nan tana fama da rashin lapia amma taqi zuwa asibiti sbd tsoron shiga mutane ne da ita kozaki fa'damin sunan asibitin dake hanyar barin gari saina kaita.

Cikeda baqin ciki da takaicin mamar daya cikata tace,

Nibansan wata asibitin bayan gariba.

Zaro ido mama tayi tace,

Aa kuma kikace zaki asibiti ne kikaga ha'darin a bayan gari?

Zaro ido tayi sbd shaf ta manta da haka tafada da farko.

Ummi da mamy takalla taga kowaccensu tayi nisa cikin nazarin maganganun a ranta tace nashiga uku wannan tsinanniyar matar zata kaini karshe na tona asirina da kaina dole nayi gaggawar sanar da zee a 'dau mataki akanta.

Jamaal kuwa ficewa yayi a 'dakin yana jujuya zancen mama da yanayin da ayeesha tashiga akan tambayar.

Wani mugun kallo ayeesha tabi mamar dashi tana qissima irin mummunar kisar dazatai mata.

Khadija kallonda ayeesha kewa mamarta ya ta6a zuciyarta sbd tagane manufarsa saidai bata tunanin zata bari sukai ga cutatar da mamarta zata takawa cin amanarsu da munafurcinsu burki kowama ya huta.

Mamy da ummi ne suka tafi gida sbd mamy zata 'danyi barci rana ta huta shima sbd mamar ta matsa ne akan taje ta huta ita zata zauna da neesar.

Bayan fitarsu khadija ta matso ahankali ta tsaya gaban mama tace,

Mama ki fita duk wata harkar ayeesha da mutanenta sbd they are very evil and dangerous,
I know wat they are really capable of in fact they can kill without any hesitation so pls mama stay away from them banason wani Abu yasameki all abinda nakeso yanxu shine neesah tasamu sauqi nabata all the evidence nadanakedashi tayi facin 'dinsu kuma badan komai nakeyiba sai sbd Ahmed.

Dariya mamar tayi duk da tayi mamakin maganar khadijar sosai tace,

Karki damu khadija kawai dai yanxu ki sanar dani komai inason nasani.

Ayeesha itada.....
Shigowar zeey 'dakin tana kuka ya katse khadija fadar abinda tai niyya ta miqe tana kallon zeey dake kukan munafurcin tausayin neesah.

Babu Wanda yace mata qala harta qaraci kukanta ta miqe ta fita tana jin takaicin qin fitarsu khadija 'dakin.

Kallon mama khadija tayi murya qasa qasa tace,

Be careful mama these people are very very dangerous.

Fita khadijar tayi tareda rufo qofar ya rage daga mama sai neesah dahar lokacin ko motsi batayiba kuma idonta a bude.

Ga mamakin mama sai ganin neesar tayi ta rintse idanuwa hawaye sun gangaro.

Mamakine yakamata sbd Dr yace qwaqwalwarta bata aiki daidai to meyasa take hawaye alhalin batasan komaiba yanxu.,
Well idan kuwa neesah na hawaye it means akwai abinda take tunawa tana hawayen.

Gyara zama tayi sbd gwada tabbatarda zarginta ta yamutsa fuska tana cewa,

Wai meyasa haryanxu mamyn neesah bata dawoba nidaifa tsoro nakeji kar masu bibiyar neesah subiyo ta hanyar mamynta gashi ita bata hankalinta bare ta fa'desu a kar6o mamyn kafin itama su....kasa qarasawa tayi tace,

Allah karka bari komai yakuma faruwa da kowa.

Ta gefen ido ta qurawa neesar ido ga mamakinta saitaga idanuwanta a bude jikinta na rawa hawaye na ganganrowa da gudu daga idanuwanta.

Miqewa tayi ta qaraso gaban gadon takalli neesar da kyau tace,

Poor neesah,,,
Tell me neesah tun yaushe kika dawo normal sbd you can't fool me narigada Nagano ki.

Lumshe ido neesar tayi batareda tabada kantaba ta juyawa mamar baya.

Murmushi mama tayi tace,

You see neesah nasan matsalarki duk da khadija bata zayyane min komaiba but you see khadija nason taimaka miki amma bazan bar hakanba until nima zakiyi min wani Abu 'daya.

Idan kin amince I promise to stand wit you until you bring them down,
Koma meyene zanyi danki samu yanda kikeso just promise me zaki barwa khadija Jamaal ta aura.

Cikin wani sabon baqin cikin sunan Jamaal kawai data kira yasata miqewa idanuwanta na rinewa da qiyayyarsa datakejin tana qara kama kowace kusurwa ta jikinta takalli mamar murya a shaqe tace,

And why will I trust you bayan abubuwan dana gani da idanuwana suna faruwa da mutanen dana yarda dasu gashi na rasa Ahmed..

Kuka tasaki mai cinrai tanajin tsananin kewar Ahmed na cinta har cikin jininta.

Neesah keba maqiyiyata bace kuma banason kizama maqiyiyata shiyasa nake baki wannan damar domin dukkaninmu musamu abinda mukeso cikin ruwan sanyi after all koma mezakiyi you need evidence kuma this is the only option for you to get it.

Cikin kuka da takaici tace,

'Yarki na 'daya daga cikin mutanen dana tsana sbd she knows everything amma taqi fada gashi yanxu na rasa Ahmed bakusan ya nakeji ajikin zuciyataba jinake gwara na mutu nabi Ahmed sbd shikadai ne me sona and now I can never be with him.

Share hawayenta tayi tareda kallon mamar cikin ido tace,

Na yarda da shara'dinki sbd bana buqatar ko jin sunansa bare buqatar cigaba da zama dashi sbd zamana dashi ya qare har abada so you can take him all for your daughter but let me clear sumthing to you,,don't double cross me sbd zuciyata yanxu a bushe take nima zan iyayin komai ga duk Wanda yayi gangancin sukata,
And for you daughter zanji da ita idan nagama da manyan sbd wannan alqawarine na 'dauka duk Wanda keda sa hannu ko sanadin mutuwar Ahmed will pay ciki harda Jamaal,ummi kawai nacire duk da itama bazan iya cigaba da zama a gurintaba.

Idanuwan neesar take kallo tabbas banda qiyayya da bala'i babu abinda take hangowa a tsakiyar idanuwan.

Ajiyar zuciya tasaki tace,

Well let's say the deal is sealed..

Sabbin hawaye ne suka gangaro mata ta kwanta tana sheshekar kuka ahankali tana kiran sunan Ahmed ahankali sbd she's ready ta fight them koda zata rasa ranta.

Shigowar mamy yasa mama miqewa tana cewa,

Bari naje gida Nima na 'dan miqe.

Cikin murmushi mamy tace,

Ai kuwa angode sosai.

Tana fita a mota ta tarar da khadija bayan tagamo ganin likita dataje.

Harta tada mota ta hango zeey zaune cikin wata ash corolla8 tai saurin kallon mama taga hankalinta baya wajen taja jiki ba qwari sukabar asibitin.

Da daddare mama takalleta tace,

Khadija inason kifa'damin duk wasu bayanai dazaki bawa neesah idan ta warke.

Cikin kallon mamaki tace,

Mama karki shiga wannan alamarin idan neesah ta warke zan fa'da mata komai da kaina dan ko suwaye ma yanxu nafasa fa'da miki sbd banason kisa kanki a rigima.

No khadija kifadamin komai ina son nasani sbd inason protecting 'dinki takowane hali,
Inason nizan bada bayanin sbd koma suwaye su fuskanceni bakeba sbd karsu cutatar dake.

Jikin khadijar ne yayi sanyi ta miqe tareda cewa,

Zan fa'da miki komai gobe insha Allah mama.

Harsun kwanta taji takasa barci sbd zeey data gani a asibiti 'dazu.

Saukowa gado tayi ahankali tareda zura dogon hijab ta 'dau wayarta da kudin mashin ahankali ta fice.

Asibitin ta nufa ta tsaya 'daga nesa ka'dan da 'dakin.

Wata nurse taga tazo tashiga saikuma taga mamy tafito 'dakin.

Bataga fuskar nurse 'dinba saitaji tsoron abinda yasa mamy tabaro nurse
Ita kadai a 'dakin.

Ahanki ta lalla6a ta isa qofar 'dakin ahankali ta tura qofar.

Zaro ido tayi jikinta na rawa sbd ganin fuskar zeey sanye da kayan nurses ta na kallon neesar dake bacci tana dariyar mugunta ahankali.

Wayarta ta zaro ahankali ta danna video recording.

Sosai fuskar zeey tafito ta zaro wani qaton dogon syringe zata yiwa neesah allurarsa saikuma ta tsaya tana tunani alamar ta manta wani Abu saita ciro wayarta daga aljihu ta danna kiran.,,

Ayeesha gani nasamu shigowa na manta a ina leloh yace na soka mata.

Cikin qaguwa ayeesha tace,

Ki soka mata koma a ina kika samu mudai ta mutu mu huta konasamu kan Jamaal nikadai.

Kashe wayar tayi ta 'daga syringe din zata da6awa neesah wayar kiran mama data duba bataga khadijarba yashigo wayarta
A tsorace zeey tajuyo sukai ido biyu da khadijar ta zaro ido cikin tsoro sbd ganin recording take.

Da gudu khadija tabar jikin qofar zeey tabiyota da mugun gudu.

Cikin mugun tsoro khadijar ke gudu gashi dare yayi kuma zeey a mota take.

Daqyar tasamu mashin jiki na rawa ta hau tafada masa inda zai kaita.

Pls qara gudu takusa kamomu wlh zata iya komai idan takamani.
Chapter 19 · 0% Book details