← Book details Beelal Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 13

Sashe 8

Beelal Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suna tambayar Babangida ba a samo Beelal in ba, bayan da lokacin yana nan babu wanda ya damu da su.Fatima kuwa ta san tana bu e baki kuka zai wace mata dan yanzu ma burinta kawai ta gan ta a cikin gida. Tun da ta shigo cikin gidan idanunta suka sauka a kan kayan Beelal na wanki wanda ta wanke masa jiya da yamma, tana kallonsu wata shu iyar riga da shi da kansa ya shanya rigar yana ta cewa take bashi shi ma yana wankin, ta ce sai dai suke shanya tare saboda hannunsa marar lafiyar har yana cewa idan ya ara girma zai ke yin wankin take ce masa. "Haba Beelal ai duk girmanka ni zan ke maka wanki saboda larurar da ke tare da kai, idan kuma Allah ya hore mini sai in ke biya ana wanke maka idan ka yi aure dan kar a orawa matarka wahala dan ba kowace mace ce za ta awainiyar wanki ba bare matan yanzu da basa son wahala su ma so suke a hidimta musu" "Ni ba wani aure da zan yi Mama a gida zan zauna muke zaman mu tare da ke, ni fa a duniya kwata-kwata ba na son rabuwa da ke sai sai in mutuwa ce ka ai za ta raba mu ita ma dan dole ce" Wannan kalaman nasa na jiya suna fa o mata sai kuwa wani kuka mai arfi ya wace mata ganin gashi ma ashe kwana aya ya rage musu jiyan raba tsakaninsu duk da kasancewarsu masoya na ha a amma rashin imani da tsoron Allah ya sanya Idrisu ya raba su, idanunta ta sauke a kan katifar da Idrisu ya kwanta a kanta jiya wacce ke a waje aure da net in da ta sanya masa wani haushi da takaici ta ji a lokaci da ta kalli katifar kuka ne ya wace mata. Hannu ta sanya ta toshe bakinta da kukan ke fitowa aki ta nufa da an gudu-gudu, tana shiga akin ta fa a kan katifar ta a ribda cike ta kwanta tare da kifa fuskarta a kan tafukan hannayenta ta saki wani kuka mai arfi wanda yake fitowa da acin rai ha e da zunzurutun kewar anta tilo Beelal, tana jin zafin da zuciyarta take mata, tausayin yaronta yana da a ninkuwa a ranta tana tunanin irin rayuwar da zai yi a wani waje da babu ita babu wani wanda ya sani sai Idrisu mutumin da ba ya aunarsa kuma yanzun ma ta tabbata ba aunar ce ta sanya ya auke yaron ba, illa wani udiri nasa marar kyau da Allah ne ka ai ya sani, tausayin Beelal na ara shigewa zuciyarta tana tunani ya zai ke aiwatar da abubuwan da ba ya iya wa sai dai ita ta masa saboda NAKASAR da ke tare da shi. Sai da ta yi kuka mai isarta, aikuwa idanun suka sake suntumewa, amma bata damu da hakan ba, cikin sauri ta tashi daga kwanciyar da ta yi ta auki abu ta goge fuskarta tas, da hanzari ta tashi domin duba wayarta wacce Hajiya La ifa ta turowa wani mai pos da ya tura mata acc no sa ta turo ku i aka sake mata wayar ko sati biyu bata yi ba, fatan ta dai Allah sa Idrisu bai auke wayar ba, wurin da ta ajiye wayar ta je ta duba cikin ikon ALLAH sai ta ga wayar tana nan, dan dama ta siyar da tsohuwar, hannunta har karkarwa yake da ta akko wayar dan ta tabbata idan har da ya auke wayar shikenan ya datse mata abin da ta sa a a ranta yanzun nan. Wayar ta kunna ta kamo sunan Yayarta har ya kira kafin kiran ya shiga sai ta katse saboda tana ganin Hajiya La ifa idan ta ji abin da take shirin yi za ta iya dakatar da ita dan haka sai ta fsa kiranta, bu e wayar ta yi ta fitar da sim in ta karya shi, cikin hanzari ta tashi kamar an tsikareta ta fito da sauri, takalmanta ta saka ta nufi hanyar ofar gida. Shagon siyar da wayoyi ta nufa, kawai jefa afarta take kamar wanda ake hanka ata, tana zuwa kuwa ta yi sa'a a bu e, ta sanar da mai shagon wayar take son siyarwa ganin wayar kamar ma yanzu aka bu eta a kwalinta ya shiga son jin dalilin siyar da wayar dan dai ya fara tunanin ko dai wayar ce take da matsala dan a zahiri dai babu wasu alamu da suka nuna haka. Fa a masa ta yi amfani take son yi da ku in, nan ya sayi wayar dubu 25 wayar da dubu 35 aka siya haja ta siyar masa dan ita bata da lokaci ko nutsuwar da za fa yi ciniki ko jayayya da shi. Ku inta ya bata ta kamo hanyar gida, tana shigowa ta auki aramar pos inta ta sanya ku in wani hoton kati na Beelal ta akko ta tsaya kallon hoton cike da alhinin nisa da ya yi da ita, hoton lokacin Beelal yana tsayuwa aka aukeshi, afar nan marar lafiya ta karkace ya aga hannunsa mai lafiyar sama yana dariya, tunowa da shekaran jiya tana gyaran aki ta akko hoton Beelal da ke game a wayarta ya dakata ya kar i hoton yana dariya ya ce cikin in'innarsa. "Mama kamar ba ni ba a nan kin ga na girma" Ya fa a yana dariya. "Eh mana ai kowa ma da haka ya girma, wata rana ma magidanci za ka zama" Ta fa a tana dariya. "Mama ki bani hoton in ajiye shi a wurina" "Ai wannan hoton babu wanda zan baiwa nawa ne sai dia idan ka girma zan sa a wanka maka shi, sai kaima ka ajiye, amma dai wannan nawa ne, duk inda ka gan shi to ni ce na kaishi wurin dan babu wanda zan iya bawa sai dai in mutuwa na yi" Maganar da suka yi da Beelal shekaran jiya a kan hoton ta fa o mata, kafin ta ankare sai ganin igon hawayenta ta yi a jikin hoton cikin sauri ta goge hawayen daga jikin hoton ta sanya a cikin jakar. Tsayawa ta yi tana arewa akin kallo yana rayawa a ranta cewar sai kuma in rai ya kai, dan ita dai ta san a udurin da ta yi babu gudu ba ja da baya. o ta akko da mukullan ta kulle akin, tana fitowa waje ma ta rufe ofar gidan. Shagon mai caji ta nufa wanda suke waya wani lokacin da Hajiya La ifa a wayarsa idan Hajiyar ta kira wayar Fatima ta ji a kashe, sa o ta bashi a kan cewa idan Hajiyar ta kira ya ce mata ta tafi Lagos. Mai machine ta samu ta ce ya kaita Kazaure, a tasha ya sauketa ta biyashi ha insa motar Kano ta hau suka au hanya. Wajen sha aya da rabi suka ido cikin Kano. "Allah sarki Yayata ki yi ha uri da abin da zan aikata na san ba za ki ji da i ba, sai dai hakan shi ne mafita kuma shi ne kwanciyad hankalina dan matsawar na zauna a nan ban tafi neman Beelal ba to tabbas rayuwata za ta are ne a unci! Ki yafe mini yau gani a cikin garin Kano amma ba wai dan in je gidanki in kai miki ziyara ba sai dan kawai hanya ce ta kawo ni, ki min afuwa Yaya!" Cewar Fatima a zuciyarta tana share hawaye, dan shigowar motarsu garin Kano ya ara tada mata mikin abin da ke damunta a cikin ranta. A an kaba aka saukesu, an sahu ta samu ta ce dan Allah ya kai ta inda za ta samu motar da za ta kaita Lagos, har wurin ya kaita ta bashi ha insa ta samu wuri ta zauna dan ba ma lokacin motar za ta tashi ba. Sai wajen arfe uku motarsu ta tashi, amma duk zaman Fatima a wurin ko ruwa bata sanya a bakinta ba sallah kawai ta gabatar, ko yanzu ma da suke tafiya kanta kawai ta jingina idanunta a rufe tana jin yadda mutane ke ta hira a motar amma ita ko abin da suke cewa bata sani ba damuwar da ke tattare ita ta wargaza mata komai, dan rashin Beelal a kusa da ita ba aramin abu bane. MMN AFARAH 09030283375 *BEELAL* NA MAMAN AFARAH *FCW* Book 2 Page 1 *HAMEEDA* Tana arin bu e baki ta yi magana Musty ya aika mata da wata uwar hararar da ta sanya ta kama bakinta ta yi shiru. Hajiya Zulaiha kallon Mustyn ta yi ganin sai wani kumbura baki yake yana une sai ta ce "Hameeda maza jeki uzurinki" "To" Haeeda ta fa a cike da ladabi ta tashi ta bar falon. "Haba Mom wai ya kike min haka ne, a gaban wannan aramar yarinyar kina son ta rainani ne?" "Oh wato ka san ma arama ce yarinyar da bata fi 7yrs ba kai kana kusan 19yrs amma kamsr wata sa'arka kawai daga shigowarta sai kake neman dukanta kuma na san halinka babu wani laifi da ta maka" "Ko ma ta mini laifi ko bata mini ba ai dai bakya fifita ar aiki a kan an gida ba ko" "Sannu masu gida" Cewar Hajiya tana kallonsa. Alhaji Tahir ne ya shigo da sallama. Amsa masa Hajiyar ta yi shi kuma Musty ya ce "Oyoyo Dad" "Wato baka san ma na dawo gidan ba, daga masallaci fa nake yanzu kana can yawonka na dawo ba yanzu na dawo ba" "Haba Dad yawo kuma ai ina can wajen friends ina" "Ohk hakan ma ya yi kyau" Kallonsu kawai Hajiya ta yi ta auke kai abinta ta yi wajen dinning in, su ma bin bayanta suka yi Dad ne ya jawa Musty kujera ya zauna sai shi ma ya zauna Mom ta shiga zuzzuba musu abinci. Sai da suka kammala cin abincin nasu sannan suka dawo falon suka cigaba da hira abinsu. *BAYAN SATI BIYU* Da la'asar sakaliya ne Musty ya shigo gidan da moyarsa bayan mai gadi ya wangale masa get, yana yin parking ya bu e mptar ya fito hannunsa ri e da leda, hango Hameeda ya yi tana shanya wasu dosters da ta yi goge -goge shi ne ta wanke
Chapter 8 · 0% Book details