← Book details Dacewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 24

Sashe 13

Dacewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wlh ayeesha karki ji da wai Jamaal nacan tareda wannan tsinanniyar mai girman kan nan kuma ina tabbatarwa jikina na bani wani Abu nacan zai wakanu a tsakaninsu and trust me da zarar yafara kusantarta kasuwarki ta fa'di wanwar.

Cikin tsabagen masifa da bala'i tace,

Wlh duk tayi wannan kuskuren saina aika har uwarta lahira bare ita,
Wannan wannan aneesar ni wlh uwarta ta haifomin masifa da bala'i wallahi,
Ji nake kamar zan buga tsabar bala'i da baqin cikin danake ji a yanxu
Wlh Jamaal yaci sa'ar ba qaramin so nake masa ba da wlh tuni nasa an masa kaciya amma wlh ko a yanxu idan yakaini maqura sai in danne son na 'dau mataki akan wannan jan ajin da basarwar dayakemin.

Zeey ma a qule tace,

Wlh ne nama fara gajiya da wannan bala'in kawai musa a sheqata zuwa lahira kowama ya huta.

Waya ayeesha ta 'daga ta danna kiran liloh riqaqqen 'dan ta'addar daya qware a iya kisa da fyade tareda sata.

Bugu 'daya ya 'dauka murya a tsananin a buge.

Kasa bayani tayi sbd tsananin baqin ciki da masifa dake cinta saidai zeey ce takar6a tai musu bayani itama duk da itama a qone take da 6acin rai.

Bo'de motar daduke jingine akayi da qarfi
A tsorace suka juya har zeey na wayar hannunta na faduwa.

Ahme......bata qarasaba yakai mata wani gigitaccen mari tareda shaqureta cikin tsananin masifa jikinsa har wata rawa yake.

A tsorace zeey ta matso tareda riqosa tana qoqarin 6an6are ayeesha da idanuwanta suka firfito sbd mari ga shaqa.

Wani mugun naushi ya sakarwa zeey 'din a baki saida haqorinta 'daya ya fa'do ta qwalla wata razananniyar qara sbd azaba dakuma ganin haqorinta 'daya a hannunta.

Daurewa tayi bakinta na jini tace,

Ka saketa idan yaso ka'dau ko wane irin hukunci daga baya bayan kaji dalilinmu nayin hakan.

Wurgi yayi da ita harsaida head 'din kanta ya fa'di ya rufesu da duka ido a rufe dan ji yake ko kashesu zai iyayi.

Saida suka daku kowaccensu fuskarta ta canza ma'ana kafin ya tsaya yana cewa,

Uhumm yanxu kubani hujjar Ku INA saurarenku kafin nakira Jamaal nafada masa yasan yanda zaiyi daku.

Ayeesha dago da idanuwanta dasuka ka'da jajir tayi sbd baqin ciki da dukan da tasha tace,

Munayin hakane sbd kai da ni kaina,

Jamaal ya tabbatarmin da har abada bazai ta6a son neesah ba hakama bazai ta6a rabuwa da itaba sbd karka sameta kuma yayi alqawarin azavtar da ita harsaita kashe kanta da kanta...

Zeey baki na jini ta kar6i zancen da cewa,

Nikuma neesah ta tabbatarmin da tabbas idan bada kaiba bazata iya rayuwar farin cikiba qarshema kashe kanta zatayi ta mutu kuma ko wancan karon data rufe kanta a toilet danta mutu Jamaal ne yaso raping nata taqi yarda shine yamata duka shiyasa taso kashe kanta a ranar
nikuma sbd bazan iya ganin neesah cikin wannan halinba yasa na yarda muka ha'da kai da ayeesha dan mu rabata dashi tasamu farin cikinta ita kuma ayeesha tasamu mijinta ita 'daya.

Sosai zancensu ya shigesa nan take tausayin neesah da tsanar Jamaal tareda qudirin 'daukar fansa suka shigesa.

Kallonsu yayi yace,

To meyasa yanxu naji kuna maganar sheqata lahira?

Da sauri zeey ta goge jinin bakinta tace,

Dama ba kasheta zasuyiba 'dauko mana ita ne zasuyi mu 6oye harsai ya yarda ya saketa kafin asakota kuma na tabbatarda kaima zakaso hakan dan haka pls kazo mu hadu mu qwato neesarmu daga hannun maqiyinta.

Dogon tunani yayi yaga tabbas wannan itace hanya 'daya dazai samu neesah,
Wani murmushin gefen baki yasaki tareda kallonsu yace,

Well I'm all in,.

Juna suka kalla suka saki wani murmushin qeta da samun nasara tareda qullin mummunar fansa dazasu 'dauka akan wannan dukan daya musu bayan sun gama amfani dashi.

Dinner dai watsewa tayi sbd tafiyar Amarya batareda tabari kowa ya qara ganinta ba sbd ba qaramin dakuwa sukaiba dan saida Ahmed 'din yakaisu akai musu dressing fuskokinci kafin yakaisu gida sbd sai washe gari ne za 'akai Amarya ayeesha.

Mamuh💋

🌲 *R H F W F*🐄

_Don't forget to vote, follow and comments_

_*DACEWA*_
_(when east meets west)_

_By_
_Mamuh geee_

*Viawattpad@mamuhgee*

*38-39*

_ina roqon masu bina nema daga farko pls su sassauta su nema a groups sbd gskia ba qaramin shiga haqqi bane sbd yayi nisa sosai a gurin mai rubutawa sai a nema daga wasu tunda baza'a rasaba.._

Koda su ummi suka dawo babu Wanda yatafi 'dakin neesah sbd sunsan zuwa wannan time 'din ta jima dayin bacci.

Neesah kuwa tuni bacci ya kwasheta cikin jikinsa sbd wata irin kasala da nutsuwa da haduwar jikin nasu ya sakar mata.

Gyara mata kwanciya yaji a jikinsa yana kallon sexy face 'dinta a ransa yana fadin,

Hmmnn stubborn girl sai shegen son girma.

Light kiss ya manna mata a wuya sai hancinsa ya shaqo sanyayen qamshin da fatarta keyi ya lumshe idanuwa sbd wani yanayin sha'awa dayaji na shigarsa.

Sake shigar daita jikinsa sosai yayi tareda 'dan matseta ya lumshe idanuwa batareda wani 6ata lokaci ba wani ni'imtaccen bacci yayi awon gaba dashi.

Zeey dai a daren ranar kwana tayi da mugun zazza6i ga fuskarta datayi sumtum sbd duka da haqorin daya fita daga bakinta.

Ayeesha kuwa a zaune ta kwana sbd Sam baqin ciki da tunanin 'daukar fansa ya hanata koda kwantawa bare ta rintsa.

Ta 6angaren Ahmed kuwa jiyake komaima zai iya akan neesah koda kuwa 'daukar ran Jamaal 'din ne sbd baya jin zai iya jurar ganin duk wani Wanda zai iya zama shamaki tsakaninsa da farin cikinsa ma'ana neesah.

*******
Very late suka farka shine ma yafara bude idanuwansa ya qurawa fuskarta dake wani sheqi ido ya shafo fuskar a hankali tareda zamewa ahankali ya fa'da toilets 'dinta.

Alwala yayo yazo ya gabatarda sallah yana idarwa ta bude idanuwanta akansa.

Fargaba,tsoro da tashin hankaline suka shigeta lokacinda ta gansa amma jin kai ya hanata nunawa sbd alamun dai tabbas tare suka kwana anan dakinta.

Jikinta tafara duddubawa sai kawai jinsa tayi ya 'doro kansa ta wuyanta tareda xuro hannuwansa ya Rungumota da wata irin muryar data kashe jikinta qasa qasa yace,

Kwantar da hankalinki babu abinda qaninki yayi miki bare ki kai qarata gurin ummi.

Juyowa tayi da sauri ta kalli fuskarsa ya kashe mata ido 'daya
Saurin sauke kanta tayi cikin wata muguwar kunyar da bata taba sanin tanada itaba.,

sakinta yayi ya fice yana murnushin ganin dama ashe tasan kunya.

Turus yayi ganin ummi da mamy a Palon zaune sai inna rabi dake kaida kawo.

Kallon mamaki ummi tafara aika masa tace,

Inna Rabi dama an bude qofar palon nan ne?

Cikin murmushi inna tace,

Aa haryanxu a rufe take.

Shafa kansa yayi tareda qarasowa gabansu yana gaida mamy cikin basarda kallon da ummi ke masa ya miqe yabar palon

Murmushi mamy tayi cikin farin tana kar6ar cup 'din kunun gya'da da inna rabi ke miqo mata.

Ummi kuwa miqewa tayi ta nufi 'dakin zuciyarta cikeda farin ciki.

Har lokacin tsaye take tsakar 'dakin tana mamakin zancensa,,,
Lallai Jamaal 'dinnan dama yana magana haka kuma ita yakewa zancen rashin kunya irin wannan.

Murmushi tasaki daidai shigowar ummi kamar tasan meya kawo ummin ta fa'da toilet da sauri batareda tabari ta hada ido da ummi ba.

Wani sabon farin ciki ya qara qule ummi takoma Palo gurin mamy da itama sai farin cikin take suka taru suka 'dora sabuwar fira zukatansu fes.

Yinin ranar tsaf a 'daki tayi abinta zuciyarta fes duk da gidan akwai baqin ummi dazasu tarbi Amarya anjima idan ankawota.

Shikansa ba a gida ya wuniba yana gurinsu Yusuf a masaukinsu sunata firarsu duk da bayasa baki a firar tunda yaje ya kwanta ya lumshe idanuwa ya fa'da duniyar tunani.

Qarfe Tara aka kawo Amarya ayeesha gidan a sashenta bayan ankawota gurinsu ummi sun sanya alkhairi.

Qarfe goma gidan yayi tsit kowa ya watse su ummi ma duk sun kwanta.

Parking yayi bayan ya duba agogon hannunsa ya tabbatarda kowa ya kwanta yafito motar tareda nufar sashensa.

Harzai bude qofar palonsa yashiga saiya ji yana sha'awar zuwa yafara ganinta kafin ya shiga gurin ayeesha.

Bedroom 'dinta yashiga daidai fitowar khadija zata 'dauko ruwa kicin.

Cak ta tsaya kallonsa qafafuwanta na rawa sbd dama ba isashiyar lafiya ne da itaba bare yanxu da idanuwanta sukai mata mugun gani wai Jamaal 'dinta zai shiga 'dakin neesah da tsakar daren nan.

Sam shi ko kallo bata ishesaba yashigewarsa 'dakin tareda turo qofar.

Kwance take a tsakiyar gadonta ta dunqule sbd sanyin ac dakuma window 'din dakin dake bude har iska na 'dago labulen.

Qarasawa yayi tareda aje kayan hannunsa ya zauna kan gadon tareda jawo duvet blanket ya lullu6a mata tareda gyara mata kwanciya a jikinsa.

Bai ankaraba bacci ya 'daukesu ahaka dan har wani qara qanqamesa tayi.

Qarfe 'daya daidai zeey taredasu leloh da yaransa suka shigo gidan ta hanyar Ahmed daya bu'de musu qofa.

Dukkaninsu sanye suke da baqaqen kaya da bindigogi
Ita kanta zeey da Ahmed baqaqen kayane ajikinsu.

Ayeesha dake tsaye tsakar 'dakinta tana kai kawo kamar zata buga sbd baqin cikin daren farkonta gidan mijinta amma yaqi tahowa gareta.

Wayar zeey takira daidai lokacin dasuka iso bakin windon 'dakin khadija dake zaune tsakar 'dakin har lokacin tana dirzar kuka.

Jin motsin mutane a bayan windonta yasata tasowa ahankali tazo bakin windon.

Isowa ayeesha tayi gurinsu cikin san'da suka kalleta cikeda mamaki murya qasa qasa Ahmed yace,

Amma dai kinsan so kike ki 6ata mana aiki shiyasa kika fito sbd Yaya zaiyi tunanin ina kika tafi da tsakar daren nan.

Tsaki taji ahankali cikin takaici tace,

Ai wallahi saina qunsawa captain baqin cikinda zai kusa tafiya da ransa sbd wannan abin dayamin a daren yau.

Zeey tace,
Yanxu dai duk ba wannanba mu hanxarta muyi abinda yakawo sbd yau idanba satota mukaiba banajin zan iya koda numfashi da lafiyata.

A matse Ahmed ma yace,
Please Ku lura da kyau gurin shaqa mata qyallen nan sbd inason ta shaqesa da yawa yanda bazata farkoba harsai gobe idan munxo.

Motsi sukaji a razane suka juya leloh haryana seta bindigarsa zaiyi harbi ayeesha tayi saurin riqesa tana cewa,

Bakada hankali ne zakayi harbi aji qararsa asirinmu ya tonu.

A hasale zeey tace,
Kibarsa idan ya saba da gidan prison yana marmarin komawa tomu bamu sababa bakuma zamu ta6a zuwaba.
Chapter 13 · 0% Book details